Written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Raheenat📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★https//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial&_yn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITRESFORUM.com
*rip rip this page is for you my lovely one so enjoy the page this na for u no be so*😉
31_32
Washe da baki fatuha ta amshi jidda ta wuce da ita bedroom ta cire mata kaya, direct toilet ta shige da ita sai da ta wanke jidda tas sannan suka fito.
Wash Fatu ta ce, tare da cewa, "Ah bilahilazi birni tayi yanzu dubi sau biyu ina sab'e ki, ko gajiya bakiyi da wanka kamar kwad'o" jidda ce ta washe baki ta ce "Anuty daddy baya son dati shiyasa, always yake min wanka yayi ma kansa"
"uhm..! ta6e baki fatu tayi ta ce, "yo ke ki kasan wannan," washe baki jidda ta kuma yi ta ce, "baba na fa nake nufi Anuty"
"aiyo wai wannan baban naki ai dole yake wanka daga ganin shi ya cika tsirfa"
"daddy nawa"
"uhm shi fa, ke ni wani mai ake shafa maki idan anmaki wanka" smile jidda tayi ta d'auko mata lotion d'in ta mai kamshi fatuha ta amsa tana jujuyawa ta ce, "ah'ah wanga farin mai haka fa? yo ai wannan kamar turare ne" jidda ce ta fashe da dariya ta ce, "Anuty ba turare bane maine ga turare na chan saman dirss mirror wanda daddy ya siyo min a uk,"
"tir qashi me kuma uk? washe da baki jidda ta ce, "wata qasa ce haka"
"a'a ha shi baban naki har shawagi yake qasa-qasa ta6 kinga matso na shafe ki da mannan kar yaji shiru ya zo ya min tijara dan na lura dan ta kife ne baban naki" haka ko ta shafe jikin jidda da lotion tare da anyana man a ranta ita ma ta gama shafa basilin dan ita yanzu ta zama yar birni.Sai da ta gama shafe jidda da mai tsaf sannan jidda ta gwada mata inda night dress din ta suke kar ku ga abu komai fatuha ta gani sai ta mai sharhi, bayan ta gama shirya ta tsaf, sannan ta d'auke ta dan kai ta d'akin baban nata wanda tayi ma laqabi da sangami.
Direct part din Sadiq suka wuce a hankali ta murd'a handle d'in kofar ta shiga, jidda tana ta zuba mata surutu, tana shiga parlour ta saki baki da hanci bata san sanda ta dire jidda ba a qasa wani irin sanyi dad'i ne da kamshi ya doki hanci ta kasancewa sadiq mutun ne mai san sanyi da kamshi, shiyasa part d'in shi yafi na kowa sanyi a gidan, washe baki tayi tana qarewa parlour kallo saboda iya kar had'uwa parlour ya hadu.
