CAPTAIN SADIQ

4.3K 221 0
                                    

written
     by
        Salma mas'ud nadabo

    Edit by
        blood sister deejah

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

                       3_4

Kaitsaye bedroom nashi ya wuce komai na bedroom d'in golden colour ne wani makekyen gado ne atsakiyar d'aki wanda ke kama da ba a kwanciya a saman shi, dan komai na d'aki very neat ne dressing mirron din shima abin kallo ne kayan shafa ne kamar suyi magana dan yawa,  perfume kam ba'a magana da man gyara gashi tsayawa lusafa maku haduwar d'akin 6ata lokaci ne, kayan shi ya fara cirewa
ya shige toilet, wow toilet d'in ma abin kallo ne dan ya had'u iya had'uwa baifi  30 minutes ba ya fito d'aure da towel a qugun shi d'aya kuma yana goge gashin kanshi da shi dressing mirror ya nufa ya shafe jikinsa da mayuka masu kamshi tare da gyara sumar sa da sajan shi wardrobe nashi ya bud'e, wow wardrobe din ma abin kallo ne saboda kaya ne a ciki kamar gurin saida kaya suit kala2 da uniforms d'in shi na sojoji kamar suyi magana da yake shi mutun ne ba mai yawan sa manyan kaya ba, dan haka k'ananan kaya sunfi yawa hannu yasa ya ciro T-shirt din shi white mai gajeran hannu da 3quarter black,  ba k'aramin kyau yayi ba haka yasa kyan shi ya bayana sosai agogo ya mak'ala ma hannu shi mai tsada silver na azurfa har ya kai bakin kofa phone nashi ya fara ringing wayarsa kira iPhone 7 white chak ya jaa ya tsaya hannu ya kai saman dressing mirror nashi sweet Mom ne rubuce a screem d'in phone din ahankali yasa hannu ya  d'auka ya  ce,  "hello Mom..!
  "son na d'auka bacci ya d'auke ka?
   "no mom yanzu zan fito"
"ok..  datse kiran tayi daga dayan bangaran  cikin isa yake saukowa daga steps  hannu sa d'aya cikin aljihu Jidda dake dining ce ta rugo da gudu ta rungume shi ta ce, "daddy welcome back..!  d'aga ta sama yayi yana mata wasa tana dariya har suka qaraso dining tana rik'e a hannu shi Mom sai murmushi take ita tayi serving d'in su  shinkafa ce da miya wadda taji kaji da namomi  da ganyaye  cikin kwanciyar hankali suke cin abincin, wadda sadiq da kanshi yake feeding Jidda itama tana feeding nashi yarinya ce wadda baza ta wuce 4 years ba chocolate Colour ce mai kyau da ita gashin kanta yasha gyara sanye take da gwon pink mai dan siririn hannu, yadda sadiq ke bata kulluwa hakan zai gwada ma ba k'aramin ji yake da ita ba, Mom dake zaune tana Kallan su sai taji tausayin Jidda ya kamata, da shi kanshi d'an nata Jidda ce  ta  katse shuru da cewa, cikin muryar ta mai tsamin, "daddy Ina tsaraba na? kallan ta yayi yana murmushi ya lakace mata hanci ya  ce, "sweetheart ki bari daddy ya gama lunch mana" baki ta turo gaba ta  ce, "Uhm daddy na k'osa naga tsaraba ne"
   "Uhm na sani swetheat bari mu gama tukun" Mom ce ta washe baki ta  ce, "ke dai baki gajiya duk san da yayi tafiya fa sai ya maki tsara"
   "to ai  grandma  Ina so ne" ta ida zan can tana turo baki
"ke ko Allah ya shirye ki" cewar  Mom duk hiran da suke idan sadiq nakan little daughter d'in shi wadda ya ke jin ta har cikin ranshi sadiq  ya  ce, "oya cigaba da cin abinci sweetheart mu gama na baki tsaraba ki, sannan muje shan ice cream ko dear"
   "yes dadd.! haka cikin wayau ya samu yayi feeding nata.

