page 12

73 3 0
                                    

*A DUNIYARMU*
   Writting by (Mrs bb)

12.

Ina taya ta hura wutar tana tsanana ina yak'e,don banson nuna mata halin da nake ciki saboda kar hankalinsa ya tashi.
Duhun dare ya fara don duk mutanen wajen sunfito sun hura wuta kasancewar sanyi akeyi mai tsananin shiga jiki, gashi cikin dajine dole sanyin wajen ya linka na ko Ina.
Sallah na je nayi na dawo na ansheta Itama tatafi tayi,
Lokacin babani ya dawo daga kiwonsa har ya kaso wani tsuntsun ni dai bazan ce ga sunan sa ba,zama mukai inda ake taruwa idan dare yayi ayi fira,wuta ake harawa mai yawa duk zamu zagaye ta azauna ayita hira ana cin abinci,anan nasha furata inajin fad'uwar gabana tana yawaita ina dai yin k'ok'arin dannewa saboda karsu fahimci halin da nake ciki......... Dare yayi dare don har tsuntsaye Sunyi tsit........lokacin kuwa yayi bacci Amman ni na kasa yin nawa saboda tashin hankalin da nakeji zuciyata na k'ara shiga.

Bazan iya gane ko k'arfe nawa ne na dare bah, Amman dare ya raba sosai can k'asa k'asa na fara jiyo karar jirgi..........afirgice na tashi daga shimfid'ar da nake kirjina yana d'agawa saboda tsananin tension,ahankali sautin jirgin yake sake tunkaro jejin dandanan jikina yafara rawa banajin Motsin kowa alamun baccinsu suke basuji abunda na keji bah......... Saida karar ta fito fili ta karad'e jejin sannan duk kowa yafito cike da tashin hankali......tuni wasu sunfara kuka suna neman wajen zuwa.

Jikina karkarwa yake Ina mamuk'e da jikkata samb'arutu ta rik'eni cikin jikinta, duk da tashin hankalin da take ciki Itama hakan bai sa ta mance dani bah,babani ma wajenmu ya iso yana rawar jiki yace Mani,
"ki kwantar da hankalinki kinji ummu,babu abunda  suka isa suyi mana face da yardar ubangiji indai ina nan bazan bari acutar da rayuwar kiba, sai inda k'arfi na ya k'are."

Maganarsa ta karya Mani zuciya saboda ganin babani ko kare kansa baya iyawa taya zai iya kare waninsa,wasu zazzafan hawaye suka ringa silalowa ga fuskata nace masa,
"Aa Babah baza ai haka ba, kuzo muruga zama bai ganmu bah, mu yanka ko Ta ina ne Allah zai karemu........... Kuka na kucceman don har Cikin k'ok'on raina bana son wani Abu yasa mesu.
Sambarutu tace cikin rawar murya tana sake matseni jikinta tace,
"ummu bakisan had'arin dake cikin jejin nan ba Idan dare yayi, akwai halittar da mutane sune abincinta,ko yaya taji k'amshi mutun acikinsa sunan ka cinyayye saidai wani ba kaiba."

