CAPTAIN SADIQ

3K 147 12
                                    

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red opare-speed_dial_yn_=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com

                           35_36

    A hankali ya murda handle d'in kofar toilet ya zura kafar shi ji kake suuuu gwajaf yayi fad'uwar yan bori, fatuha da ke maqale bakin kofa ta kasa kunne jin fad'uwar sadiq ya sata bushewa da dariya har da rawar tanbola dan shauqi, bud'e kofar tayi ta shigo bedroom tana shigowa ta qara fashewa da dariya, saboda zaman da sadiq yayi a qasan toilet qarasowa tayi bakin kofar toilet din, a hankali sadiq ya dago sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata dariya ta kuma saki tare da bala masa harara ta  ce, "ah mai kyau ansha qasa..! dariya ta kumayi tare da gyara tsayuwa ta  ce, "toh mai kyau bari na kirama hajiya ta kirama mai d'auri saboda nasan ka goce koka kare  dan  ba  karamar  faduwa  nasan  kayi  ba" ta qara bushewa da dariya, sadiq ko cije lips yayi yana jin wani irin rad'ad'i da tsanar fatuha na ratsa sa, kenan  ita  tasaka  masa  mai  a  toilet  dan  ya  fad'i kallon banza ya wurga mata yana qoqarin tashi amma ya kasa wani irin rad'ad'i qugunsa ke masa dan  ba  karamar  fad'uwa  yayi  ba  sosai  yake  jin  rad'ad'i a kugunsa, cije lips yayi ya zauna dan baya iya tashi dariya fatu take saki  ganin  yarda  yake  cije  le66e yana  rinrintse ido ta ce, "Kwarankwatsi baka iya tashi Qur'an ka bugu ba kad'an ba qila ma ka kare ko ka goce", dariya ta kumayi ta nuna idanuwan ta da yatsu biyu sannan ta nuna idon sadiq wanda ke binta da kallon tsana sa'a  kawai  yake  nema  ya  wawuro  ta  ya  cigaba  da  duka saboda  ya  kai  maqura iya  maqura, daure fuska tayi ta ce, "ka tuna turani da kayi d'azu a matatakala na fadi? toh Allah ya isa  ba kasan wacece fatuha ba ko? kaje kauyan wudil ka tanbayi *wacece fatuha diyar Baffa jauro qawar fatsima*, sannan ta qara fashewa da dariya ta ce "Kuma daga yau zan fara nuna ma irin kala haukar fatuha, kuma wallahi kasani fatuha ba'a mata abu ta hakura ko ta dangana, d'azuma a lokaci ba hakuri nayi ba shi yasa na rama," ta bala masa harara tana qoqarin fita, sadiq ko wani miyan bakin ciki ya hadiye yana jin wani irin bakin ciki ,ji yake kamar ya tashi ya shaqe fatuha har sai numfashin ta ya kusa daukewa ya sake ta lumshe idanuwansa yayi zuciyarsa  na  masa suya  da  tafarfasa  tamkar  garwashi, yana  matukar  mamakin  yarda bagidajiyar yarinyar bata  shakar sa tunda Mom  ke  kawo  masu  aiki  bai  ta6a cin  karo  da  mai  aiki  irinta ba, alwashi ya  d'aukarwa kansa  sai  ya  gyarawa yarinyar  zama  ko  yana korata.

