Written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM
★We are the best★http/mobile.Facebook.com-Real-Hausa-fulani-writers-forumRHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R
*_Email_*
realhausafulaniwritersforum@gmail. com*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM
61_62Sai da ta gama gyara part din tsaf sannan ta koma kitchen, lokacin har farfesun yayi ta juye a kula tare da plate ta zuba a tray da bread a hankali take taka upstairs saboda ta cika tray din da kayan abinci, bakin kofa ta aje tray din sannan ta bude kofar ta shiga har cikin bedroom ta aje a stool qara leka fuskar sadiq tayi a qaro na biyu murmushi ta saki tare da zama gefan shi tana kallon yadda sajansa ya kwanta luf har mamakin kyau irin na sadiq take, sai dai yayi yar rama sannna fuskarsa tayi fayau dariya tayi ta ce "Ohni sangami ciwo yayi kamu kayi bulun buqwi tunda likita ya tsulama allura kaji zafi sai bacci kake, qila ma suma kayi saboda zafi, kai ma ka ji yarda naji ranan yadda kayi bacci kamar ba masifafe ba, amma da ka warke zaka fara cika mana gida da tsuwa, na huta da masifar ka ko ta kwana biyu ce uhm bari na lalla6a naje nayi wanka a toilet din ka tunda kai ka zama gawar shanu dan tashin ka ba yanzu.
Tashi fatuha tayi ta bude wardrobe ta ciro qaramin towel ta rage kayan jikinta tasa towel, duk wannan abun da fatuha ke duk a kunnan sadiq dan ya dade da tashi kawai dai yayi lamo ne, toilet din ta shige ta sheqa wanka ta fito ko da fito cikin sanda take tafiyar har ta qaraso gefe bed leqa fuskar sadiq tayi tana riqe da qaramin towel tana goge gashin kanta ta ce, Allah sarki ba wan Allah sai bacci kake baka san wainar dana ke toyawa ba wai da zaka tashi dana sha masifa, yarfe gashin kanta tayi wanda hakan yasa ruwan gashin ya watso ma sadiq a fuska dan motsa ido yayi hakan yasa fatuha zaro ido tare da yin lamo tana zare ido tana yarfe hannu ganin ya juya ya gyara kwaciyar shi ya sata sakin a jiyar zuciya, baki dressing mirror din shi ta tsaya tana kallon mayukan dake baje akan dressing mirror tsuru-tsuru tayi tana tunanin man da zata shafa can ta kai hannu kan wani mai na gashi kasancewa fatuha ba boko yasa ta d'auka ta fara shafawa sadiq dake kallon ta ta qasan ido sai dariya yake guntsewa, in taqaice maku duk wani mai dake saman dressing mirror sai fatu ta shafa dan taji ya mai kyau ya ke ji sannan ta fita daga d'akin, tana zuwa bedroom dinta kaya tasa sadiq dake d'aki dariya yayi sosai har da riqe ciki dan guntun saki ya ja tare da cewa "Yar kauye kawai..! Sannan ya tashi a hankali duk da har yanzu baya jin karfin jikinsa wanka yayi sannan ya fito yasa jallabiya ash mai kyau sannan ya gabatar da sallolin shi, yana idarwa ya qara koma wa ya kwanta dan karfin hali kawai yake.
