[6/15, 11:48 AM] Mom Muhseen: *A DUNIYARMU.*
Written by mrs bb
Mom muhseen.43&44.
Duk halin da ake ciki ya kwashe ya sanar wa Asim,tare da sake sanar dashi abunda yafaru yanzu shida hanan din.
Cigaba yai da cewa"wallahi banyi niyyar hutting dintaba itace ta tun zurani,akanme zata ringa furta kallamar so ga wani katon banza wanda nine nacancanta da ita,ayau nayi niyyar fara bayyana mata abun danakeji akanta,amman shine zata kuntata zuciyata saboda shi.
Bacin bakina da nashi yace mun inhar inason ta wallahi yabarmun saboda ahalin yanzu,bazai iya auren hanan ba saboda ganin cewar kawarta yake aure,zai so taje inda zata samu farinciki hakanma ya isheshi."Kallonsa asim yake yana sake danne dariyarsa don ida yace zaiyita yanzu tofa fada zasuyi,duk wani haushinsa kanshi zai juye mashi shi.
Yadan yi gyaran murya yace,"Aboki baka kyauta ba,duk abunda ta fada wanda yafi wanda tace bai dace kafurta kalamin da kayi mata ba,ai ko wani kaji yana gayamata irin haka sai inda karfinka ya kare,to balle ace kai dakanka ka yi mata haka,taya bazataji zafinkaba karinga controlling temper naka idan ranka yab'aci."
"Naji nayi badaidai ba pls taya zan samu ta sauko,zuciyata bazata jure fushinta ba wallahi nasan bazata sake kulaniba,pls Aboki bazan jureba inasonta Ina son Hanan,itace muradina itace mafarkina in ban sameta ba bazan taba samun natsuwaba."
Wannan lokacin duk yadda yaso danne dariyarsa kasa wa yayi,
Saida ta fito yadunga yi yana rike cikinsa,Kallonsa kurun yake cike da tarin haushi,
"Sorry Abokina wallahi kaban dariya,kaine fa kake cewa Kai ba kayin soyayya,daka ga yarinya kawai zaka fada ayi auren kurun awuce wurin,amman kaine yanzu duk ka fita hayyacinka kan so."Cikin shan mur yace"Asim banson iskanci,taya ina neman yadda zaka shawo man matsala amman kana man shine kake dariya,plsss solution nake nema."
"Shikenan Aboki tashi zakai muje wajenta don saika sauke girman kanka ka bayar da hkr gaskiyar magana."
"Nidai inhar zata hkr wlh zan bata,ahaka suka shiga wajen mama don ya gaidata.
*********
Bilal ne ya kawo Amnah har cikin gidan yashigo,yagaida su iya da baba.
hira muka hauyi sosai,muna dariya daga yadda ya ke yawan kallon mariya nasan cewa bilal ya kamu,ban dai ce mashi komiba har kusan tara na dare sannan suka tafi.KO minti goma basuyi da tafiyaba saiga Su Asim sunyi sallama,
Ina daki ni banma jiba mariya na karanta magana jari ta ukku labarin nan mai suna,
*Mai Arziki KO akwara ya saida ruwa*
Iyace ta leko dakin tana cewa,
"Zulaiha kifito ga Asim nan shida Abokinsa."
Wani irin bugawa kirjina yayi saboda har ga Allah wannan fadan da mukai baisa naji tsananin kaunar sa danake ya raguba,
Kallona tai nayi kamar banjiba muka cigaba da karatunmu,tashi tai tafita
Gaba daya hankalina yabar kan karatun,ganin haka yasa mariyar cewa."Anty ko mubari sai gobe sai A idasa."
Murmushi nayi nace"to mariya."Zulaiha ta fita can bakin motarsu tasha mur sosai,
Bata sake cewa komi ba bayan gaisuwa da tayi masu.
Aj yace"kinga nasan ta fada maki komi nasan nayi laifi kije ki lallaso man ita na bata hkr."Cikin rashin sukuni tace"Amman Yah Aj haka ake rayuwa tsakani da Allah,kai dakanka kafurta ma Hanan wadannan kalaman masu ciwo,ba itaba koni naji babu dadi."
Asim yace"sorry love Aboki yayi badaidai ba zuciyace ta tun zirashi,baiyyi da niyar bata mata rai ba Aboki yana son Aminiyarki nasan bakinso ace tarasa irin wannan zazzafar kaunar."
Ya fada yana dariyar shakiyanci bata rai Aj yayi yace,
"Wallahi Zan fasama baki gabanta,tau kacigaba da man dariyar."Murmushi tayi tanama Asim kallon kauna,tace"sorry yah Aj bashi ne yakar zoman ba."
"Au kema abunda zakice kenan,lallai kunyi daidai ba kuda laifi."
Juyawa yai zai fita daga zauren.
Asim yayi hanzarin rikoshi,
"Plsss sorry ba zamu sake ba kayi hkr."
Fizgewa yai yayi ficewarsa.
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...