*A DUNIYARMU*
Written by mrs bb
Mom muhsen.47
*remain 3 page insha Allah*😊Riga da siket ne nasaka na less pink da purple zanen fulawowin manya masu tsananin kyau da daukar ido,shirin nake ina murmushi mai kyau akan fuskata,haka nakejina yau tana mun dadi,tun daya furtan kalam nan har yanzu basu bar sukar zuciyata da dodon kunnena ba.........gyale nasa purple da takalma suma purple da jikkarsu,feshin turare nakeyi saida naji yayi man zam zam sannan na ajiye na dauki jikar da wayata na nufi falon..........Amnah mukai karo da ita wajen wucewa tsayawa tai tana kallona rike da baki,
"Aaaaaaah Antynah!kece haka tunda kikazo gidannan bakiyi gayun da ya burgeni irin wannan bah."
Murmushi nake ina kallonta nace"banda zolaya qanwata."
"Wallahi Anti bawasa kinganki wai wannan ai idan yah yagani susucewa zai.......duka na kai mata tana cewa daman shine yace na maki magana yana jiranki,gama anty fati can tazo tace tunda ke baki taba zuwaba ita taxo."
Murmushi nai muka nufi falon tare da ita........duk suna zaune hajiya da fatin da hajjo bilal ne yashigo yanzu Aj yana kasa wajen kafafun hajiyar.Anty fatin tafara magana tana rike baki,
"Aaaaa hajiya haka yar taki take da kyau,irin wannan gayu na daukar hankali ai saiki ruda yan maza."
Gaba daya suka saka dariya gefenta na zauna ina cewa,
"Sorry kinjini ban zoba wlh banda natsuwa kwana biyu shiyasa amman kiyi hkr idan na fara zarya gidanki sai kince ya isa haka."
Tayi dariya "haba dai yarinya,Abdul zai barki kiyita zarya ahanya wanna ruwan kyan duk yan samari su gama ganeshi."
Shiru nai ina satar kallon inda yake,murmushi yake mai kyau yace"ina zata ganki balle tayi maki zaryar,ganin mu wuya zai maki sai kin ringa hadawa da kamun kafa tukunnah."
Mikewa yai yana ficewa hira ta barke sosai nan nakeji hajiya na gaya masu,ai UK zamuje idan mun daidaita dashi kawai aure za,a daura muwuce don zancigaba da karatu.
Kunyar danaji yasa nai saurin ficewa suna man dariya,
Yana zaune yana jirana na bude gaban na zauna,
"Bazaki jamu ba.,i like 2 see u idan kina draving."
Murmushi kurun nayi nace"And me."
Tada motar yayi yana fita gidan sannan yace"and u what."
Kauda kai nai nace"nima inason inga kana driving yama fi maka kyau fiye dani,"
Smile yake wanda ban tab'a ganinsa ga fuskar saba yace"thank u."
Shiru mukai muna cigaba da tafiyar iska mai dadi yana kadawa,ga kamshin perfume dinsa ya cika motar,duk yadda nasaka turare in dai nazo inda yake nawa disashewa yake......."how was yesterday."
Natsinci muryarsa yana fadar haka,yatsina fuska nai nace"fine""Bakice mun komi ba,ni ko ma miye kifurta man i need to hear something for u"
"Nifa nace maka bakai kama da wanda zan iya aura ba,kurun ka hkr ga hajjo can itama ai tana sonka to donme zaka matsaman."
"U mean u are jealous for her."
Zaro ido nai nace"Allah yakyau man,miye abun wani jealous tare da ita."
Dariya yayi yace"inhar kin tabbatar haka kike nufi cikin ranki ni kuma i will insha Allah."
Wata irin duka kirjina yayi idona ya ciko da kwallah nace"aidaman ba sona kake ba hakan kazo kacikani da kalaman yaudara,ni banson irin haka kaje kaita auren nata sai me sai akace maka Hanan ma bazata samu mai sonta ba."
Dariyarsa ya shanye yaki cewa komi hankalina ya sake tashi ba kamar jin danai ta kirasa awaya.Sai yasaka handsfree tace"uncle plsss kayo man tsaraba ice cream dinan mai dadi."
Ya na murmushi yace"bakida matsala my dear,sai kuma me."
Ta sake shagwabewa tace"and kuma kadawi da wuri zaka kaini gidan party n kawata."
"Angama baby bakida matsala."
Jinai kamar nayi tsuntsuwa nabar cikin motar,xuciyata daci take man duk wani farin ciki ya kau kan fuskata........shima ya danne feelings dinsa bai sake ce man komiba
Har muka isa gidan dady saidai hankali na yayi matukar tashi yadda nasamu gidan,ya lalace lalacewa ta tatashin hankali......nan take naji idanuna sun ciko da kwallah......na tuna wannan gidan duk unguwar in banda gidanmu nashine na biyu waje. Haduwa,amma gashinan kamar ana gurgurarsa ana cinsa,bansan sadda na durkushe ina kuka ba......har jikina yana rawa.
Kamo ni yayi yana lallashi aman banma jinsa saboda wani ciwo daya taso man cikin zuciyata,sosai nake kukana har muka shiga gidan..........komi babu cikin falon nan wanda da yake cike da kayan alatu,amman gashinan tayils dinma duk sun ciccire bango duk ya gurgure,daker na isa falon dadyn atuce keta faman goge aman da yayi.......dukrkushewa nai ina kuka sosai,kallona atun keyi tana tambayata lafiya meyafaru Hanan.Jin an kira sunana yasashi bude ido cikin sauri,
Yace cikin disashiyar muryar marasa lafy"rabi wakikace kamar naji kin anbato Hanan ko."Tace"eh dady itace gata nan tana kuka vansan me yafaruba."