         Washe da baki fatuha ta fito daga part d'in sadiq  jin  zuciyarta  take  fes  tamkar  an  zuba  k'ank'ara sai da ta daidaita kanta sannan ta fara matsar kwallar gulma, bedroom d'in Mom ta nufa tana yarfe hannu  a hankali ta bud'e k'ofar d'akin Mom ta hango kwance saman bed tana karanta azkar, cikin nutsuwa ta shigo tana matsar kwalla Mom ce ta d'ago su kayi 4eye's da fatuha murmushi ta saki tana qoqarin tashi  zaune ta ce, "fatuha qaraso mana" jikin kofa ta qara maqalewa tana matsar kwallar gulma dakyar ta iya furta, "Mom dama baban jidda ne ya ce na kawo masa ruwa ina shiga dakin na ganshi ya fadi a kewaye kuma ya kasa tashi" tana ida zancan ta fashe da kukan munafurci Mom tashi tsaye tayi cikin tashin  hankali a rud'a ta  ce, "muje bedroom d'in nashi naga ko lafiyar baby" Mom na gaba fatuha na baya tana aika gwalo suka shige part din direct bedroom d'in sadiq ta shige yanan zaune inda fatuha ta barshi yayi-yayi ya tashi amma ya kasa Mom ce ta qaraso tare da kiran sunan shi cikin damuwa ya juyo yana kallonta fatuha na bayan Mom tana matsar kwalla da sun hada ido da sadiq ta aika masa gwallo shikuma ya aika mata harara Mom  ta  ce,  "sannu baby kaji bari mu taimaka ma ka tashi,"
          "no Mom ba ku iyawa a miqomin phone d'ina tana saman stool na kira *ola* da *Sunday*" cikin sauri Mom ta miqa masa wayar fatuha na gefe ra6e zuciyar ta fes.

    Bugu daya biyu *ola* ya daga kiran sadiq, sadiq ya sheda mashi yana neman su, shi da *Sunday* cikin sauri suka qaraso  bedroom din, ganin su Mom tsaitsaye yasa jikin su *ola* yin sanyi hango sadiq su kayi zaune a toilet yayi zaman yan'bori a hankali *ola* ya qaraso tare da gaida Mom cikin hausar su wadda bata fita amsa masu tayi sadiq a hankali ya ce, "*ola* taimaka min na tashi kai da *sunday*"
      "OK boss" Sunday da ola suka taimaka ma sadiq ya miqe suka d'aurashi saman bed  Mom sai sannu take masa itama fatuha sannu ta masa wani irin mugun kallo ya mata, ya kauda kai Mom ce ta ce, "baka ji fatuha na ma sannu bane" lumshe ido yayi tare da ware su ya ce, "ban ji ba.! ya qara maida idanuwan shi ya rufe, wayar shi Mom ta curo ta kira doctor yakub ba ayi  minti 39ba sai ga doctor yakub riqe da briefcase din shi ya shigo, fatuha ta masa isowa har bedroom din sadiq gaida Mom yayi sannan ya shiga duba sadiq tare da tataba inda ya bige sannan yayi yan rubuce-rubuce, gyaran murya yayi ya ce, "Alhamdulillah  buguwa ce amma bai goce ba kuma bai kare ba, abin ya zo da sauki"  murmushi Mom tayi tare da hamdala, sannan doctor ya bashi magani da ze shafa da kuma na ciwon jiki  sannan yayi ma su mom sallama ya tafi, Mom da fatuha kuma suka fita.
             cikin cool voice nashi sadiq yace da ola ya taimaka ya kai shi bathroom ya watsa ruwa amma ya fara goge man da ke zube a toilet sai da ola ya wanke toilet din tas sannan ya taimakawa sadiq ya shiga toilet,  ola na bakin kofa yana jiran sadiq yana gama wanka ya kira ola ya taimakamasa ya fito ko da ya fito ola ya fito masa da jalabiya milk bayan ya gama shafe jikin shi da mai sannan ola ya taimakamasa ya shafa masa magani sannan yasa jalabiya ya koma saman bed ya lumshe ido ,ola ne ya 6alo magani da ruwa ya bashi ya sha yana gama sha ya lumshe ido bacci mai nauyi ya d'auke sa, ola ya koma saman sofa ya zauna Sunday kuma ya kwashe kayan da suka baci da mai  ya fita.