                       *******
       Fatsima da fatuha ne tafe antaso daga makarantar allo suna tafe suna tsoka dan wannan ya zamar masu jazaman, in antashi daga makaranta sai sunyi tsokana san ransu suke komawa gida, wata Rana da kuka wata rana da gudu suke komawa gida yau kam a guje suka koma gida, fatsima ta shige gida fatuha ta shige gidan su baffa ne zaune bisa tabarma Inna na gefe tana zuba mai ruwa abuta saboda magrib ya kusa, fatuha ta kunno kai tare da sallama ta yarda hijabin ta k'asa baffa ya bita da kallo, washe baki tayi ta ce, "baffa sannu da gida"
  "yauwa yar albarka, an dawo daga makaranta kenan?
   "eh baffa"
"yauwa ya karatun"
    "lahiya lau baffa"  taje ta amshi buta da ke hannu inna ta kawo ma baffa yayi alwala ya wuce masallaci bashi ya dawo ba sai bayan isha'i, inna da fatuha na zaune suna cin tuwan dawa ta miyar kubewa wadda tasha man shanu baffa ya shigo da sallama, fatuha ta ruga da guda ta rungume shi "ah'ah zaki karya ni fatuha wai ke baki san kin girma ba" baki ta turo ta  ce, "gaskiya baffa ban girma ba"
   "to naji" ya ja hannu ta suka zauna bisa tabarmar da Inna ke zaune murmushi inna tayi ta tashi ta shige madafi ta d'auko kwana abinci Malam ta aje mai yana samata albarka bayan sun kamala cin abinci fatuha ta kwashe kwanikan ta dawo ta zauna kusa baffa ta  ce, "baffa..!
  "na'am fatuha"
"Baffa Ina so gobe na bika gona dan Allah"
"makaranta fa fatuha" baki ta turo  gaba ta  ce, "ai gobe litinin baffa ba ta sahe" inna da ke gefe ta ce, "toh fatuha kin san sai 5:00 Malam ke dawowa ki bari sai ranar alhamis ki bishi kin ji" kwalla ta Fara matsewa baffa ya ce, "yi hakuri ki shirya goban sai muje ko" washe baki tayi dan ita akwai abinda take san daukowa a gona shiyasa zata bishi inna ce ta katse mata tunanin da cewa, "haba Malam wai me yasa kake biyewa fatuha dan Allah, taita sangarcewa"
   "kinga ladingo bana san haka haba dan Allah, Allah ya bamu yarinya sai baza mu faranta mata ba, mun dad'e muna san yara Allah bai bamu ba sai yanzu, yanzu kuma ya bamu sai muki faranta mata, gaskiya bazaiyu  ba ladingo, ke ma kin fara d'aukar maganar mutanan waje Kenan, toh yayi ni dai ba maimatsa ma d'iyata akauyan nan" kyale shi ladingo tayi ya ida zan can tare da d'aukar fatuha wadda tuni bacci ya kwashe ta inna ta bishi da ido tare da kwashe tabarmar tsakar gida.

                         ****
      After dinner mom da sadiq ne zaune a palour suna kallan news Jidda na kwance  jikin shi, da alama tana wasa bacci ya d'auke ta Teddy's d'in ta a baje cikin palour baba jummai ce ta leko daga d'akin ta ta zo ta fara kwashe kayan wasan tana kaiwa d'akin jidda dakine mai kyau fadi tsaruwa dakin 6ata lokaci ne sai da ta gama kwashewa ta zo d'aukar jidda dake mak'ale da baban ta sadiq  ya ce, "ah baba barta yau tare zamu kwana"
   "to shikenan maigida bari na mata wanka nasamata kayan bacci"
  "to shikenan" ya miqa Jidda  Mom ta juyo ta kalle shi tana sanyin magana amma ba tasan 6acin ran son shiyasa taja bakin ta tayi shuru, can ta ce, "ni ko baby aikin da baba jummai take bai mata yawa ba, gashi ba yarinya ba ce"
  "haka ne Mom tunda Mary ta tafi ba a kawo wata ba, ni wallahi Mom tsoran d'aukowa sweetheart wata yar aikin nake duk  basu  iya  komai  back wallahi" ya ida zancan yana 6ata fuska  Mom  ta  ce, "ya zamuyi dole a samo wata  saboda aikin ya mata yawa"
  "to shikenan duk yadda kukayi ki fad'a min"
   "to.. kun koyi waya da abban ka"
  "yes munyi jiya lokacin yana airport yace sai yayi 2weeks zai dawo"
   "eh haka kasan har yanzu suna magana kan kwangillannan ne"
   "eyya to Allah ya taimaka"
Mom ta ce, "amin gobe kai da Jidda in ka dawo daga wajan aiki ka kaita gidan sister ka ya kamata ka leka, ka bama su hanan tsaraba su ko"
   "tam bari mu gani idan na dawo da wuri  sai muje" sai ga baba jummai dauke da Jidda ya amshe  ta yayiwa  Mom sai da safe..

CAPTAIN SADIQ Where stories live. Discover now