CAPTAIN SADIQ

2.9K 152 12
                                    

Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

             
                     79_80

     Ko da fatuha  ta shiga class ba wani walwala, haka su Nana suka dinga tanbayar ta mai ke  damunta ta fada masu meke damun ta, amma firtaqi gaya masu damuwar ta, Nana ce ta ce, "fatuha kenan baki daukemu a matsayin qawayan ki ba ko wayanda  zamu  kashe  tare  mu  birne  tare ba? Shiyasa zaki boye mana abin da ke damun ki" Zara ce ta budi baki ta ce, "Kyale ta Nana ai dai mun san matsayin mu yanzu, bai  zama  dole  ta  fada  mana damuwarta  ba" Zara na qoqarin jan Nana subar seat, fatuha ta riqe Zara ta  ce, "please kuyi hakuri, zan fada maku damuwa ta.! ta ida zancan hawaye na sulalo mata, duk abin ya faru haka fatuha ta kwashe ta fada masu ta  karashe  zancan  da  cewa, "ina  son  captain  so  mai  tsanani  wanda  ke  tafiya  tare  da  bugun  numfashina  amma  sai  gashi  lokaci daya" kuka fatu  ta  saki mai  cin  rai ta  fada  jikin  Nana tana  gunjin  kuka, Zara taji haushi ba kadan ba haka  suka dinga bama fatuha hakuri tana raira kuka dakyar suka shawo kanta.

         Bangaran majeed ban da dad'i ba abinda yake ji, zuciyar shi fes take daya lumshe ido kyakyawar fuskar fatuha yake hagowa sai ya qara sakin smile, matsala sa  daya  da  fatu  ta  kasa  sakewa  da  shi.

      Jingine yake saman kujera office ya rasa sukuninsa, idanuwan shi na lumshe saboda nauyin da suka masa har wata masasara ke rufe shi ga wani  irin  zafi da qirjinsa ke masa, tamkar  an  daura  masa dutse  mai  nauyi a hankali ya ware sexy eye's ball's dinsa da suka rine sukayi jaa wayarsa dak'e ruri cikin aljinhunsa ya curo sabuwar number ce baro-baro a screen din, da kamar ba zai dauka ba sai ya daure ya dauka tare da karawa a kunne, daga  dayan  bangaran cikin zazakar muryata cikin yauki Basma ta masa sallama, amsawa yayi a taqaice tare da tanbayar, "wake magana? gyara kwanciyar tayi daga inda take tare da kankame wayar dan wani irin sanyi ke ratsata, dan gyaran murya tayi cike da shagwaba ta ce, "Yaya sadiq ni ce fa Basma..! ko number ta ashe baka da ita? ta ida zancan cikin shagwaba Sadiq dake kishingide saman kujera, ranshine ya qara suya dan shi duduniya ba macan dake birge shi ko bashi sha'awa kamar fatuha, ko wannan magana ma da take yi jiyake kamar tana watsa masa ruwan zafi,  tsuke fuska sadiq yayi kamar tana ganinsa ya ce, "Yanzu ina wani aiki ne letter mayi magana idan na dawo gida" bai jira cewarta ba ya katse wayar tare da yin wurgi da ita ta daki bango ta dawo watse ko ta kanta bai bi ba ya sa kai ya fice daga office din, domin idan ya cigaba da zama tabbas kwakwalwar shi da zuciyarsa suna iya bugawa.
            bin wayar tayi da kallo tare da dan bata fuska, ta aje wayar ta kwanta.

    Ko da aka tashi su fatuha majeed ne ya zo daukar su, ganin shine yasa ta had'a gira sama data kasa dan ba abinda ta tsana kamar ganinsa, ba yadda ta so haka ta bale murfin motar ta shiga tare da gaishe shi, kallon ta yake mai cike da so da kauna, sannan ya ce "My love daga gani yau kin sha wuya da yawa? ina fata dai kina kulla min da kanki?" dan guntun tsaki fatuha ta ja ciki-ciki sannan ta ce a cikin zuciyar ta "Har wani kira kake na kulla ma da kaina mtww dan iska kawai" muryar  majeed ce ta doki dodan kunnan ta a karo na biyu ya ce, "My love! ko duk gajiyar ce tasa ko magana ba'a san yimin?" dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi la66an ta ta ce "A'a" murmushi majeed yayi tare da cigaba da driven, haka ya dinga janta da surutu tana amsa masa sama-sama sannan ya wuce da su shoprite yayi masu siyaya ice cream da cake, jidda ko sai dadi take ji dan har yanzu bata san inda aka dosaba.

CAPTAIN SADIQ Where stories live. Discover now