CAPTAIN SADIQ

3.6K 163 9
                                    

Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM

                      69_70

👏🏽Godiya gare ku mosayan ❤wannan novel, ina jin dad'in yarda kuke comments😍 ana mugun tare irin sosai din nan.🤸🏽‍♀🤸🏽‍♀

    wannan shafin naki ne Maimuna Lawal Allah ya bar zuminci har ya'ya da jikoki Ameen🤝

         Fatuha na shiga bedroom ta aje ice cream din saman bedside drawer dan gabaki d'aya ice cream din yafita ran ta, a duniya ba abinda ta tsana kamar mai kyau yayi nisa da ita, ita kanta har mamakin hakan take jiki ba qwari ta ida cire school uniform tare da shigewa bathroom ta sheqa wanka ta fito, bayan ta tsane jikin ta tabi da lotion mai kamshi tare da sanya black after dress din ta mai stone's d'aure gashin kanta tayi kamar ganmo tare da murza yar hoda  da lipstick masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, fitowa tayi daga bedroom din ta wuce na Mom cikin sallama ta shiga mom Na tsaye gaban dress mirror tana shiri da alama fita za tayi cikin fara'a ta amsa fatu ta ce, "Mom fita zakiyi ne?"
        "eh wallahi zani gidan Ammi ne, dama yanzu nake cewa ko zaki raka ni? dan murmushi fatuha tayi itama tana san zuwa wajan Ammi din nan amma tunda ta zo sau biyu ta ta6a zuwa gashi tana san ganin Basma, amma Assignment ba zai bari ba gashi malam anjima zaizo ta  ce, "Mom kin manta yau wednesday,"
       "oh haka fa na manta fa shaf next time munje"
       "kuma wallahi Mom ina san zuwa Basma har ce min take bani da kirki bana zuwa,"
       "ai ta fada duk zaryar da suke maki baki zuwa masu kema kin fara koyan halin uncle din naki," dan smile fatuha ta saki mai cike da jin dad'i ita dai duk abinda za'a ce daga mai kyau yake so take ta  ce, "Mom ai baya san yawo uncle shiyasa"
      "ke kuma sai  biye masa kike ko, zuminci fa abin wasa bane" Mom ta ida zancan tana daukar handbag din ta kusan a tare suka fito, angel na zaune a parlour tana kallon cartoon ganin grandma zata fita yasa ta tashi tana cewa, "grandma zan biki please"
        "nope yau malam zaizo" zu6uro baki Angel  tayi gaba tana sanyin kuka ta  ce, "please grandma ki je dani," fatu  ta  ce, "angel kiyi hakuri grandma ta je kin ji, muma ranar Friday mun tafi kinji.! d'aga kai jidda tayi ba dan taso ba,  har bakin mota suka raka ta suka juyo.

    A dai-dai bakin kofa suka ci qaro da sadiq yana sanye da 3 quarter black da white t-shirt da alama gym zashi, kauda kai fatuha ta yi ala dole fushi take da sadiq, smile yayi tare da d'aga angel sama yana mata wasa tana dariya ko kallon inda fatuha take bai yi ba saboda ya lura yau rigima take ji, ra6awa tayi ta gefansa zata wuce ta cika taf qiris take jira ta fashe, ruqo hannu ta yayi hakan yasa ta tsaya chak a wajan, ta kasa kwace hannu ta sai binsa da take da kallo, aje jidda yayi qasa yana aje ta kamar jira take tayi cikin gida da gudu, fisgo da fatuha yayi ta fado saman fafadan qirjinsa har tana jin bugun zuciyarsa lamo tayi a qirjin nasa idanu ta  lumshe, a hankali ya d'ago da habar ta yana kallon ta lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha cikin cool voice dinsa ya ce "Fushin na menene uhm? dan 6ata rai tayi tana qoqarin zamewa daga jikinsa tunda bai san fushin me take ba, dan matse ta yayi da karfi ta saki yar qara, ta fara matsar kwalla kamar  jira  take  tana  binsa  da  idanu  ta cikin  tattausar  murya  sadiq  ya  ce, "daga nace zanyi tafiya sai fushi fatuha 3 days fa kawai zanyi kin ji dear," turo baki gaba tayi  ta  ce, "ni ba fushi nake ba"
      "to me kike?
"ba komai"
   "ok tunda ba fushi kike ba please ki had'a min kayana, na rasa kayan da zansaka kin riga kin shagwaba uncle da yawa," d'an zunburo baki ta kuma yi maicike da shagwaba sadiq  ya  ce, "please karki ce bakiyi"
      "zanyi mana"
"promise.!
    "promise..!
"good girl"ya sakar  mata  peck  a  goshi ya fita.

CAPTAIN SADIQ Where stories live. Discover now