Written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Raheenat📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★http/Mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=,H-R
*_Email_* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*_Facebook_*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
63_64
Juya bayan da sadiq yayi yasa fatuha jan dan guntun tsaki tare da kallon agogan dake maqale a bango kusan karfe 8:30 na dare, tashi tayi ta bar part din ta koma part din su tana shiga bedroom ta rage kayan jiki ta, ta shiga toilet ta sheqa wanka ta fito daure da towel ko shafa mai ba tayi ba, ta bude wardrobe ta ciro kayan baccin ta riga da wando pink masu mayan flowers da zanan ya'yan cartoon, d'aure gashi kanta tayi da wata yar kibiya ta d'aure kai sannan ta fesa turara har zata kwanta sadiq ya fado mata a rai ta barshi a d'aki shi kad'ai, gashi baya da lafiya tashi tayi zubur zata fita sai kuma taci birki ta ce "Ko naje tijara zai mun dan ba mutunci gare shi ba, karma ya tsinka ni.! wata zuciyar tace haba fatuha duk rashin mutuncin mutu bai da lafiya ai dole ya shafa wa mutane lafiya riqe handle din kofar tayi kamar me na zari can kuma ta bude ta wuce part din sadiq ta shiga dakin har yanzu bacci yake parlour ta dawo ta kuna kallo dan ba wani bacci take ji ba cikin jin dadi take kallon arewa24 suna shirin tarkon kauna gaba ki d'aya film din ya mata d'adi sosai sai da aka kamala film din misalin karfe 10:00 na dare sannan ta leqa dakin sadiq, bakin bed din ta tsaya tana qaremasa kallo a hankali ta kai hannu zata taba goshinsa amma ta kasa dunqule hannu tayi tana nazarin jikin nasa ganin ya motsa ya sata gyara tsayuwa tana kallon yanayinsa lumshe ido tayi a hankali ta kai hannu tata6a goshin sadiq ji tayi zafi rau kamar garwashi mamaki ne ya kamata da tsoro cikin rawar murya ta ce "Mai kyau?" shuru sadiq yayi saboda shi kad'ai yasan yadda yake jin fever na damu shi kneeldown fatuha tayi gaba gadon ta qara cewa, "mai kyau.! a qaro na biyu, bude sexy eye's ball's dinsa yayi a hankali yana kallon fatuha data fara matsar kwalla smile yayi ya ce cikin cool voice nashi "Menene fatuha? kin kasa bacci ne?" girgiza kai tayi alamar a'a "to menene? kallonsa fatuha ta kumayi ta ce "har yanzu masasaran nan bata sauka ba duk da likita ya duba ka tana matsama baka ji jikin ka da zafi ba? da a kauye ne da inna ta dafa ma magunguna kuma da kasha zaka warke, amma nan likita sai duba ka yake amma ka qi warkewa mai kyau, dan Allah ka daina tunani kaji shiyasa kaqi warkewa" ta fadi zancan tana zubar da hawaye kallon ta sadiq kawai yake yana mamaki irin tausayi na fatuha gabaki d'aya tabi ta rude tunda taga bai da lafiya lumshe ido yayi tare da warewa ya sauke so a kanta ya ce, "insha Allah fatuha zan daina kinji" murmushi ta saki mai hade da kuka-kuka ta tashi ta shiga toilet din sadiq shi kuma ya bita da kallo ruwa ta d'ebo a babba boll na roba tasa towel a ciki ta dawo d'akin har yanzu idanuwan sadiq na kan fatuha ko qif tawa bayayi, sai da ta qaraso gaban shi ya lumshe ido aje boll din tayi a gefen bedside drawer idanuwanta taf da hawaye cikin nutsuwa ta shiga matse towel din a hankali ta nufo towel din goshin sadiq ta fara dadanna masa kamar yadda inna ke mata idan tana masasara, ko ina na jikinsa take bi inda ke bude tana danna masa towel din a hankali fever ta fara sauka shi kanshi Sadiq yaji dadin jikinsa sai dai dan dumin da jikin yayi bacci ne ya fara fisgar shi kafin ka ce me bacci ya kwashe shi, sai fatuha dake ta faman dannamasa towel.
A hankali ta fara gyangyadi dan ta fara jin bacci, sai bacci ya fisgeta sai firgigit ta tashi ta cigaba sai da bacci yaci karfin ta, ta fada fadadan qirjin sadiq bacci ya kwashe ta.Kiran sallah asuba ne ya tashi sadiq a hankali yake bude sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha da ke bacci male-male a qirjinsa gashin kanta ya baje saman qirjinsa ta kankame sa, matsar da gashin kanta yayi gefe yana qarema fuskar ta kallo, har mamaki wayau irin na fatuha yake gata qarama amma sai dai tana da halin manya, kasa dauke idanusa yayi kanta, yunqurin tashi yayi yaji ta motsa komawa yayi ya lumshe ido yayi lamo kamar mai bacci.
tashi fatuha tayi tare da ware ido ganin ta jikin sadiq kwace a zabure ta mike tsaye ta ce "Nashiga uku yaushe bacci ya kwashe ni? wayo Allah na da mai kyau ya tashi ya ganni dana bani" hannu ta kai goshin sadiq jin ba zafi yasata sakin ajiyar zuciya ta furta, "Alhamdulillah jikin yayi sauki bari nayi sauri na d'auro alwala" part din ta bari ta wuce nasu.
ESTÁS LEYENDO
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...