Jidda ko bedroom ta shige da gudu lokaci sadiq ya fito daga wanka, sanye yake da bathrobe hannu shi riqe da towel, yana goge gashin kan shi jidda ta ruga ta rungume sa ciki da farin ciki ta ce, "daddy..! wani irin murmushi ya saki tare da shagwabe fuska ya ce, "uhm ni fushi nake da angel" tare da d'aukar ta ya zaunar da ita saman bed ya cigaba da cewa, "shine saboda kinyi new Anuty kika manta daddy ko angel? shagwabe fuska ita ma tayi tare da d'aura hannu ta saman cheeks d'in sadiq ta ce, "sorry daddy" ta marairaice kamar za tayi kuka, dariya yayi tare da fara yi mata cakulkuli, dariyar su jidda ta ankarar da fatuha washe da baki ta nufi kofar bedroom ta bud'e a hankali ta shige, zaro ido tayi waje tana kallan d'akin baki bud'e tana cewa, "kai Amma wanga gida ya had'u kwarankwatsi yanzu gobe ni zan gyara wanga gurin," baki ta qara washe wa duk wannan maganar tana yin tane cikin zuciyarta, sadiq dake ma jidda cakulkuli tana dariya jin kamar an bud'e daki an shigo yasasa da gowa a hankali, ya sauke sexy eye's ball's din shi kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata ita dinma shi take kallo tana aiyana irin kyau na sadiq a zuciyarta "ta6 amma dai sangami ba qaramin kyakyawa bane Qur'an" washe baki ta kuma yi ta ce "Amma fa sai bakin rai kamar fir'auna tir da wannan hali wallahi ga kyau ga bakar zuciya, ko da yake na kusa maganin shi ai," daka mata tsawar da sadiq yayi ne yasa ta dawowa daga dogon tunanin da take tayi wiqi-wiqi da ido, "you are very stupid ina maki magana kin yi shiru ehhh ? are u deaf or what" tsawar da sadiq ya daka wa fatuha har wani fitsari taji ya taho mata gadan-gadan ganin yana nufo ta yasa ta bud'e kofar tafita daga d'akin da gudu sai da taje dai-dai kofar parlour ta bud'e baki yadda zai jita ta ce, "Allah ya isa mugu kawai" sannan ta bud'e kofar ta ida fita a guje sadiq dake bakin kofar bedroom yana jin ta lumshe ido yayi yana jin wani irin tsanar fatuha na ratsashi da mamakin rashin kunyar ta ,a hankali ya ja jikinsa ya koma saman bed lokacin jidda har tayi bacci shima kwantawa yayi tare da kara masu gudun AC ya ja masu blanket.
Tana isa d'aki ta kulle da makuli gudun kar sangami ya shigo wato sadiq, toilet ta shige da gudu tayi fitsarin data matse saboda tsabar tsawar da sadiq ya daka mata shi ya haifar mata da fitsarin dole, tsoki ta ja tare da cire kayan jikin ta tayi wanka sai da ta wanke jikin ta tas sannan ta d'auki k'aramin towel ta daura ta fito, rigar baccin da Mom ta gwada mata ta ciro ta sa duguwar riga ce pink mai manyan follows milk rigar ta wuce gwiwa ba qaramin kyau tayi ma fatuha ba, ita kanta sai da ta yaba kyan rigar sannan ta kwanta saman bed tare da janyo blanket ta lullu6e ko 2 minutes ba tayi ba bacci ya sureta.
ASUBA TA GARI
tsaye yake gaban dress mirror yana shiri cikin uniform nashi kasancewa yau Monday ba qaramin kyau yayi ba, kofar bedroom ya kalla tare da jan tsaki sannan ya kalli bed jidda na bacci.Bangaran Fatuha ko yau bacci har da munshari ba ita ta tashi ba sai 6:00am, cikin sauri ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba tayi sauri ta zura uniform din ta, kasancewa Mom ta fada mata jidda na zuwa school shiyasa take shirin cikin sauri cikin sauri ta nufi part d'in sadiq dai-dai bakin kofa tayi tsaye gaban ta na dukan uku-uku saboda ta tuna artabun da suka sha da sangami jiya kawai shahada tayi tare da qundun bala ta bud'e kofar ta shiga tare da yin sallama, ba kowa parlour hakan yasa ta murd'a handle d'in kofar bedroom sadiq ta hango tsaye gaban dress mirror a hankali ya dago sexy eye's ball's din shi wani irin kallo ya wurga mata tare da jan tsoki, cikin