Written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Raheenat📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best ★http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-
*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFUROM.COM
93_94
Daukar fatuha akayi chak aka maida ta mota aka ja suka bar harabar gidan Hanan sai matsar kwalla take basu zame ko ina ba sai asibitin da aka kai sadiq, suna shiga lokaci majeed na qoqarin fita kamewa yayi yana bin su da kallo kamar gunki ganin halin da fatu ke ciki duk saboda shi, bin bayan su yayi wasu hawaye masu zafi na masa zarya duk wannan abun da ya faru saboda shine, shiga da fatuha emergency akayi.
Bayan yan mintoci aka fito da fatu har lokacin bata farfado ba tana kwance amma Dr yace da sauki tashin hankali da tunanin ne ya haifar mata da yankewar jiki ta fadi, dakin da aka kwantar da sadiq aka kwantar da fatu kafin anjima jirgin su ya tashi har yanzu kwance yake bai san halin da ake ciki ba
A hankali fatuha ta fara ware idanuta wayanda suka mata nauyi tana bin dakin da kallo, yunqurin tashi tayi ta kasa dakyar ta iya miqewa zaune dafe da kanta dake tsanata sara mata tamkar zai rabe biyu, ta juyo ganin sadiq kwance kefan ta ya dagawa fatu hankali yunkurin sauka daga saman gadon ta je wajan sadiq ta kalli drip din dake hannuta, hannuta tasa ta cire drip din dake hannuta tana kuka da sauri ta matsa kusa da sadiq kuka tasa ganin halin da yake ciki kuka take sosai tamkar ranta zaifi saboda tsanin firgita da halin da sadiq yake ciki a hankali ta fara cewa, "mai kyau meya same ka haka, karka tafi ka barni ka ji idan babu kai babu ni ka ji sadiq d'ina, ina son ka handsome I love you more than how you think please don't leave me alone, na rokeka nima mutuwa zanyi.! Sosai fatu ta rikice dan bata cikin hayacinta duk tabi ta rude sai fama kuka take har sautin kukan ta ya fara fita waje Mom da shigowar su asibitin kenan suka shigo dakin dan duba jikin fatu dana sadiq.
kuka fatuha take tana mai cigaba da cewa, "mai kyau ka tashi wallahi na rasa ka mutuwa zanyi, Allah bana iya zaman aure da majeed please ka tashi, ni kai nake so kai ne farin ciki na ka ji sadiq" ta ida zancan tana kuka mai cin rai Mom ce ta jawo ta, ta rungume tana shafa bayan ta fatu na cewa, "Mom sadiq nake so Allah bana son majeed ku ce masa ya tashi karya tafi ya barni" kuka fatu ta kuma saki ta qanqame Mom "shhhh ya isa kukan haka fatuha, ki kwantar da hankalin ki kin ji indai mai kyau ne ya zama naki..! dagowa tayi tana kallon Mom da mamaki idanuta sunyin jawur lokaci daya kukan da take ya dauke tana jin kalaman Mom kamar ba dai-dai ta ji murmushi Momta sakar mata ta ce, "yes abinda kika ji haka ne, yanzu ba kuka ya kamata kiyi ba kulla da mijin ki ya kamata kiyi idan kun dawo kunji bayani gabaki daya" wani irin farin ciki ne ya lullu6e fatu wanda bata iya boyewa lallausan murmushi fatuha ta saki tana goge hawayanta da bayan hannuta ta qarasa bakin gadon sadiq tana dariya mai had'e da kuka tana cewa, "mai kyau kana jin abin da suke cewa wai da gaske na zama matarka, kayi sauri ka warke ka ji handsome.! majeed dake gefe smile ya mata yana daga mata gira wata irin kunya ce ta lullu6e fatu, sai yanzu ta tuna da su Mom da sauri ta miqe tana qoqarin ta fita daga dakin da gudu saboda tsabar kunya, Basma ce ta tare ta, "ina zaki je kibar mijin naki, ko kin mata kema baki da lafiya kina buqatar kulawa" waki-waki fatu tayi dan tama manta bata jin dadi, harara wasa ta aikawa Basma dan ta bata hanya ta wuce, gabaki daya dakin aka fashe da dariya, sunkunyar da kai fatu tayi.Khaleed dake gefe ne yaja Basma suka wuce gida dan ta samu hutu kafin anjima akaita dakinsa kusan a tare suka fito da majeed yana qoqarin bude mota, motar su ya jawad ta tsaya shida shukara suka fito tare da fatsima sai matsar kwalla take qarasawa majeed yayi tare da cewa, "haka ake sai ku fito min da mata ba tanbayar izini" harara jawad ya aika masa ya ce, "ka raina mutane ai matar taka zaka tanbaya mai yasa ta biyo masoya" ya kai masa duka ya goce yana dariya jawo fatsima yayi jikinsa ya rungume tsam cikin cool voice ya ce, "my wife me ya saki kuka haka kina so ki bata min kwalliyar ki" fatsima da tayi wiki-wiki tana raraba ido neman kwace kanta take dan rashin kunyar yan birni tafi karfinta kamar bai san mai ya kawo su asibitin ba, amma sai wani iskanci yake dan murmushi majeed yayi ya ja karan hancin fatsima washe baki fatsima tayi tare da rufe face nata (lol su fatsima anqaro wulaqanci😜)
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...