41.

82 7 0
                                    

*A DUNIYARMU*
Writing by mrs bb

                  41.

Saida naji karfina yakare muryata ta dishe saboda kukan,shiyasa na hakura amman na yanke shawarar gobe goben nan dole nabar gidan nan,banga wurin zama anan ba taya yarinya sa,ar islam wadda naba shekara kisan hudu taringa gaya man magana son ranta,kurin dan ina zaune gidansu ana hidimta man.
To bazan sake zama wani yayi man abuba har irin haka tafaru,zanje nayi aiki da jiki insamu kudi nayi wa kaina hidimar.

Hajiya da Amnah kuwa basuyi bacci ba,don duk inda hankalinsu yake atashe yake,tunda hajiyar ta tambayi Amnah abunda yafaruta zayyane mata,taringa surfawa hajjo balbalin bala,i karshe harda marinta tayi.
Taita kuka tana cewa bsu sonta zata tai wajen Anty B tunda su sun tsaneta.
Hajiyar tace"eh zanso haka da na huta kowa ma huta don gidanku,ke har  kinkai matsayin yiwa wani gori cikin gidannan,to kicigaba Abdul zai dawo zanji idan shine ya daure maki gindin iskanci cikin gidannan."

AJ bai dawo gidan ba yana can shida harun basa zaune,don kuwa jibine ake gabatar da shariar a kotu,suna ta kammala shaidunsu kuma lawyer su kwararre ne afannin aikinsa,yasan komi hujjojisu kadai sun isa su tabbatar wa da kotu gskiyar lamarin,tunda ga dady kabir yace shi zaizo ya fadi dukkan abunda sukai,ko A bazai rageba kuma bazai kara ba,don yanzu yasamu sauki hibba da harun kulawa suke dashi sosai,da Atu yaronta nanan har yayi wayau sosai don yafara rarrafe,har yanzu hajiya ma,u da ilham basu dawo ba.

Tunda yatai office bai zauna ba,shige da fice kurun suke wadannan yan iskan dasu kama wadanda aka turo masu,cikinsu harda wanda yayiwa Hanan fyade,shiyasa alokcin yace aware mashi shi waje na musamman,sadda ya waiwayar daga baya bakaramar azaba aka gana ashiba,don yadda Aj kejin radadin ciwon abunda yayi,haka yazage yasa akaimashi dukan fita hayyaci saida takai duk sirrin Alhaji kallah yatona,wannan yasa aka kyaleshi da bugun.
Wannan yayi mashi dadi don nan ma wata shaidarce akotu.duk wata shaida sun tanajeta sun kammalata,sun kuma bata kyakkyawa tsaro,don sunsan Ana iya zuwa afarmakesu akashe mutanen,in kuwa akai haka to komi zai lalace.
Harun yayi kokari sosai don shine ya bada wajen da za,a boye Dadynsa da wannan guy din da aka kashe ma yayansa,sai wanda yayiwa hanan fyade,sannan suka samu natsuwa.
Yaga sakon hanan, sadda ya ganshi murmushi kurun yayi,  ya ci gaba da hidimarsa.

Basu samu kansu ba sai karfe sha biyun dare,sadda ya dawo gidan kowa ya kwanta yanema kanshi abin da zaici ya wuce yayi wanka ya yi sallolinsa yakwanta sai bacci yayi gaba dashi,don akwai gajiya sosai tare dashi.

         ************
Washe gari hajiya da kanta taita dukan kofar lokacin ma ni walha nakeyi,saida nagama na bude.
Shigowa tai ta zauna gefen gadon mu tana kallona,
"Haba hanan sai kace yarinya ki kama kofa ki kulle duk kin tada mana hankali,wallahi nida Amnah bamu samu ishashen bacci ba,kiyi hkr da halin hajjo yarinyarce bata da wayau,duk Aj ya shagwabata gani take duk abunda tayi daidaine,karki biye ta zan dauki mataki mai girma akanta."

Shiru nai ina sharar kwallah tace"inhar kin daukeni uwa wajenki karki sake damuwa da lamarin hajjo,duk cikin mu babu wanda yake goranta maki duk matsayin yar gida haka muka daukeki,wallahi inajinki kamar Amnah da fati ki cire damuwa da maganganunta tayine don ta bata maki rai,kuma tayi nasara.
Bata hankaline kokadan duk don Abdul take wannan haukan kuma wallahi basonta yakeba nasan wannan,inhar na isa dake kibar batun cewa zakibar gidannan,nan gidankune kina ma dadamar kawo duk wanda kika gadama,inhar kin daukan mahaifiya to ki saki ranki kicigaba da sabgoginki kibarni da hajjo."
Ina kuka kasa kasa nace"shikenan hajiya nagode,insha Allah zanyi yadda kikace,amman hajiya don Allah abarni da batun makaranta,nidai na hakura da karatun yanzu sai zuwa nan gaba idan nasake samun natsuwa,jifa wasu suka ringa bina don Allah kice mashi yabarni da karatunnan sai nan gaba,hankalina yatashi ko na cigaba da zuwa bazan samu natsuwar dazan yi karatun ba."
Jinjina tayi tace"shikenan inhar hakan zai sama maki natsuwa zan mashi maganar,in yaso inkomi ya lafa kawai sai kitai UK can sai yafi."
Godiya nai mata tace natashi nafito akarya.

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now