Written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Blood sister deeja📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
17_18
After lunch sadiq ya kwashi su jidda da Hanan da Jamal zuwa shan ice cream sosai sunje yawo daga nan ya wuce dasu munjibir park, cikin jin dadi suke wasan su duk inda ka kalla a wajan yara ne da manya ke hutawa har ma turawa, resting chair ya samu ya zauna yana Kallan su Jidda yadda suke wasannin su cikin nishad'i daga nesa kuwa yan'mata sai yaba kyansa suke da tsarin shi wasu mamaki su kar dai ace duk yaranan nashi ne, dan iya kar haduwa sadiq ya hadu wasu ma sai jan su Hanan suke a jiki dan su samu damar yi ma sadiq magana ganin ba wasa a fuskarsa ya suka hakura basu suka bar munjibir park ba sai gab da magrib.
Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu jidda, Jamal kuma na kafadar sa yaran shi yayi ma alamar su kwaso kayan dake cikin motar su biyo shi da su, haka ko akayi suka kwaso kayan ba komai bane sai kayan zaqi kala-Kala da teddys da kayan wasa da ya saima su.
Anuty bilki na zaune a parlour saman three star Hanan ta rugo take fada jikinta ta ce, "Momi.!
"yeee yan'matan Momi sun dawo" bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo yana Cesar, "Ah sister ke kadai ce a parlour Mom fa?
"tana part din Abba"
"ok.! ina baba jummai?
"Tana kitchen"
"ok Hanan kira min rabi'a ta amshi kayanan ta kai maku su d'akin angel"
"OK uncle" rugawa tayi kitchen ta Kira rabi'a.. sanye take da farar riga mai dogwan hannu sai mini skirt da alama wannan kayan unform ne na yan'aiki.Har qasa ta duqa ta gaishe shi tare da amsar kayan ta wuce da su bedroom d'in Jidda sadiq ya ce, "sister ni zan wuce masallaci may be sanda zan dawo kin tafi"
"Ai kwana zanyi a gida" waro ido yayi ya ce, "Gidan naki fa" yar shewa aunty bilki tayi ta ce, "ka manta mai gidan baya nan sai gobe zan koma"
"oh haka har yanzu bai dawo ba?
"eh.!
sannan sadiq ya sa kai ya fi ce zuwa masallaci.*****
Duk wata gona dake da bishiyar mangwaro sai da suka leqa suka tsunko nunanu, daga nan suka biya wajan shafi'u mai rake suka amso bashi, acewar duk sanda bala dan mai gari ya basu murtala zasu biyasa bayan sunyi tafiya mai nisa fatsima ta ce, "Kai wallahi na gaji"
Fatu ta ce, "ai sai da nace maki mu zubar da ruwan tulun mu zuba mangwarayan mu cikin tulun, idan mun koma gida sai muce biyo mu akayi muka fasa dibar ruwan"
"kwarankwatsi ke dai fatuha wayau gare ki amma kinsan wani Abu"
"a'a saikin fada.!
"qara muje da ruwan Qur'an saboda mun dad'e"
"Haka kuma fa ga wancan Malam D'alha d'in sai sauri ya ke yaje ya fara zalinci"
"ke dai bari" ta qara gyara tsayuwar tulun ta
"kinko iya qarin jiya fatuha?
"hehe yo tun yaushe na iya shi, Ke nifa Malam D'alha ne baimun ba shiyasa bana bashi hada amma Qur'an na iya"
"toh bilahillazi yau sai kin bashi saboda yau ban shirya ma bugu ba, Ko bishiyar nan da muka hau na maqale duwawuna sai zinga yake" Fatuha ta kwashe da dariya ta ce, "Sai ki je gida kiyi gashi da ruwan d'umi Inmaki na maitafasa"Cikin sallama ta shigo gida inna ta amsa, Inda Sabo ya kamata ta saba da wannan baqin halin na fatuha in ta je d'iban ruwa sai ta shekara bata dawo Ba.
"Inna Ina abinci na?
"yana madafi" kwanan samira ta jawo tuwo ne miya kuka yasha manshanu sai kamshi yake loma daya zuwa biyu tayi, fatsima tayi sallama cikin shirin ta na zuwa makarantar allo, tare suka zauna suka ida cin tuwo zata d'au hijabin ta kenan inna ta leko daga uwar d'aka ta ce, "yanzu saboda Allah fatuha sai na ce kiyi wanka zakiyi kome? raban ki da wanka tun shekaran jiya wuce kiyi wanka nan ku tai makarantar" baki ta turo gaba tana dire-dire "gaskiya inna ki bari sai na dawo nayi"
"Aifa baki fita sai kinyi wanka"
Da kuka da komai fatuha tayi wanka sannan ta fito suka wuce makaranatar allo.Zaune suke a parlou suna hira cikin ni shadi su Jidda sai wasa suke aunty bilki ta ce, "Ku dai baku gajiya da wasa ko, Ince dazu ba manjibir park kuka je da uncle ba duk wasan da kukayi a can bai ishe Ku ba ko? Oya ku wuce ku shige bedroom kuyi bacci" su duka suka hada baki wajan cewa, "sorry Momi..! tare da lagwa6e kai duka parlou aka fashe da dariya.
Abba ya katse dariyar da cewa, "Yauwa gobe Ina so ku shirya da wuri zamu je family house meeting"
"Toh Allah ya kai mu Alhaji" inji mom sun dad'e sosai suna hira a parlour sannan kowa ya tafi part nashi, Inda su Jidda suka maqale ba su kwana ko Ina sai part din sadiq haka ko akayi da yake shi mutun ne mai son yara.Bangaran su alhaji ko sosai suke zuba soyayya tare da gwada wa juna su yarda sukayi kewar junasu, sosai alhaji ke gwada ma Momi salan sa daga nan suka lula duniyar ma aurata.
*****
Zaune suke Malam Dalha sai amsar hada yake da zabgegiyar bulala shi a hannu, burin shi bai wuce ya ga su fatuha sun kasa ba ya wanke su da bulalar.
"Ke tashi ki bani taki hada" cikin tsiwa fatuha ta tashi ta fara karanta wa Masha Allah cikin murya mai sanyi da dad'i (ni kaina sai danayi mamaki wai dama fatuha ta iya karatu haka) Malam Dalha ko sakin baki yayi har ta gama sannan ya koma ya zauna gwiwa sage. lol***
Tsale-tsale suke kamar ba dare ba cikin bedroom d'in sadiq wasan pillow suke haka shima ya shiga cikin su, wasan su ke cikin nishad'i haka shima sadiq ya biye masu shima kamar qaramin yaro suna haka har bacci ya kwashe su.
Ahankali yasa hannu ya bud'e wardrobe ya ciro picture d'in shi da kausar na maqale a qirjin shi a hankali wasu hawaye masu zafi suka zubo masa, yasa bayan hannu shi ya goge, bazai ta6a mance wannan ranar ba bayan sun gama wasan pillow shi da kausar suka je waje suna wasan ruwa, anan su kayi picture d'in da camera cikin sanyin murya ya ce, "I miss you my wife..! yana rungume da pic d'in har bacci ya dauke shi...
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...