Magana zanyi amman dirar jirgin ya sakani shiru tuni wasu sun fara nau sawa cikin wannan dajin,sun gwammace wannan halittar tacinye su da su tsaya ganin zubar da jinin y'an uwansu,
Jirgin ba d'aya bane helicopter hudu ne guda uku kedauke da mutane...... D'ayan kuma kayan aikinsu ne da wasu irin bindigu masu tsananin firgitarwa......ban idasa tunani naba naji sunfara sakin wuta duk wad'annan bukkokin sun saka masu wuta, kwatanta tashin hankalin da muka gani Abune da bazai fad'uba zulaiha,gabana akarinka kashe mutanen jejin nan kamar kiyashi,tun ina kuka da sauti har takai muryar ta d'auke......... Wani da tunda sukazo aka ajiye masa kujera ya kafe bai motsaba, inajin ogansu Ne umurni Ya bada akawo masa ni........kasancewar duhun dareni bazai iya ganin fuskata ba Amman ni zan iya ganin tashi ba,jana ake kamar wani kayan wanki kafin mu isa inda yake jikina ya kakkarce jini kawai yake fitarwa.......... Hawaye na sharce ina d'an shashshekar kuka k'asa k'asa.
Ganin halin da nake ciki yasaka babani rugawa Ya rungume ni yana kuka yana rokonsu yana cewa,
"na rok'eku karku cutar da ita, amanace garemu na had'aku da mahaliccinmu ku rabu da ita ni kuyi mani komi Amman ku barta karku cuceta....... Ya karashe yana kuka wanda jinake kamar zan fashe saboda tsananin zafin da nakeji zuciyata..........wani harbi wani narkeken k'ato ya kai mashi ga cikinsa.........wanda saida yayi aman jini saboda Bala,i wani kukan kura nayi na isa wajensa Ina ihun ceton rai,kiransa nake Ina karawa jijkigashi nake Amman ga duk kan alamu babani ya rasu....... Sambarutu Itama duk tare muke wannan tashin hankalin,ba mufita wannan ba nasake shiga wani,jana akaringayi har gaban Wanan Mutumin dake man kama da wasu......... Zulaiha gaban idona suka zuba masu fetor da sauran mutanen wajen jejin suka kunna masu wuta.............

_kuka ya kucceman yinake inajin ciwon har k'asan raina jinake Inama ni suka kona basu bah zulaiha,har gobe har jibi ke har abadan abada bazan iya manta alkairin wad'annan bayin Allah ba kuma insha Allah har na koma ga mahaliccina bakina bazai gajiya da yi masu addua ba._

D'aureni ogansu yasaka akayi,kamar huhungoro Motsin kirki bana yawa zulaiha ahaka suka fara hidimar gino gold dinsu duk jikina yasaki gaba d'aya................saida na suma Na farka yakai sau shurin musaki saida aikinsu yayi nisa wani daga cikinsu yajuyo kaina murya k'asa k'asa baisan ajishi yace,
"zan tai makeki Amman sai kin bani had'in Kai wajen Abunda na keso,idan kin Amunce to zan tseratar dake daga wannan wajen."
Duk da halin da nake ciki Nayi dauriya nace masa me yake buk'ata gareni.

Cikin waige da tsoro yace Mani,
"sunana Ismael wancan da kikagani shugaban mune anan Amman bashine babban ba, babansa da mak'arrabansa sune masu wannan aikin, d'angidan Alhaji kallah ne nasan kin sanshi tunda naganki nagane ki, yar wajen marigayi Abdullahi ce ko."

Dandanan na idasa wartsakewa nad'aga Kai saboda bana iya magana inacikin matsanan cuyar wuya,
Cigaba yayi da cewa"ina d'aya daga cikin yaran babansa na kusa nasan komi akansu, akwai abunda ya faru nina jawo matsalar wanda tasaka aka rufe masa masa,na antar sa ta dalilin hakan ya kashe mani yayana, Wanda ya d'auka bansani bah nikuma ban tab'a nuna masa cewar Na saniba saboda ina son d'aukar fansa,zan kunce ki na nuna maki hanya mafi sauk'i kibi har Allah ya sadaki da garin zamfara,kwance ni yaringayi cikin sauri yana cewa akwai wasu evidence yanzu haka wajena zan baki duk sadda Allah yasaka kika samu natsuwa ki nemeni akwai komi aciki wanda zaki samu ganina............ Muje cikin sand'a da dubara muka fara b'acewa ganinsu gudu muke cikin jejin yana jana har Allah ya nuna mana wata hanya mik'ak'ka yace,
"ki kula akwai b'arayi akwai dai risk hanyar kiyita addua Allah ya sadaki da mutanen Kwarai."
Ina hawaye nace daker"nagode kaima ka kula karsu gano kaine ka ceceni Ngd Allah yabamu nasara."
D'aga mani hannu yake yajuya Aguje don koda sun ganshi yasan yadda zai yakare kansa.........

Maman Muhsin ce✍🏻

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now