CAPTAIN SADIQ

3.1K 136 0
                                    

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*fan's ana mugun tare dinnan sosai*🤝🏽

                      39_40

Bayan ta gama ma jidda wanka ta shafe ta da mai tare da saka mata kaya jeans n t-shirt riga pink wando bleu sannan ta gyara mata gashin ta, tuni jidda ta fito tayi kyau masha Allah, toilet ta koma ta d'auro alwala kasancewa 4:00pm tayi ita da jidda suka gabatar da sallah suna idarwa fatuha ta cire veil din kanta tana kallon gashin ta a mirror tana washe baki, jidda ce ta ce,  "Anuty gashin kine haka? jiyowa fatuha tayi washe da baki ta ce,  "kema kin gani ko? Ai Allah daga yau na gama yawo da d'ankwalli wallahi wannan gashi kamar ba nawa ba"
             "gaskiya Anuty kina da gashi dama ki qaramin.! Jidda ta ida zancan tare da washe hakora murmushi Fatuha tayi tare da maida dankwallin ta jawo hijabinta dana jidda suka  wuce wajan malam.

           Sosai suke karatun, damma karutun ya zo ma fatuha da sauki dan duk wani qari da malam ya mata jiya ta juye masa shi, shi kansa yana yabawa da qoqarinta,  qara musu yayi, dan haka basu suka shiga gida ba sai 6:00pm

    Sadiq dake tsaye gaban dress mirror yana gyara sumar shi a hankali ya ji an bud'e kofar dakinsa, cikin zafi rai ya juyo a tunaninsa fatuha ce ta zo masa da wani sabon rainin sai kuma idanuwansa ya gane masa majid.😀
   6ata fuska yayi tare da juya masa baya yana  mai  cigaba  da  shirinsa  cikin  nutsuwa, smile majid yayi ya qaraso with full confidence nasa ya  ce, "big man fushi kake dani ko?
   kauda kai sadiq yayi ya nufi wajan drawer yana ciro kayansa murmushi majid yayi tare da zama saman sofa, tsaf sadiq ya gama shiryawa fuskarsa daure ya dau phone nashi da ke bedside drawer, zai fita majid ya riqe masa hannu tare da shagwabe fuska ya  ce, "sorry bros.! juyowa sadiq yayi ya wurga masa harara ya  ce, "leave me alone..! tare da fisge hannusa zai murda handle na kofa kenan majid ya ce, "haba  sadiq am sorry nine fa majid" juyowa sadiq yayi yana kallonsa ya qara bala masa harara ya  ce, "kasan da haka shine ka manta dani ko?
         "sorry kasan bana zama sosai shiyasa amma ai na kusa dawowa nan da aiki, ka ga dawo ka zauna muyi magana"  Jin hakan yasa sadeeq sakin handle d'in kofa ya dawo ya zauna majid ya  ce, "baby me ya samu qafar ka naga kamar kana d'ingishi?
  jan tsaki sadiq yayi ya ce "tsautsayi ne kawai"
         "eyya sorry " sadiq ya  ce, "Tashi muje parlour na gaji da zama a bedroom"
          "OK.. Majid yace
parlour suka koma suka dasa sabuwar hira basu suka daina hira ba sai magrib, dauro alwala sukayi tare da wuce wa masallaci

"Aunty..!
       "na'am.!
              "dan Allah ki koyamin qarin d'azu ban iya ba sosai,"
        "to shikenan nima zaki koya min na boko ko?
       "eh zan koya maki mana Aunty"
"To bari mu fara yin sallah"  Tashi sukayi tare da dauro alwala suka gabatar da sallah  bayan sun idar fatuha ta qara biyawa jidda karatun sannan jidda ta fara koyawa fatuha ABCD karku so ku ga kwamacala dakyar-dakyar ta dan iya shima ba sosai ba amma tasa ma ranta sai ta iya ko dan ta dinga jin abinda sangami ke cewa wani lokacin.

Bayan sun dawo masallaci majid ya fad'a two sitar ya  ce, "wash am tied..!
Guntun tsaki sadiq ya  ja  ya ce "kai dai kam ka bani daga zuwa masallaci har ka gaji sai ka ce ba namiji ba mtss..!  fruit ya curo a fridge ya fara ci majid ya zuro hannu suna ci suna hira majid  ya  ce, "ni fa na fara gajiya da wannan gwarancin aura zan zo nayi wallahi.! smile sadiq yayi ya ce, "aiya kamata kam dan  gaskiya  ka  dade  ba  aure"
      "aikai ma ya kamata kayi wani auran sadiq, duba da yau kusan shekara kausar 5 da rasuwa sadiq, ya kamata kayi aure haka ko saboda angel..! 6ata fuska sadiq yayi ya ce,  "majid bana tunanin zanyi wani abu wai shi aure yanxu, tunda na rasa kausar na rasa wani 6ari na rayuwata, majid kafin a samu mata kamar kausar sai antona, kausar tatara komai dana ke so agun mace, bana tunanin akwai wata ya'mace da zata iya maida gurbinta" ya ida zancan cikin  sanyin  murya hawaye masu zafi na zubomasa kallon tausayi majid ya masa cike  da  lallashi  ya  ce, "sorry baby na famama inda kema ciwo ko? girgiza kai yayi tare da goge hawayan idanusa da bayan hannu  yayi smile ya ce, "majid baka famamin komai ba, indai tunanin kausar ne ba yau na fara ba, yau kusan 5 year da ita nake kwana da ita nake tashi majid.! murmusawa majid yayi tare da qoqarin canza topic dan a duniya ba abinda ya tsana irin damuwar sadiq haka shima sadiq ba abinda ya tsana irin damuwar majid, kallon ball suka shiga yi tare da yin musu dama sun saba ba yau suka fara ba danma yanzu sun girma ne, da da ne har kuka sai Sadiq ya sa majid cikin nishad'i suke kallon.

CAPTAIN SADIQ Where stories live. Discover now