*A DUNIYARMU*
written by Mrs bb.29.
Tare muka fito zuwa falon da zulaiha suke da Asim, kararta da karad'inta shi ya sani idasawa aguje, turus nayi gaba ganin yadda ta yiwa asim wata irin runguma, kunya ce ta kamani ga Aj tsaye baya na, narasa inda zansa kaina don kunya, kamar in nitse haka nakeji...........jinai yace mashi,
"Dallah malam saketa haka nan, tunda ba cewa akai andaura auren ba."
Sai lokacin suka saki juna sai murmushi suke, ina tsaye duk ji nake kamar na zura aguje.
"Duba duk yadda kuka bata kunya, bakuyin hakuri adaura haba, zakewarku tayi yawa."
Nidai fita nayi ban yiwa asim din magana ba, saboda wata irin kunyarsa da nakeji, itama sai yanzu taji kunyar kasa tsayawa tayi ta rugo tabiyo bayana.
Karshe bamusan tafiyarsu ba.
Daki muka zube ta kamani ta k'adaddabe, sai murna take tama kasa natsuwa ta sanar dani meke faruwa, saida na k'waci jikina sannan nace,
"Wai lafiyarki k'alau ki gaya mani mana nima muyi murnar tare."
Harda k'wallanta tace,
"Hanan tun bayan dana baro gida babu abunda ya faranta raina irin haka, Asim ya sanar dani dadynsu yace yadawo gida, yayafe masa kuma yashirya yi mashi auren."Ai ni nama fita murnan rawa na tashi ina takawa, kafin narungumeta ina cewa.
"Na taya Ku murna zuly wallahi kinganni nan nikaina jinake babu kamar yau din, saboda albishir din Abokinku cewa zai maidani makaranta, wannan rana ta zo da alkairi Allah ya sake nuna mana wadda tafita."
Tace,
"Ameen hanan."Kallonta nayi cikin tausaya wa nace,
"Zuly ya batun babanki kenan, kina nufin zakiyi aure ba tare da yardar shiba, karki manta cewa Asim ya fad'amaki cewar bazai tab'a aure ba tare da yardar dadynsa ba, kenan ke kina nufin baki sasanta da naki iyayenba zaki yi auren, kina son albarkar Aure kuwa kina son farincikin ki ya dore har iyakar k'arshen rayuwarki kuwa."
Kallona take idanunta hawaye kawai suke fitarwa tace.
"Ya zanyi Hanan, Wallahi bazan iya gujewa wannan auren ba, inason Asim bazan boye maki ba, kullim kwanan duniya sha,awata kara karuwa take kina son na jefa kaina ga halaka, Hanan idan na biye ta baba wallahi bazai tab'a amuncewa ba, kibarni kawai nayi farin ciki na tare da Asim."
"Uhmm lallai na yarda soyayya takan canza komi kuma ta canza kowa,nayi mamakin jin haka daga bakinki zuly, wai shin kin manta girma da darajar iyaye, wallahi kinji na rantse maki muddin kikai wannan auren ba tare da yardar mahaifanki ba keda farinciki har abada, ba fata nake maki ba ina nusar dake kuskuren da kike kokarin yine, sannan wallahi koshi Asim din sai yaringa maki wani gani gani, don zai kalleki matsayin wadda bata dauki iyaye matsayin komi ba, zulaiha bazan so abunda zai cutar dake ba, ni mai kaunarki ce gaskiya nake fad'a maki, kishirya ki koma ga iyayenki kinemi yafiyarsu kikuma rokesu akan subarki ki auri Wanda kike so, muddin ba haka ba to bazance ga abunda zai faru nan gaba ba, saidai nace Allah ya kyauta."
Kuka na barta tana yi nasan maganata tayi mata zafi, Amman bazan iya barin zulaiha ta yi wannan auren ba tare da yardar iyayenta ba, don kowa yayi aure farinciki mai dorewa yake nema da saka albarkarsu, ina mata sha,awar koma wa gaban iyayenta Don inhar akai bikinta gidansu sai tafi mutunci da kima ga idon iyayen mijin dashi kanshi mijin.
************
"To ya kuka k'are da mutuniyar taka."
Murmushi yayi yace,
"Lafiya munyi magana ta fahimta, imfact ma mun shirya mun dawo yaya da k'anwa."Dariya Asim yayi yana cigaba da tukinsa yace.
"Aj ina ganin ba daidai bane don iyayena sun amunce da aurenmu nida zulaiha ita nata basu yarda ba kuma muyi, ina ganin zaka rakani mufara musu abun asiyasance.........siyayya zamuyi ta gani ta fad'a na kai gidan matsayin itace tayi, sannan muduba duk wasu bukatu nasu mu dauke masu,karmu yarda sugane ba itace keyi ba, wannan hanyarce kawai zata saka koda zulaiha ta koma gida su tarbeta cikin mutunci, karshe hakan zai sauko da fushin mahaifinta akanta, tunda Wanda ya dauka da darajar yacuceshi kuma ya gudu.""Amman badai kuyi maganar da ita ba ko."
"Aa bamuyi ba na auna hankalinta ne, inga zata iyayin Auren babu yardarsu."
Murmushi Aj yayi yace,
"Dadina dakai abokina kana da wayau da hankali, hakan ma daidai ne Allah yasa mudace.""Yace ameen Aboki."
***********
Harun ne ke kulawa da dadyn nashi don yana kwance Asibiti baya lafiya, kusan sati kenan hawan jini ya ta soshi gaba ga ciwon suger, hajiya ma,u tayi tafiyarta garinsu itada ilham, atu ce kurun gidan da yaronta.daga ita sai harun ke kulawa da Dadyn.
Duk Wanda ya ganshi sai ya tausaya mashi, ya rame yayi baki idan kaganshi ba zaka tab'a cewa shine ba, don harun kuka yake wata sa,in idan ya ganshi cikin wannan halin.
Gefe guda zaman shida hibba gwanin sha,awa tun yana kwatsarta har yazo ya bada kai buri yahau, kulawa take dashi yadda ya kamata, haka zata yo girkin abincin masu suger ta kawo nan asibitin, don wani zubin harun ita yake bari yatai wajen aiki, idan atu tazo suyi jinyar tare.
Hibba zuwa yanzu kullum cikin nadamar abunda tayi wa qawarta take, don har idan tayi sallah tana rokon Allah ya yafe mata, ya kuma jikan Hanan.
Tayi nadamar halin mahaifinta don zuwa yanzu ta fahimci komi, zagon k'asa sukai ma baban hanan bacin duk irin Abun alkairin yayi masu,tayi alkawarin cigaba dayiwa hanan addua har karshen rayuwarta, sanan ba zata sake kwatanta abunda tayi ma hanan din ga kowa ba.
Yau jikin da sauki sosai don har yana iya tashi zaune da kanshi.
Harun ne tare dashi ya gama bashi abinci, yana mashi shirin kwamciya kallon shi yayi yace,
"Harun Allah yayi maka albarka, ya baka zuria ta gari suyi maka irin abun alkairin da kakemun."Murmushi yayi yace,
"Ameen Dady Allah dai ya baka lafiya.""Ameen to, yau nake son sanar dakai sirrin da nake boyewa shekara da shekaru, zan bayyana maka ainahin waye mahaifinka da mahaifin Hanan, da dadynku musa da uban matar ka hibbah...............
Mom muhsen ce
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...