CAPTAIN SADIQ

3K 136 1
                                    

Writte by
         Salma mas'ud nadabo

Editing Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

                          23-24

        Tashi tayi daga jikin inna tana zun6uro baki gaba,  Inna ta ce "Yar nema ba'a isa ayi maki magana bane ko me?
     "Haba ladingo  wai me yasa kike so ki rinka takura wa yarin yan nan ne? cewar Baffa Baba jummai ce tasa baki ta ce, "Ah kuyi hakuri dai, Indai jiki nane ai ta sauka ko? Inna ta murmusa batace komai ba.

           Duk wata tsaraba data kawo haka ta bajewa fatuha kayan zaqi  fatuha ko baki har kunne dan dadi saboda har da bakar alawa, wato (chocolate) haka shima d'an uwan nata da matar sa ta basu nasu tsarabar, sosai sunji dad'i musanman ladingo wanda take ganin baba jummai ta d'auke ta tamkar ciki d'aya suka fito, so da yawa tana fifitata kan jauro d'in ma saboda karamci irin na baba jummai da sani darajar d'an adam, sosai suka ji dadin wannan tsarabar.
                A guje fatuha ta qaraso gidan su fatsima kawo mata nata tsarabar, saboda dama ta mata alqawari duk sanda baba jummai ta zo, to zata kawo mata bakar alawa"(chocolate) .
                  Washe da baki ta qarasa cikin  gidan  nasu  tana  cewa, "Fatsima! Fatsima!
            "ohni fatuha lafiya nagan ki haka? ko yauma tsokana kukayi? inji gwaggon fatsima washe baki tayi ta ce, "Wallahi gwoggo baba jummai ce ta zo yau shine na kawo wa fatsima tsarabar ta"
              "Ayya ki ce min mutan birni sun zo, aiko fatsima na kewaye ki jira ta tafito" bata ida rufe bakin ta ba fatsima ta fito washe da baki Ta ce "Fatuha"
    "na'am..! tare da qarasawa wajan fatu  ta  ce, "ke baba jummai fa ta zo Qur'an"
      "Dan girman Allah? washe baki ta kuma yi ta ce ."Tayi tsarabar baka alawa?
        "Eh Qur'an gama taki nan na kawo maki,"
          "kai amma naji dadi" haka suka shige akurkin dakin fatsima suna ta hira tare da sherance muta ne inna da ke tsakar gida sai cewa ta ke Allah ya shirye su.

                         ****
   A gajiye ya dawo gida  briefcase din shi da ke hannu yaronsa OLA ya amsa cikin sallama ya shigo falon, Mom na zaune a parlou tana kallo angel na kusa da ita tana bacci, A hankali ya qaraso yayi hug din Mom ta baya ya ce  "Wash Mom am tied" juyowa tayi suna facing d'in juna ta amsa masa da cewa "Sorry son ka je part d'inka kayi taking  shower lunch inka  na jiran ka"
      "Ok, face din Jidda ya dan shafa.. sannan ya haura  upstairs.


   
     Yana shiga part na shi bathroom ya wuce yayi wanka ya fito sanye da bathrobe white, A hankali ya  nufi dress mirror ya fara shafa lotion mai kamshi yabi ko ina na jikinsa da shi, kai tsaye Wardrobe d'insa ya nufa ya curo three quarte black sai armless t-shirt ya sa , ba qaramin kyau yayi ba masha Allah.

         Cikin natsuwa ya ke sakowa daga downstairs  ya qaraso  parlour inda ya bar Mom har yanzu nan take, Dining area ya nufa, ya ja kujera ya zauna rabi'a na gefe a hankali ta fara saving na shi tuwan shinkafa miyar egushi wanda taji kaji da yan ciki kamshi sai tayi yake, sai data gama serving nashi  sannan ta mike, harara ya dala mata  dan shi kwata-kwata yan' aikin kona masa rai suke musanman yan'mata wayanda ba abinda suka sa gaba sai halin bera, wani wawan tsoki ya kuma ja wanda yasa rabi'a kyarma, dagowa yayi da sexy eye's ball's din shi ya ce... "Keeee!Tunda kin gama zubamin abincin ai sai ki tafi ko? ko sai kin gama qaremin kallo eeye."

   
     Mom dake parlour sai data ji tsawar da Sadiq ya daka ma rabi'a juyowa tayi ta ce, "Why son? Wai me yasa kai kullun sai an jika da masu aiki ne  baby? gashi nan yanzu garin fad'an ka ka tada angel daga bacci" Bata fuska yayi kamar qaramin yaro ya ce, "Mom ni wallahi bana san yan'aikin nan yawancin su duk barayi ne Mom kuma  qazamai" ya ida zancan yana tsame hannu sa daga cikin plate d'in abincin  tare da dalla wa rabi'a harara y'all ce, "ai saiki zo ki kwashe ragowar abinci ki cinye mara mutunci kawai..! ya qara jan tsoki mtssss..! ya dawo  parlour ya zauna tare da d'aura Jidda a cinyar sa ta  ce, "Daddy please muje shan ice cream"
            "Ok angel bari na d'ako car key sai mu fita" aje Jidda yayi saman three star sannan ya haura sama.