Sket da riga tasa na atamfa mai ratsin dark green da coffee brown sai gyara gashin kanta da tayi tare da yin ture ka ga tsiya dauri, sannan ta qara fesa turare rufe bedroom din tayi ta fito sannan ta haura upstairs direct bedroom din sadiq ta shige kwance ta gan shi amma sai dai wannan lokacin idanuwan shi biyu murmushi ta saki tare da qaraso wajan shi cikin sanyin murya ta ce "Mai kyau ya jiki?" lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha jim yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau tamasa ba musanman dan qaramin lips din ta pick kauda kai yayi tare da cewa, "da sauki.! ya lumshe ido smile ta kuma yi tare da jawo tray dake saman stool ta cigaba da saving nashi cikin nutsuwa kasancewa tasan bai cin abinci bane sosai, shiyasa ta zuba masa farfesun yan cikin kad'an ciki dan boll,
Cikin sanyi murya ta kuma cewa "Mai kyau.! ware sexy eye's ball's din yayi ya qara sauke su kan lips din ta cikin shagwaba da sanyi murya ta ce, "Mai kyau dan Allah ka ci farfesun nan ka ga likita yace ka ci abinci" hade rai sadiq yayi tare da lumshe ido tare da yin magana cikin cool voice nashi ya ce "Bana jin yunwa fatuha" dan bata rai tayi tare da rausaya kai ta ce "Dan Allah kaga ko akauye idan bani lafiya idan banci abinci ba inna har dure take min, dan na samu lafiya ka ga yanzu Mom bata nan bale ama dure, dan Allah ka ci" ta ida zancan tana rausaya kai tana kallon sadiq dake kallon ta kamar qaramin yaro qara hade rai yayi ya ce "ba fa naci leave me alone pls" zaro ido fatuha tayi ta ce "Kai kasan wannan" murmushi yayi wadda bai yi niya ba ya ce "Fatuha wai yaushe zaki waye?" dariya tayi ta ce "Sai ranar dana fara zuwa boko ka ga da jidda nan ita ke koyamin yanzu kuma tana gidan Aunty bilki" ta ida zancan tare da yin raurau da ido sadiq ya ce, "ai ta kusa dawowa kin ji, uhm to kina san karantun ne? bai ida rufe bakin shi ba Dr yakub ya shigo, cikin sallama tare wurgawa sadiq harara dake kwance gaisheshi fatuha tayi har qasa sannan ta dau boll din farfesun ta aje a tray tana qoqarin fita doctor yakub ya ce, "ah wai fita zakiyi da kin tsaya ai" murmushi fatuha tayi ta ce "Ina da abinyi ne a kitchen shiyasa"
"ok.! wannan abincin fa nawaye? kallon sadiq tayi dake ta faman aika mata harara tayi tsaye tare da sada kanta qasa, juyowa Dr yakub yayi su kayi ido hudu da sadiq "mtww haba captain me yasa kake haka ne please, wai bana sha fada ma ba ka rage damuwa ba uhm saboda tsabar damuwa ka daurawa kanka hawan jini, me yasa kake abune kamar mara tawakali ai kowa ya sani duk me rai mamaci ne tunda kausar ta bar duniya ka daina walwala ka maida zuwa asibiti kamar zuwa kasuwa, haba captain ko dan lafiyar ka da matsayin ka ka hakura da wannan tunanin please," lumshe ido sadiq yayi kamar yakub na magana da dutse tsaki Dr yakub yaja ya ce "To wannan abincin da kaqi ci me hakan ke nufi?" ware ido yayi yana aika ma fatuha harara dan shi kwata-kwata baya buqatar wani abinci a cikin shi amma saboda tsabar naci irin na fatuha yanzu tasa sai ya ci abinci dan guntun tsaki yaja yana kallon yakub dake ta masifa yanzu "ka daure ka ci abinci ko nama alura ai dai ba saina fadama ila da alura kema mutun ba idan ba abinci ba" duk yadda ya so ya kauce ma qincin abinci sai da yakub ya takura masa ya sha farfesun kad'an ba tare da bread ba ba laifi farfesun ya masa dadi duk da bakinsa ba test aje boll din yayi fatuha ta dau tray din ta fita alura Dr yakub ya masa tare da daura masa ledar ruwa saboda ya lura sadiq baya san cin abinci yana lafiyar ma yaci kadan bale yanzu.Dawowar fatuha ce tasa Dr miqewa ya ce "To ni zan wuce dan Allah ki kulla da cin abincin shi idan bai ci ba ki kira Aunty bilki ki fada mata ai yasan halin ta" d'aga kai fatuha tayi sannan ta taimakamasa da daukar masa briefcase din har sai da suka zo bakin kofa ta masa sallama ta rufe gidan bedroom din sadiq ta kuma.
Tana dawowa harara ya bita da shi sannan ya ja saki murguda masa baki itama tayi tare da zama saman sofa sanin ba zai iya tashi ba yasa fatu haha sadiq ya ce, "keee wakike murgudawa baki? raurau da ido fatuha tayi ta ce "Bada kai nake ba"
"Dawa kike to? ya fada cikin sigar masifa "uhm ba da kai nake ba wallahi"
"mtww wallahi karki bari na tashi dan na tashi saina karairayaki, bama na hana ki yawo ba hijabi ba eh?
"amma ai a waje ka ce ba'a gida ba," tsaki ya ja, mtww sannan ya juya ya lumshe ido.
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...