Written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Raheenat📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★http//mobile.Facebook.com./Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
51_52
Fatuha na shiga bedroom saman bed ta fada tare da sakin saban kuka tana cigaba da jerawa sadiq Allah ya isa da ace Allah ya isa na fitowa a jiki to da daran yau ba abinda zai hana shi fitowa ajikin sadiq, kuka ta ke mai tsuma zuciya har da shesheqa tana a jiyar zuciya, ita babban abinda ke damun ta koda ta zo masa muguntar sai ta kasa kuma ko tayi mai ramawa ya ke, lumshe idanuwanta tayi tare da sauke numfashi a hankali ta cigaba da jerawa sadiq alkaba'i a haka har bacci barawo ya sace ta.
Bangaran sadiq ko saman sofa ya zauna tare da ganin bai kyauta ma fatuha ba, lumshe ido yayi tare da ware su koma mai yayi mata ita ke san shiga gonarsa shiyasa shi kuma baya saurara mata da tasan yadda yake ji idan yaga albums dinan da ko fada mata akayi ta dauko su inda ya aje ba zatayi ba, iska ya busar mai zafi daga bakinsa bayan Ammi ta gama hada masa zafi ita kuma ta dagulamasa lusafi album din ya bude a hankali kamar mai jin tsoran wani abu ya shiga kallon pics din, ya dade yana kallon inda yake ganin mutuwar kausar ta dawo masa sabuwa har hawaye sai da ya zubar kamar ba soja ba, anan saman sofa bacci ya kwasheshi.*Asuba ta gari*
Ko da ya tashi da asuba wanka ya sheqa sannan yasa jallabiya ya wuce masallaci, yana dawowa ya samu bacci mai cike da nutsuwa amma duk da haka qirjin shi namasa zafi saboda tsabar damuwa lumshe ido yayi tare da jan jidda jikin shi bacci ya kwashesu.
Fatuha ko da kuka ta tashi fuskar ta har tsami ta mata, saboda ba qaramin mari tasha hannun sadiq fuskar nan ta kunbura tayi sumtum kallon mirror tayi tare da fashewa da kuka fuskar tayi jawur har idonta sai da ya qara girma saboda tsabar kuka, toilet ta shiga tayi wanka tare da dauro alwala tana fitowa after dress tasa black tare da gabatar da sallah ko da ta idar da sallah kuka ta cigaba da rerawa sannan ta tashi jiki ba qwari ta murda handle din kofar tare da ficewa daga bedroom din direct part din sadiq ta shiga.
Duk da tana jin tsoro haka ta lalla6a ta murda handle din kofar bedroom zaune ta hango sadiq saman sofa yana danna laptop yana shan coffee cikin dari-dari ta qarasa shigowa tare da yin sallama, dago kai sadiq yayi ya qare mata kallo shi kan shi yasan bai kyauta ma fatuha ba ya 6ata mata baby face din ta, ra6ewa ta shiga yi dan tak take jira ta arce sunan ta ya kira cikin cool voice din shi gaban ta ne ya yanke ya fadi duk da yauce rana ta farko da mai kyau ya fara kiran sunan ta, sai taji duk duniya ba wanda ya iya fadi fatuha qara kiran suna ta yayi hakan yasa ta fara matsar kwalla tana yarfe hannu ta qarasa kusa da shi tare da tsugunnawa tana wasa da yantsun hannu ta idanuwanta taf da kwalla hannu yasa ya dago da habarta lumshi ido yayi tare da waresu gaskiya bai kyauta ma fatuha ba ji yadda ya mai da fuskarta, tausayi ta bashi sosai kuka ta shiga reramasa a tunanin ta wani mari zai qara zabga mata "shhhh.! ya ce mata cikin cool voice nashi shiru tayi tana matsar kwalla bedside drawer ya bude ya ciro magani a dan top sannan ya dawo sofa ya zauna tare da talabo mata fuskar matsar maganin yayi a hannu ya shiga shafa mata a face din ta kuka fatuha ta saka sai kace ya watsa mata ruwan zafi iskar bakin shi ya shiga hura mata mai sanyi lumshe idanuwan ta fatuha tayi, wani irin dadi taji dan tunda ta tashi da safe fuskar ke mata radadi sai yanzu da taji dama-dama, ware eye's ball din ta tayi kan sadiq, tana kallonsa sadiq da ke qoqari dagowa goshin su ya hade ushhh ya ce, shagwabe fuska fatuha tayi tare da fara kuka sorry yace mata sannan ya sa hannu ya murza mata wajan dan karya kunbura har lokacin da ido fatu ke binsa komai sadiq yayi murgeta ta yake, sannan ya kyaleta tare da yi mata lallausan smile tashi tayi tana qoqarin daukar jidda su fita, fatuha yace juyowa tayi tana kallonsa ya ce, "shiga da ita toilet dina ki mata wankan" to ta ce masa sannan ta shige da jidda bathroom bin ta yayi da kallo tare da daukar newspaper.
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...