1.

484 17 2
                                    

🥎🥎
*A DUNIYAR MU*
🥎🥎
Written by (Msr Bb)

Wannan Littafin na kud'ine ga ta bank 150,idan kuma Katine 200,muna Maraba da masoyan Mu.
Tunda ga page one zuwa page ten free ne.

Name:halliru salisu
Acc:3094299530
Bank: first bank

Idan Karine kuma ga number da zaki turo.
09034722970
Sai kunzo masoya

*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________

_LITTATTAFAN MARUBUCIYAR_
👇🏻
_RAI DA BURI_
_SAFAH DA MARWAH_
_SAINA D'AUKI FANSA_
_RAYUWAR AMEERAH_
_AKWAI BAMBANCI_
AND NOW
_A DUNIYAR MU_

*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI*

Free page
1.

Wata yarinya ce tafito da wani irin mugun gudu daga cikin wani gida, ihu take kurma wa bilhak'k'i da gaskiya tana cewa,
"Taimako!taimako Jama,a! ku taimake mu gidan mu ya kama da wuta, mamina, Abbyna, islam duk suna ciki wayyo Allahna, na shiga uku babu wani,don Allah ku taimake ni, zan rasa su zasu mutu."

Kururuwa kawai take iyakar k'arshen muryar ta,
Amman da ya ke munafukar unguwa ce,ko kare bai lek'oba,d'akin maigadin su ta sake koma wa karo na babu iyaka, tana bubbuga k'ofar da mugun k'arfi tana kwala mashi kira.

"Baba idi ka rufaman asiri kazo ka taimake ni, ta fad'a cikin muryar da harta dishe saboda kuka da kururuwa.
Zubewa tayi bakin k'ofar d'akin tana wani azabebben kuka, yayin da take kallon yadda gidan nasu yake ci da wuta babu k'ak'k'autawa,
Tun ta nayin kukan da sauti har takai da bakajin muryarta.

Sai da gidan ya gama ci ya babbake gaban idonta, Tana gani ta rasa Ahalinta ta rasa iyayenta maso nuna soyayyar su gare su,ta rasa Islam d'inta k'anwarta Abokiyar fad'anta,Abby d'inta Wanda bacci yake rabasu,ko wajen aiki zaije indai tana gida to tare za suje .
Maminta Wacce ta zama kamar k'awarta,suyi fad'a suyi dad'i itada mamin kamar Abokan wasa, kuma hakan baisaka sun raina mahaifiyar ta suba, kullum suna cikin farinciki da Annashuwa idan Abu ya samu d'aya su duka ya sama,haka idan wani na cikin halin damuwa babu Mai iya Kai lomar abinci cikin bakin shi.
Wasu zafafan hawaye suka shiga ziraro mata daidai lokacin da take jin jiniyar motar y'an kwana kwana,wani kullutu ne yazo yato kare Mata mak'oshi,
Sai yanzu zasu zo,tun da wutar takama takirasu kusan awa biyu kenan sai yanzu za suzo,
Wannan na d'aya daga cikin matsalolin dasuka addabi *duniyar mu*
sadda motar tashigo, gidan,hayak'i kawai ya keyi,don wutar taci iya cinta sai y'ar wacce keci k'asa k'asa.

Wani irin fitinennen zafi Takeji acikin zuciyarta da k'irjinta,
tun ta nayin kukan fili har ya koma na zuci,tana gani Ana fiddo gawarwakin iyayen nata,
Ta islam ce kawai ba,a ganiba wanda hakan ya nuna ta k'one Tass don ko tokarta baza,aiya ganiba.
Zuciyarta tabushe idonta ya yi wani irin fitinen nen jaaa,
Tun k'arfe d'aya na dare wutar ta kama,tun daga lokacin har k'arfe shidda na safe tana zaune inda take,tana kallon gawarwakin iyayen nata.
Tunda A bun yafaru bata ga kowa nasu bah sai yanzu,kuma babu nisa tsakanin su da gidan k'an nen Abby d'inta,don ihun da tayi ya isa ace har na bayan gidan sunji bawai suba ma,
Amman shine sai yanzu za suzo to me za suyi masu, meyayi saura kuma,komi ya k'are suntafi mami ta tafi Abby ya tafi,Islam ta tafi shin meyayi Mata saura, meyasa nima ban zauna mun k'one tare bah.......kuka take tuk'uru amman na zuci.
Tana kallon sadda dady kabir ya shigo cikin nuna tashin hankalinsa Amman na bogi,zuwa can saiga dady Musa shima d'in kamar dady kabir ya shigo,yama fishi iya pretending d'in...... Kan wani lokaci gidan ya cika tab da mutanen unguwa dakuma abokan kasuwancin Abby,manyan mutane masu mulki da kud'i matan su dady da yaransu sai shigowa suke suna garzar kuka.

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now