Writing by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Blood sister deeja📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM
13_14
Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un duk wani mai rai mamacine yau dai kausar ta rigamu zuwa gidan gaskiya, shi kuma sadiq aka wuce da shi emergency dan bai san inda kansa ya ke ba, dangi sunyi kuka sosai na rashin kausar saboda kausar mutuniyar kirkice.
Yau kusan sati daya kenan da rasuwar kausar sadiq na asibiti sosai yake samun kulawa wajan su jawad da majid, wanda bai ma san suna yi ba, Jawad ne zaune a d'akin asibiti saman three star yana shan coffee yana d'an kallon sadiq dake kwance har yau tamkar gawa, sosai yake damuwa da halin da d'an uwan nasa ke ciki.
A hankali yake bud'e sexy eye's balls d'in sa, abubuwan da suka faru na dawo masa tamkar yanzu akayi su, wani irin kuka ya fashe da shi maitsuma zuciya yana qoqarin tashi ya cire drip din da ke maqale a hannusa, Jawad ne ya taso ya rungumesa alamar lallashi kuka ya qara fashewa da shi yana fisfisgewa kamar zarare yana cewa, "Bros I cant live with out my wife please bros ka barni na bita" ya qara fashewa da wani sabon kukan, ganin abin nashi kamar ba kai d'aya ba ya sa jawad yayi ma d'aya daga cikin yaran sadiq masu tsaron lafiyarsa magana dake tsaye bakin kofa ya ce, "Kiran Dr yakub.
Jum kad'an Dr yakub ya shigo shi da nurse tana d'auke da trayn alururi, dakyar Dr da jawad suka samu suka danne sadiq aka masa alura bacci, sai da yayi kusan 30 minutes yana sanbatu sannan bacci ya d'auke sa Jawad ne ya ce, "Dr Ina fatan dai sadiq ba brain nashi bane ya sami problem ba? ya ida zancan yana matsar kwalla "karka damu kawai mutuwar ta firgi tashi ne amma, insha Allah zai samu sauki daya tashi komai zaiyi normal, Allah bashi lafiya"
"Ameen Dr.2weeks letter
Sosai Jidda ke samun kulawa wajan Mom da baba jummai da mai aikin ta Mary, sadiq ko duk wata walwala ya daina idan kaga yana smile to Jidda na hannusa, inda ya d'aura mata son duniya nan wani bangare na zuciyarsa kuwa ji yake Nigeria ma ta isheshi saboda ya rasa abar kaunar sa, daga karshe ya yanke shawawar barin kasar bai samu wata matsala ba wajan aikinsa ya d'au hutu sheraka d'aya, Mom ce zaune a parlour sadiq na riqe da jidda wanda bacci ya d'auke ta acinyar sa cikin sanyi murya kamar mai koyan magana da yanzu magana ma wuya take masa ya ce, "Mom Ina san nabi jawad londan idan zai koma"
"toh ai shikenan son"
"Amma Ina san idan zan koma na koma da Jidda, saboda sai hankali na yafi kwanciya" Mom ce ta daka tsale ta dire ta ce bata san zancan ba, ba inda zai tafi da ita duka yarinyar nawa take zai tafi da ita, ba yarda ya iya ya hakura wannan kenan.
CIGABAN LABARI
A hankali ya d'au jidda wanda ke bacci ya kaita bedroom ya kwantar da ita ya shiga wanka, inda yake jin mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa sai da ya zubar da kwalla sosai, 30 minutes yayi yana wanka ya fito sanye da bathrobe, A hankali ya kai lips d'in sa goshin Jidda ya mata peck, ware manyan eye's ball din tayi ta ce, "Daddy.!
"oya tashi ayi wanka muje yawo wajan hajiya da Umma" baki ta washe ta ce, "ok daddy.! d'aukarta yayi ya kaita bathroom ya wanke ta tas suna wanka suna wasan ruwa.****
Yanzu saboda Allah fatuha kin kyauta kenan? ince bana ce ki kyale Rabi'u ba eh?
