*A DUNIYARMU*
WRITTEN BY MRS BB.33.
Jikin baba yana ta sauk'i masha Allah,don zogin da take mashi ta rage saboda daman idan tana d'urar ruwane yakejin kamar ya tuge k'afar...........gobe ake shiga aikin dashi.....sau biyu ABDUL JAB yana zuwa dubashi....yau dai tun safe da yafita bai isa office ba saida ya biya wajensu,yake sanar dasu insha Allah gobe kafin ashiga aikin zasuzo da zulaiha........farinciki ya kama su Albarka kawai suje zunduma mashi office d'insa ya wuce don yana da bak'o tun kusan kwana uku yake zuwa baya samunshi.
Wayarsa ya ciro ya yiwa Hanan text cewar sufara had'a kaya yau zasu iso da dare da safe sujuyo,idan yace kiranta zai ba makawa office d'in baizai idasa shigaba,don zata shagaltar dashi.......murmushi yayi yanajin new feelings ba zai iya tantance na meyeba illa iyaka dai yasan idan yana sauraren muryarta to tabbas komi yake ci ko yake sha bayajin d'an d'anonsa sai muryarta kawai,murmushi mai kyau yakeyi har ya ida shiga cikin compound din wajen,gaisashi kawai ake har yasamu isa had'ad'd'en office d'insa kamar hotel,messenger sa ne ya iso cikin sauri ya anshi jikkar hannunsa yana gaidashi.
"Yallabai mutumen nan yanzu yabar nan,tun seven thirty yake nan gashi har kwata to nine,yace zaije wajen aikinshi zuwa 4:00 pm zai dawo."Zama Aj yayi kan kujerarsa yana kunna ac da remote yace"four nabar ofis zanbar garin sai gobe zan dawo,kabashi no dina sai yakirani."
"OK sir"
Aiki yake yana shan coffee yana murmushi........
(Nikau nace wannan smile haka AJ kamar anbaka kyautar Hanan🤭)***********
"Wannan ai tashi na kama ka ne,haba don Allah ai kamata yayi ace tun shekaran jiya anfad'a ma mutun yayi shirinsa a tsanake."
Zulaiha na gefe tana danna waya dariyarta kurun take dannewa,don tasan muddin ta fito fad'a zasuyi,don yanzu abu kad'an yake hasala Hanan din.
"Kina jina ina b'ab'atu kin mun banza wallahi sai nace ma babu inda zanje,haba dan Allah."
Dariyar ta kucce mata tafara k'yalk'yalata harda rik'e ciki.........ajiye doguwar rigar nayi dana d'auko zan linke,kallonta nake cike da haushi ganin abun nata bana k'arewa bane na nufota a fusace kamar kububuwa,aguje ta fito tana haki binta nayi ina cewa wallahi yau mai rabani dake ko Asim albarka........gudu muke mune har cikin compound din gidan,inda muke parking motoci........."in bacin baki tausayina tun safe nake abu guda baki ji kaina kin tayani ba,sai ki tusani gaba kina man dariya........Allah kika shigo hannuna yau kin bani......gudu muke kuma dariyar take mun.....gashi lokacin har anfara kiran magruba bakwai tayi.........rigada wando ne jikina masu taushin gaske,sunbi jikina sun lafe....wandon lemon green top din fara k'ar......... Kaina da farin siririn gyale......wanda sulb'in gashina yasaka shi saukowa kan kafad'ata......nagaji over don ba k'aramin gudu mukai ba,sanda zamu zagayo me zan gani motace fake sukuma suna saman motar suna hira,hasken dake wajen ya haskesu kamar wasu yaran turawa kowa yasha kananan kaya,fesin caf ce kan Aj ba ka gano idonsa.........Zulaiha idasa wa tayi wajensu tana shashsheka.......wanda ni kuwa kunya da haushin bazatar su ta rufeni,ga karin haushin sun sameni zigidir........kwana nayi nashige cikin gida nabarsu nan.
"Amman kun ma memu wlh tun yaushe kuke nan."
Dirowa Asim yayi yana binta da kallon kauna,jiyake yadda yaganta hakanan kamar ya had'iyeta d'anya.........amman babu halin hakan,murmushi Mai tattare da tsantsagoran kauna da bege yake aikamata yace"just ten minutes ago,
Gudun me kuke haka"Murmushi tayi ta kalli AJ dake ta kallonsu kamar ya samu tv hada yin tagumi,dariya sukai mashi tace"yah Aj kana lfy kuwa."
Shima dirowar yayi yace"naga kamar zaku had'iye juna ne."
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...