*A DUNIYARMU*
Written by mrs bb.40
Gaba daya maganganunta sun tsaya mashi ga makoshi,kamar bazai fito ba saboda haushi,metake nufi da kalamanta to wacece matar tawa har da tace da alama itama girman kanne da ita.
Fitowa yayi yana bina da kallo nai kamar ban ganiba,saida komi ya kammala sannan na nufi lecture dina,kasancewar babu abunda yake bakona,nayi zaman makarantar kusan 3years shiyasa komi nakeyi sa compotable.
Babu wadda nakula duk yadda naga wata nason mun magana,sai insha mur don kokadan banson sabawa dakowa,balle har kisamu damar cin amanata kamar hibba.
Abu guda yatada man hankali shine,ganin wasu mutane duk inda nayi suna biye dani,hankalina yayi mugun tashi ko cap danaje saida na hdu dasu,duk atsorace nake text nayiwa Aj cewa.
"Nifa wasu na bina tunda nazo,duk inda nai suna biye dani pls i need ur help."Harna tashi lectures babu shi babu alamarshi,babu refly hankalina yasake tashi ainun,kamar naruga nabar makarantar.
Adaddafe nakarasa awannina bamu tashiba sai shida,sauri nake nshiga mota karsu ganni,kasancewar nan yabar mun motar.
Amman banyi nasara ba suma tasu suka shiga suka rufa manbaya,agigice nake tukin inayi ina waige bakaramin go slow na hada saman titin ba......duk nayi zufa najike sharkaf.....gudu kawai nake suna biye dani,nida nai niyar biyawa wajen zulaiha amman dole na zarce gida.....afujajan nashiga get din ko tsayawa gyara parking banba na fito aguje haka nashige gidan ina sauke numfashi.Zubewa nai falo cikin kujera ban ma lura da wai wake falonba,nafi karfin minty ashirin ina shashsheka da waigen hanya kosun biyoni.
Jinai anmun magana"Hanan,lafiya meyafaru."
Kallon mai maganar nayi Bilal ne cikin damuwa yake tambayata.
Hanya kurun nake nuna mai na kasa magana,Amnah ta fito dasauri tazo tana bubbuga bayana saboda ganin yadda jikina yake karkarwa,bakina yakasa magana.
Numfashina kamar zai barjikina isowa yai yace"keda waye biyoki akai sai lokacin nashiga d'aga kai."
Fita yayi da sauri har yana hada hanya har bakin get,yafita can waje yaduba ya hanga,har lungunan bayan layinsu ya leka amman baiga kowa ba,Saidai sawun tayoyinsu kenan sai anbiyotan,to suwaye har yanzu ba abar farautarta ba kenan.
Komo wa yayi yayita kwantar mun da hankali,cewa babu kowa sun tafi daker na samu natsuwa ajiyar xuciya kurun nake saukewa,duk na gigice ko jikata ban daukoba daga mota saidai amnah na aika taje ta daukoman bilal ya gyara parking din,ya kawo man makullin.Dariya naji ankwashe da ita babu kakkautawa,ahankali nakai kallona wajen maiyinta,bakowa bane sai wannan yarinyar mai jijidakai,mai shegen girman kan tsiya wacce take ganin tafi kowa watau hajjo.
Dagani har Amnah kallonta muke har lokacin dariyar take yi hankalinta kwance,saida ta tsagaita sannan tace"basa ban ba barawo da maraba,yau naga kauyanci da najima ban ganiba......saita sake kwashewa da dariya.
Amnah rai ba'ce tace"haba hajjo meye haka,ke wai meyasa koda yaushe sai kin sayar da halinki ne ehy."Kallon banza tayi mata kafin ciki tsiwa itama tave"dallah rufeman baki,badake nakeba kibari wadda akaimawa tatanka shishshigi ba kwarjini."
Amnah zatai magana na dakatar da ita nace takawomun abinci daki.
Barin wajen tayi tana hararar hajjon.
Nima tashi nayi nanufi daki don zuciyata ta kawoni iya wuya,inhar nace zan biyeta tokuwa zataji babu dadi,bankuma son dga zuwana afara samun matsala.Har na wuceta nakai kofar da zata sadani da bedroom din naji tace"aikin banza harara cikin duhu,idan anji haushi mutum ya koma tushensa mana,haka kawai anzo za,a takura mutane."
Cikin tsananin fusata najiyo nayo kanta,raina yayi matukar baci zuciyata har bugawa take na damki gaban rigarta,najijjigata cicin karfina na watsar tsakar falo,daidai shigowar hajiya idona yarufe ma ni ko ganinta banba nace.
"Kina takama nazo gidanku ko,kina jijida kai ina ci da sha da kwana nan gidan ko,saboda kina ganin cewa nidin banda galihu ko,nidin kaskantacciyace ko,tabbas inaci inasha ina kuma kwana gidanku,amman kisani nidin nafi karfin wulakanci nafi karfin tozarci ni ba matalauciya bace,amman nidin marainiyace marar uwa kuma marar uba,marar wa kuma marar kane banda dangin uwa banda na uba.
Tabbas hakane don wannan kike gayaman magana,don wannan kike mun kallon kaskanci to kiyi hkr zambar maku gidanku,inhar hakan zaimaki dadi.
Nawuce fuuuuu nashiga dakin banko kafar nayi nasa key.........silalewa nai kasa narushe da kuka,kukanda kosadda su Abby suka mutu banyishiba,kukane tundaga kasanraina yake tahowa,tunda narasa iyayena nakeyin wata kalar rayuwa,nakeyin rayuwa cike da kunci da bakinciki shin yazanyi da raina,inazan saka rayuwata inji dadi.
Har nawa wannan yarinyar take da har take gayan maganganu irin haka,menayi mata mena tare mata.
Wata zuciyar tace"taga kinshiga rayuwar AJ wanda shine dalilin tsanarki datai,don tana kishi dake."
Cikin kuka nace"inhar don shine nabarshi,nabarshi kamar yadda nabaro cikin mami,nama hakira da iyayena balle shi,na hakura da yah harun balleshi duk da tarin kaunar danayi mashi na tsallakeshi nabarshi,balle shi da ko kofar zuciyata bai kaiba...........kuka na rushe dashi inajin abunda nafada wata zuciyar tana karyatani..............inajin ana dukan kofar nai banza,don kowaye wallahi bazan budeba don ina iya hucewa kanshi.Jallabiyar nacire na saka riga yar yaloliya marar nauyi,don shara shara ma take saida nasaka legens gajere kyakar guiwa,sai have best sallolina nayi ina ta kukana nagama nahau gadon nacigana da rera kayana..........
Kuyi hkr wlh jikin babu dadi.
Mrs bb ce
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...