                            *****
             Sai da suka kusan cinye rabi alawar, sannan suka saurara mata sai dai muce Allah ya  tsare kar ayi zawo.
                   Sai yamma likis fatuha  ta waiwayi gida shima d'in ma dan zata canza kaya dan ta je gad'a Washe da baki fatuha ta qaraso gida, Inna da baba jummai sai labari suke saman tabarma ta zo ta wuce su, baba jummai washe da baki ta ce, "Fatuha yan'mata" murmushi tayi tare da shigewa uwar d'aka, baba jummai ce ta qare mata kallo tsab ta ce "Masha Allah fatuha kyakyawa ce sai dai  rashin jita baya bari a gani" tana da d'an tsawo dai-dai gwargwado ita ba gajera ba kuma baza'a kirata doguwa ba, tana da karan hanci kamar biro, bakin ta d'an qararami ne pink, ba laifi tana da hips sai dai yanzu ne ta fara kirgan dangi , wannan kenan, baba jummai ce ta numfasa ta ce..."Ni ko ladingo ina so inzan koma zan tafi da fatuha, dama  hajiya tace na nema mata wanda zata dinga taimakama yar jikarta saboda yarinya ce, shine da na yanke shawara idan jauro ya dawo daga gona sai mu tattauna kan zancan"
         " Ta6 baba jummai bana jin malam zai yarda da batun ki, saboda  baya bari taje ko ina iyakar ta cikin kauyan nan, baba jummai da malam zai yarda da haka nima da zan so hakan, ko dan fatuha ta gyaru tunda nasan birni da kauye ba d'aya bane dole inta je can ta nutsu suma  yan  kauyan  su  huta" nisawa baba jummai tayi ta ce, "Bari jauron ya dawo ni na masa magana"
            "toh Allah yasa ya amince..

  Fatuha ce ta fito washe da baki daga uwar d'aka, tasha jan baki a dole yau itama gad'a zata ta ce "Inna nayi kyau? murmushi inna tayi ita da baba jummai suka hada baki suka ce, "Kinyi kyau fatuha" qara washe baki tayi sannan ta sa kai ta fice.

                         *****
  Riqe da car key ya dawo main parlour tare da d'aukar Jidda ya ce, "Mom zamu fita shan ice cream may be mu biya gidan Anuty bilkisu"
        "OK a dawo lafiya, angel amin tsaraba fa"
            "toh grandma" sannan suka fita.

    Ko da suka fita anwanke masa motarsa CRB black, Kaitsaye wanja motar suka wuce  ola ya bud'e masa murfin motar dana Jidda tare dayi ma Jidda wasa sannan suka sa kai suka fita, sosai yayi yawo da Jidda, daga nan suka wuce gidan Anuty bilki.
                       Cikin jin dadi ta tarbe su inda ta cika Sadiq da kayan fruit Jidda ko sai wasan su suke ita da jamal, da murmushi Anuty bilki ta ce..."Ohni baby yanzu an fara zuminci" tana fadin hakan ne cikin zollaya, harara ya wurga mata ya  ce,  "oh you mean da bana zuminci ko tunda haka kika ce bari na tashi na tafi" hararar wasa ita ma ta masa ta  ce, "tab naga yarda zaka fita daga gidan kuwa" hira suka sha sosai daga nan suka wuce family house.

     Part din ammi ya fara zuwa  tana zaune saman one star tana kallon film din India wanda ko za'a kashe ta bata san me suke cewa ba, washe da baki ta juyo tana cewa "Ah'ah yau mai gidana da kansa? ya  Hauwa'u ita da  Ibrahim d'in?"
         "lafiya lau" ya ce tare da zama
    "Ka ce min da sarkin surutu ka zomin yanzu ta fara min wannan yaran nasu na yahudawa" Murmushi Sadiq yayi ya ce, "Kisha kurimin ki Ammi ai koya maki take"
            "Ah ni ina zan iya wannan gwalangwatsin wannan sai ku" Asiya ta kwallawa kira, cikin sauri ta qaraso  tare da gaishe da sadiq Ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana Ammi ta  ce, "Yauwa yan'nan kawo ma mai gida furar dana dama d'azu tana cikin fridge"
            "toh Ammi" ta mike ta wuce kicin.
    Haka akayi ta kawo masa fura ya sha sosai, saboda shi Sadiq mutun ne mai son fura sai da ya sha ya koshi sannan suka wuce part d'in Umma,

  Suna shiga part d'in da Basma suka ci karo, sanye take da riga da wando riga mai dan gajeran hannu pink mai manya flowers tayi kyau sosai duk da yarinya ce hakan yasa shape din ta fitowa, Kallo d'aya Sadiq ya mata ya watsar Gaishe sa tayi tare da jan hannun Jidda tana mata wasa  sadiq ya ce "Basma ina umma?
       "Umma na bedroom"
"OK ki  ce  mata  na  zo" Sannan ya samu  guri ya zauna.
        Umma  da murmushi ta fito sun dad'e suna hira, Inda tasa talatu ta cika masa tray da kayan motsa baki ,suna cikin hira majid ya dawo suka dasa sabuwar hira.

                        *******
  Sosai suke jin dad'i gadar inda yau sai da su fatuha suka taka, duk da ba wani abu suka iya ba, Sosai sun burge mutane ita da fatsima saboda cikin tsari suke rawar su kamar manyan yan'mata....!


CAPTAIN SADIQ Where stories live. Discover now