*A DUNIYARMU*
Written by mrs bb.31.
Shigowar Alhaji kallah itace ta sake b'ata duk wani sauran son yaya dake cikin zuciyata.
Yazo da buk'atar son mallake sabuwar super markert din da yake ginawa,wadda duk cikin garin kano babu kamarta,dalilin dayasa kuwa Alhaji kallah yin haka shine,wajen aikinsu guda da yaya don ya riga yaya fara aiki wajen,zuwan yaya shi ya dakushe ma Alhaji kallah duk wani farinjini da wasu tsarikan,idan wani aikin k'aruwane za,a yi yayane za,asaka saboda gaskiyarsa da rikon amanarsa........ahankali Kowa ya gane Alhaji kallah mahandamine,kuma k'asurgumin b'arwo ne a company din.
Zuwan yaya komi yazo yafara daidaita,karshe kujerar Alhaji kallah aka anshe akaba yaya,mafarin yafara samun wasu mahaukatan k'udi wanda ya zama anan garin yaya yana cikin jerin masu kudin da akeji dasu ake kuma alfahari dasu,wannan dalilin yasa Alhaji kallah ya b'arka masu wata sata har suka korai,yazo yashiga kangin talauci abubuwa sunyi mashi tsaye,komi ya dagule mashi,dole ya yanke shawarar komawa wajen yaya,Allah sarki yaya da zuciya guda ya tareshi bayan yaji kukanshi yaji tausayinsa,nan yayi mashi goma shatara ta arxiki tare dayi mashi Alkawarin maidashi wajen aikinshi..........don dadi kuwa Alhaji kallah yaji dadi Amman dayake zuciya mugun nama ce,sai tabashi shawarar yadda zaiyi yaga bayan yaya,tare da duk abunda ya mallaka............mafarin yaje yayi bincike akanmu yaje sukai magana da musa sannan suka sameni............Tabbas da acikin hayyacina nake bazan tab'a biyewa muguwar Aniyarsu ba,saboda lokacin ashe musa asiri yayi mani,Naji duk duniya babu wanda nake k'i naji natsane shi sai yaya,sanda sukazo da bukatar ganin bayanshi shida iyalinsa banyi musuba saboda bana iyayin musu da duk abunda suka sani........nayi kuka nayi bak'in ciki harun, kasancewar dani aka shirya yadda za,a kashe d'an uwana najini wanda banda kamarshi fad'in duniya......inaji ina gani Alhaji kallah sukayo hayar yan iska suka kona gidan yaya,duk da asirin dake jikina hakan bai hanani jin ban kyauta ba, wallahi harun inajin banda wani sauran anfani aduniya,nayi silar barin dan uwana duniya na salwantar da rayuwar ahalinshi,kuka ne ya kucce mashi mai tab'a zuciyar duk mai sauraro,harun banson wannan rayuwar sonake inmutu, taya zan cigaba da rayuwa cikin wannan bak'in cikin,natsani kaina jinake kamar nasoka ma kaina wuk'a..............yaci gaba da kukan.Harun yasadda kai ya na jin zuciyarsa kamar zata keta kirjinsa ta fito,wani irin numfashi yake shak'a yana fesarwa,jijiyoyin kanshi suntashi sunyi rad'o rad'o,sun d'auki almost thirty minutes ahaka kafin harun ya d'ago yana kallon yadda mahaifinshi yake kuka,cikin wata kalar murya data canza amo yace.
"Daddy ina hanan take."
Wani kukan ya kucce mashi wanda yafi na farko,bai hana shi ba kuma bai lallasheshi ba,don wannan masifar duk shine yayi dalilinta,da tun sadda musa yake zuwar mashi da maganar da yayi mashi kyakyawan warning da duk haka bata faruba,saida yaji ya gaji don kanshi sannan yace,
"Harun Hanan ta mutu"
Nan ya shiga gaya mashi duk irin abunda sukai har kawo kashe Alhaji Nasir makama shida hanan.........tunda yake bashi labarin babu abu mafi firgitarwa da tashin hankali irin wannan daya ke sanar dashi yanzu,idonshi ya zaro gaba d'ayansu yana kallon mahaifinshi.......jikinsa rawa yake kamar mazari bakinsa kar karwa yake yace.........."Daddy kun kashe hanan hazbunallahu wani imal wakil Daddy me tayi maku,me marainiyar Allah ta tsare maku,wallahi wannan jarabtar da kake fuskanta alhakin tane,tun anan duniya kafara ganin saka makonka,shin Dady mekuke nema wanda Allah baibakuba har kuke harin na wani,har kukayi dalilin barinsu duniya basuji ba basu ganiba.....innalillahi wa inna ilaihir raju,un wayyo Allahna,Hanan sun rabni dake,sunyi dalilin rushewar rayuwar da muke mafarkin yi........kuka rurus harun keyi shima Daddy yana taya shi wanda duk abunda ke faruwa tun daga farko har k'arshe Hibba naji,taji komi itama kukan take nan bakin k'ofar........anrasa mai lallashin d'aya saida likita yazo sanann harun sukai shiru allurar bacci akawa dadyn dandanan bacci ya sureshi yana ajiyar zuciya.
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...