"yo inna ji nayi kwarankwatsi bana iya hakura"
"Aikin kyauta tunda kin sa maitafasa tamin tanadi kinji d'ad'i saiki zubar da ruwa a qasa kisha" baki ta turo gaba ta ce, "Gaskiya inna baki so na kwarankwatsi Baffa yafi sona" ta ida zancan tana matsar kwalla inna ta ce, "Fatu kenan kin ta6a ganin inda uwa ta haifi d'a tace bata so, Kawai dai halin kine ban so fatuha, ki daina tsokana" baki ta washe ta ce, "yo ahe kina so na kwarankwatsi na daina tsokana amma bilahilazi duk wanda ya shiga gona ta sai ya ci wuya Qur'an" Sannan ta zuri takalmanta ta ce, "Inna na tafi makarantar allo"
"Toh Allah ya shirye ki"
"ameen inna..!*****
Bayan sun fito daga bathroom ya shirya ta cikin gown maroon mai d'an siririn hannu sai mai dogwan hannu a ciki ya gyara mata gashin ta, masha Allah sosai Jidda tayi kyau kamar d'iyar larabawa, peck ya mata a cheeks ita ma ta masa ya ce, " good girl tayi kyau" baki ta washe ya ce, "oya je ki wajan grandma gani nan zuwa"
"OK daddy" ta ruga da gudu ta fita ya bita da kallo yana smile, shima shiryawa yayi cikin jeans black and red t-shirt mai ratsin black sannan ya maqala ma hannu sa agogo black na zalla fata sai sheki yake, ya zura takalman sa black ba qaramin kyau yayi ba abin ka da farar fata d'an hutu sajan nan nasa ya kwanta luf-luf, a hankali yake sakowa downstair, a parlour zaune ya samu Mom Jidda na zuba mata surutu, cikin natsuwa ya gaishe ta ta amsa sannan yaja hannu Jidda suka fita Mom ta masu a dawo lafiya.****
Zauna suke suna karatu fatuha tace, "kwarankwatsi na gaji, yo hi haka akeyi ya tasamu gaba ana abu daya"
"Rabu da shi Qur'an nan kadai ya iya a karatun" cewar Fatsima dariya suka kwashe da ita, ashe Malam D'alha ya ji dariyar ya fido so waje yana zare masu idanu ya ce, "Dan buhun uban ku kun raina mutane ko? yau zaku ci uban kune" sai da ya zane masu jikin rad'au sannan ya kyale sun inda suka rinqa jeramasa Allah ya isa.*****
Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu Jidda part d'in hajiya suka fara shiga, d'auke da sallama suka shiga hajiya da ke zaune saman two star ta washe hakora tana cewa, "Ah'ah wana ke gani yau, kaine a gidan namu amma yau 6atan kai kayi maigida" Smile sadiq yayi ya langwabe kai ya ce, "Kai hajiya sokike ki ce bana zuminci ko? sannan ya samu waje ya zauna hajiya ta ce, "Dama yi kake? ta ida zancan tare da qwalawa Asiya mai aikin ta ta kawo masu kayan motsa baki "oh ashe da wannan yan neman ka zo" hajiya ta fad'a tare da jan Jidda ta d'aura saman cinyarta sadiq ya ce, "Kawo maki ita nayi ta maki 6ana"
"lallai kam aiko da taci na jaki" su duka suka kwashe da dariya sun dad'e sosai suna hira sannan suka wuce part d'in Umma.
Da sallama suka shiga Umma dake kitchen ta leko ganin sadiq ta washe baki ta ce, "ah'ah yau za'ayi ruwa da qanqara" da gudu Jidda ta ruga ta rungume Umma, Shagwabe fuska sadiq yayi tare da zama yana cewa, "Umma har da ke cikin masu ce min bana zuminci" kamar daga sama ya ji saukar magana "Toh dama yin zuminci kakeyi" cewar majeed juyowa yayi ya dallama majid harara, sanye ya ke da kayan ball green da alama daga ball yake sadiq ya bud'e baki ya ce, "Toh d'an hana ruwa gudu" yar shewa majeed ya saki ya hau upstairs.
Basma ce ta fito qanwar majeed baza ta wuce 15years ba ta gaishe da sadiq ya amsa ta ja hannu Jidda suka je dakin ta, sun dad'e sosai suna hira da Umman sannan ya bi bayan majid.
D'akin majid ya shiga ya zauna saman sofa lokacin majid na wanka, sanye da bathrobe ya fito yana murmushi ya ce, "Ashe ka biyo ni? harara sadiq ya balla masa majeed ya ce, "bani na kar zoman ba rataya aka bani, ka zo sai yi ma mutane borin kunya kake" ya ida zancan yana dariyar shaqiyanci, basu suka bar gidan Umma ba sai isha'i lokacin su Alhaji sun dawo daga kauya.****
Fatuha da fatsima ne bakin rafi suna shan mangwaro "bilahillazi mangwaron ga zaqi garai" cewar Fatu
"sosai ma Qur'an" inji fatsima fatuha ta ce, "kin san wani Abu na matsu baba jummai ta zo mu ci d'ad'i nifa tsarabar nake mawa"
"ke dai bari fatuha"
"nima wallahi duk cikin tsarabar wannan bak'in abun yafin dad'i" ta washe baki ta ce, chakule ko (chocolate) lol....
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...