  Fadawa  gado  fatu  tayi  ta  ce, "Wash Qur'an yau nayi aiki inama a ce fatsima na kusa" ta qara bushewa da dariya, ta kalli bed jidda na kwance tana sharar bacci dariya tayi ta ce "Allah sarki angal wato(angel) yau na naqasa baban ki sai hakuri angal na san in zafi yayi zafi har sunnan ki sai ya fada" ta kara fashewa da dariya tare da rausayar da kai to ce, "Amma fa gaskiya ban duba masa ba" ta ida zancan tana cire kayanta ta shige toilet tayi wanka d'aure da towel ta fito lokacin jidda tatashi, murmushi tayi ma jidda tare da d'aukarta dan lokaci 4:00pm saura malamin jidda ya kusa zuwa wanka ta mata a tare suka fito suka shirya sallah su kayi saboda anata kiraye-kirayan sallah bayan sun gama sallah fatuha ta rako jidda har waje lokaci har malam ya zo ji tayi itama tana sha'awar karatun, cikin gida ta juya tare da shiga bedroom din Mom, Mom na zaune saman daduma karasowa tayi tare da murmushi ta tanbayi Mom itama tana so  ta fara zuwa malam na qara mata karatu Mom ta ce, babu komai ita  ma  ta  je washe da baki ta fita, taje wajan malam itama ba laifi fatuha ta d'an san sururi da yawa sai dai karatun nata ba tajweed shine kad'ai ya d'an bata karatun ba laifi sunyi karatu sosai inda fatuha ta nutsu tana ta karatu, dan wannan malamin ba karamin malami  bane.

     Bayan sun gama karatu misalin karfe 6:00pm suka shigo gida cikin farinciki, Mom na zaune saman three star tana kallo abba na gafenta gaishe su tayi cikin nutsuwa sannan ta shige daki jidda kuma ta fada jikin Abba tana zuba masa surutu kiran sallar magrib ne ya sa Abba tashi ya wuce masallaci, jidda kuma ta shige bedroom lokacin fatuha ta fito daga toilet daure da alwala, murmushi fatuha tayi ta ce, "Jidda yi maza kiyi alwala kiyi sallah kiyi ma baban ki addu'a, bai da lafiya kinji"  waro ido  jidda  tayi ta ce, "Anuty me ya samu daddy" take Ida  zancan tare da rugawa wajan kofa zata fita, jawo ta fatuha tayi ta ce, "yi hakuri mu fara yin sallah sai na kai ki kinji jidda" toh tace mata tana matsar kwalla fatuha kuma na lallashin ta.

    Bayan sun gama sallah fatuha ta shirya jidda cikin night dress din ta blue n white wando da riga ba qaramin kyau su kayi mata ba, ta ja hannu ta suka wuce part din sadiq.

       Suna Shiga suka samu ola zaune saman sofa, sadiq ma zaune saman bed, yana shan coffee da gudu jidda ta fada jikinsa tana kuka ta  ce, "daddy..! lallashin ta ya shigayi yana  cewa, "angel menene yake damun ki? bata fuska tayi ta ce "Daddy ashe baka da lafiya shine baka fada min ba? ta ida zancan tana matsar kwalla sadiq y'all ce, "sorry angel lafiyar daddy qalau, waya fada maki daddy bai da lafiya? fatuha ta nuna da ke manne jiki kofa kamar ka ce tak ta arce wani irin kallon tsana ya gefa mata tare da qaqaro murmushi yayi wa jidda yana kallonn fatuha ya  had'e  rai  tamkar yayi  bindiga ya  ce, "angel na rasa yadda akayi grandma ta samomaki new Anuty mahaukaciya" ya ida zancan yana kallon fatuha ido cikin ido, kauda kai tayi tare da turo baki gaba angel tattoo ce, "daddy new Anuty ba mahaukaciya bace ba"
       "injiwa ya ce maki ba mahaukaciya ba ce" fatuha ko wani irin tsoki ta ja tare da jan kofar bedroom da karfi ta fita lumshe ido sadiq yayi yana tunanin irin hukuncin da zaiyi ma fatuha in ya tashi...

CAPTAIN SADIQ Where stories live. Discover now