"Tadani Rabi inganta tadani yau zanga jinin yayana,bayan tsawon wasu shekaru bazanso inbar duniy ban nemi yafiyarta ba,tadashi tayi yana neman glass dinsa don ko gani baiyi yazun saboda ciwon suger dayayi mashi katutu.Isa nai gareshi ina kuka na rungumeshi sosai muka hau kukan tare,
Ita kanta atun kuka take,duk ta lalace baka tab'a cewa itace yar gayunnan..........daker muka lallashi kanmu mukai shiru yariko hannuna duka yace,"Hanan kinga yadda Allah yyi dani ko,kinga alhakin ki dana yayana kinga yadda na koma saboda hakkin marainiya ko,hakika cin dukiyar maraya gubane tashin hankaline,nayi nadama nayi dana sani arayuwata,awannan halin jinake gara na mutu ko wannan yar yarinyar ta huta da jagainiya ta itada harun,.
Har yau ma,u da ilham banajin duriyarsu.........su biyun nan dai da matar harun hibba suke hidima dani,sai wannan yaron Abduljabbar na wajn barrister yaron kirki,shike biyan duk wasu kudi da ake bukata asibiti,yayi man hallaci domin Harun nauyi yyi mashi yawa,aikinma yanzu albashin ba wani bane hanan ki yafe man kijikaina ki yafewa kanen babanki,nayi kuskure arayuwata wanda bazan taba daina kuka da kaina ba,inajin kunyarki inajin nauyinki hanan domin babu abunda yaya baimana ba,amman muka kasa rikeki kedaa tal.
Kullum da wannan abun nake kwana nake tashi,ko a haka Allah yabarni wallahi na jarabtu........rufe masa baki nai ina hawaye nace"dady mai aukuwa ta auku,babu sauran kuma wani abu kaddara tarigayi fata illah iyaka kawai mutari gaba,na yafe maka duniya da lahira ka cire damuwar komi Allah shikeda rayuwa idan kwanan basu kareba bazaka taba mutuwa ba,sannan kadage da rokon ruba wajen Allah don gafurur raheem ne......."
Rungumeni ya sake yi yaa share hawayensa,
"Nagode diyata Allah yayi maki albarka,kiyi man wata alfarma guda don Allah Hanan.""Inajinka dady indai bai saba dokaba zanmaka."
"Sonake na aurar dake domin nafi shekara ina mafarki da yaya yana rokona idan Allah hasadamu dake na aurar dake ga wannan yaron na gidan barrister Abduljabbar."
"Yaron yacancanci komi kuma yana sonki ya gaya man,yace amman baison atirsasaki yafison ki amunce da kanki."
Sadda kaina nayi nace dady ni da sosamu nane kdan har yah harun zai iya auren mata biyu ni shi nai niyyar aure,saboda kafin nabar gida mun alkawarin haka dashi."
Jinai kurin murya na cewa,
"Kiyi hkr hanan,Aj yafini bukatarki ni na yafe mashi shine yafi cancanta dake inhar hargobe kina kallona matsayin yayanki to nima Aj na baki matsayin wanda zaki aura."Shiru nai ina jinjina maganarsu,Allah yasani har gobe ina son yah harun saidai son Aj yadanne wanda nake mashi, kuma ahalin yanzu da zai amunce wallahi nikuma shi zan aura,saboda yadda ya nuna man kauna lokacin da kowa yake kina.
"Shikenan yah harun na amunce da hakan,duk yadda kukai yayi man."
Murmushi yayi man yace"good kinyi daidai,Dady inajin bai kamata adauki lokaci ba kurun idan akai magana da magabatansa sai kurun adaura hakan zaifi."Dadyn yace"saboda farin cikin danake ciki naji duk na samu saukin jikina harun,don haka kayi magana dashi wanna sati magabatansa suzo sati na sama kawai sai adaura hankalina zaifi kwanciya nima shima kuma yaya nashi zai kwanta."
Wasa wasa hira tatashi tsakaninmu har muna dariya Ashe atu yaronta k'yanda ta kashesa,nayi mata jaje har tana kuka.
Ban baro gidanba saida naje gidan yah harun.Danaje hibba boyewa tayi aikuwa na bita har dakin na jawota saita fashe da kuka tana ban hkr dariya naitayi mata inacewa kefa antynace kibar kukan komi yawuce,haka Allah ketsara abunsa baka isa ka canza ba kedai kikara kiyayewa Allah yayafe mana gaba daya.
Har muka dawo fushi nake dashi duk ya susuce sai rawar kafa yakeman,.
Nai burus dashi na kira zulaiha na bata labarin halin da ake ciki taita murna tana cewa ashe dai sai mun rigasu shigewa daga ciki.....naita dariya shima asim din Haka yace.
Aj ya bashi ansa da cewa"aiku naga kaunar taku ta tsufa dayawa shiyasa muka ce gara mudai musamu mu shige kafin muyi irin tsufanku."
Nan nabarsu na wuce ciki.Magabatansa sunje harga dady anyi komi ansaka ranar daurin aure sati mai zuwa.
Yau saiga anty B tauchi tazo don me za ai haka bacin sunsan hajjo na son Abdul.
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...