tsawa ya ce "Yanzu ne time din da ya kamata ki shigo eeh? baki san tana zuwa school bane, koko rashin sanin muhinmanci ilimi yasa kika zauna baki zo ba eeh? nuna ta yayi da yatsa ya ce, "as from to day karki qara kai wannan time din baki zo ba stupid girl kawai" duk da bata san Kalmar da ya fadi aqarshe ba amma jikin ta ya bata zagin ta yayi sai da ta fakaici idon sa sannan ta bala masa harara tare da d'aukar jidda daga saman bed zata fita da ita har ta kai bakin qofa, ya kara daka mata tsawa ya ce "Kin makarar da ita yanzu Kuma ina zaki kaita? oya wuce ki mata wanka a bathroom d'ina" wiqi-wiqi da ido fatuha tayi dan ita bata san me ye bathroom ba, wata uwar tsawa ya kuma daka mata y'all ce, "oh waike wace irin yarinya ce ehh ki kai ta ban d'aki na kiyi mata wankan yar qauye kawai mtss, saura kuma inkin je kinmin kauyan ci" jiki ba kwari fatuha ta shiga toilet din ba laifi dan kauyanci da tayi kadan ne sannan tayi ma jidda wankan, tana mata tana zuba mata surutu d'auke da ita ta fito sannan ta zauna da ita saman bed sadiq na zaune saman sofa yana kallonsu shafe jikin jidda tayi da mai sannan ta dau uniform din jidda zata sa mata nan fa kar ku ga zare ido dan ta rasa ta inda zata samata rigar saboda gown ce irin mai kamar biri da wando d'inan tayi tsuru-tsuru, sadiq jan tsaki yayi tare da fisge rigar ya shiga sama jidda fatuha duk tana kallon yadda ya ke samata sai da ya gama shirya jidda sannan ya mata peck ta ce, "daddy good morning"
"morning too angel how was ur night,?
"cool daddy"
"good" fatuha ko sakin baki tayi tana kallon su.Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan sadiq ya d'au briefcase din sa, fatuha kuma ta d'auki jidda suka sauko downstairs Mom da Abba na zaune a dining area har sun fara breakfast cikin ladabi sadiq ya gaishe su haka ma fatuha da jidda Mom ce ta kalli fatuha washe da baki ta ce "Ya kwanan baqunta?" murmushi fatuha tayi tare da jama jidda kujera ta zauna cikin natsuwa ta shiga saving din jidda abinci, da ta gama sai ta zauna shima cikin dari-dari sannan ta sa hannu cikin plate d'in wata irin tsawa sadiq ya daka mata wadda tasa fatuha fara matsar kwalla, cikin kakausar murya yafara cewa "Wai bana ce maki ki daina feeding din angel da hannu ki bane eeh" Mom ce ta kalle shi tare da wurgamasa harara take ce, "baby wai me yasa ka ke haka ne eeh" fada ta masa sosai sannan shima Abba ya dasa da cewa, "Kai haka ake a rayuwa? kai kullun cikin zafin rai sadiq wai me yasa baza gyara halin ka bane eh baby? kullun ciki rigima da masu aiki" shiru sadiq yayi tare da aikawa fatuha harara ita ko tayi kamar bata gani ba sai ma gwalo da ta aika masa cikin nutsuwa suka gama breakfast.
Briefcase din sa sadiq ya d'auka fatuha na d'auke da jidda suka fito harabar gidan, haka fatuha ta rinqa zare ido tana qarewa yaran sadiq kallo *ola* ne ya qaraso cikin sauri tare da amsar briefcase din sadiq ya kai masa mota fatuha na biye ta shi suna zuwa gaban mota fatuha ta aje jidda cikin mota , zata juya sadiq ya fisgota ta fado jikinsa, da sauri ya ture ta tare da taka mata qafa da booth din kafar shi ya murzashi sosai, jin za tayi ihu yasa ya matse mata baki da hannun shi da karfi yana kallon ta ido cikin ido ,idanun fatuha sun cika da kwalla taf saboda ita kad'ai tasan azabar da take ji, ture ta yayi tare da nunata da yatsa ya shige motarsa har zai tada yajiyo muryarta tana magana da yake ahankali take magana shiyasa baiji abinda take fadi ba, kwafa yayi ya tada motar suka bar harabar gidan, fatuha ko Allah ya isa ta shiga jeramasa tana kuka tare da shigewa gida a guje.
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...