39.

73 7 0
                                    

*A DUNIYARMU.*
   written by (mrs bb)

                  39.

Wannan ranar na kwana cikin kuncin zuciya,wata irin tsanar hibba ta ka mani,abunda tayi man duk bai ishetaba har saida ta auremun abunda zuciyata ke buri da kauna,anya bayan zuly zan sake yin wata qawa aduniya kuwa........hibba ta d'andanaman d'acin abota kuma insha Allah saitaga karshen cin amana tun aduniya.

Ban iya samun bacci ba wannan daren,abubuwa dadama nake tunawa nayi kukan rashin su Mami islam dina Abbyna,jinake mutuwar tasu ta dawo man sabuwa banyi bacciba sai gafda asuba daker da jibin goshi na yisalla sanan nakoma na kwanta,duk da cewa nasan inada school Early morning hakan bai hanani baccina ba.........duk nabaje kan gado don inajin dadin baccin sosai,rigar baccina duk ta yaye tazo iyakar cinyata,hular kaina itama tayi bangarenta daban,hannayena na yi filo dasu bacin ga filon can nabaro inda yake,baccina nake kasa rik'a.

AJ ne yafito cikin shirinsa zuwa office don yau ne zasu fara gabatar da karar alhaji kallah,dun tun ajiyan suka makasu station kuma yayi worning din dpo din kancewar duk ubanda ya bada belin su wallahi yagama aikin dan sanda saidai yanemi wani aikin,wannan maganar tashigesu matuka shiyasa duk yadda manyan abokansu da masu kudi harma da yan siyasar sukazo,amman kema da gus suka hana babu ma mai sauraronsu insunzo,yanzu yau yakeson ashigar da karar yana son ansar duk wasu evidence dake wajen hanan,duk da baison gininta,saboda yadda yakwana da bacin ranta wannan kukan datayi zuwan harun bakaramin k'ona ranshi yayiba,to metake nufi kenan har yanzu tana sonshi,da wannan bak'in ciki ya ga wayewar gari shiyasa har yanzu yakejin baison ganinta balle tasake bata mai rai,amman dole sai yaje.
Suit ne jikinshi farare da nick ajiki,sai bakaken sawuciki da agogonshi yagyara gashinsa yakwanta sosai, kamshi yake tayi sosai,dama wannan shigarce yake duk sanda zai zauna office 24 hours.

Amna da mai aiki keta hidimar kammala break,wasu masu aikin nata gyaran gida,hajjo tana zaune falo tana game,ga kayan zakinta gabanta tana ta sha ko karyawa bataiba.

Amnah yakira tataho cikin ladabi,
"Yah ina kwana."
"Lafia,ina Hanan."
Hanyar ta kalla kafin tace"tana ciki bansaniba ko tatashi,bari akirata."

"Kyaleta bari nasameta jiki hadaman abun da zan ci."
Tatashi yakoma kitchen d'in,kallon hajjo yayi ganin bata kulashiba yace cikin daure fuska,
"Baki gaida mutane ko,wannan banzan halin bazaki daina shiba,zamusama kafar wando d'aya dake cikin gidannan."
Shagwabe fuska tayi ganin yajuya yanufi dakin amnah,aguje tabishi.
"Yah mezakayo kabari akira maka ita ma.......wani kallo ya jefa mata yasa ta bashi hanya,wani bakin ciki yacika mata zuciya akanme zai shiga d'akinda take,sai yaje yaganta babu kayan arziki,wallahi nidai ina gidan nan wannan yarinyar bata isa ta rabani dakai ba,saboda kaine rayuwata.
Abunda take fad'a cikin ranta kenan.

Knocking yake babu alamun aza,a bud'e kawai sai yabude yashiga.
Idonsa yayi mashi kyakkyawan gani,cinyoyinta ne bayyane farare sol,gashinan yabaje saman gado iskar fanka sai d'agashi take.
Don yama rufe mata fuska sosai,ahankali yake bin duk wata gab'a ta jikinta da kallo,har Allah yakai idonsa kan albarkatun kirjinta..........uhmmmmmm wani numfashi ya sauke tare da saurin kawar da kanshi,dafe kan yayi yama rasa mezaiyi,tashinta zai koko fita zai yabarta aa ina bazan iyaba kowa na iya shigowa yaga irin halin da take ciki.
Bargon dake bayanta ya jawo yashiga rufe mata jikinta,har kan kirjinta,sannan yafara tattara gashin yana son janye matashi kan fuska kenan na tashi,.............
Kallon kallo muke kafin kwalwata tafara aiki,azabure na tashi zaune inajan bargon ina jabaya harna dangane da jikin gadon,sai raba ido nake,tashi yayi yajuya baya zuciyarsa bugawa take sosai daker yajawo maganar dazaiiyi.
"Kitashi hakanan karfe takwas da rabi kinada lecture,kishirya ina falo am waiting for you,har yakai kofa yajuyo idonsa cikin nawa yace"kifito da evidence din dake wajenki."
Yafice wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke,dafe goshina nayi nace"wannan guy akwai daukar hankali,to me yakawoshi dakin nan batare da yanemi izinin wanda keciki ba,nashiga ukuna Allah yasa bai kalleni mun jikiba.
Janye bargon nai ina kallon kaina,zaro ido nai wayyo Allah Badai haka ya taddaniba."
Najima ina takaici kafin nashiga nayi wanka,simple dress nayi jallabiyace baka tasha kwalliyar duwatsu masha Allah,nayi rolling bayan na gyare gashina na daureshi tsakiya,hoda da kwalli da man baki nasa sai turare na amir oud,nikaina naga kayan sunmun kyau,daya daga cikin najiya ne jikkata fara sol na dauka da fararen takalma hills,amman bamai mugun tsayin nanba.
File dina nadauko nafito ina ma zulaiha text cewa zanje school idan nadawo zan biyo akwai magana.

Hajiya nashiga na gaida taita saman albarka dayin adduar Allah yabada sa,a,naji dadi sosai harda bani 5k inyi break in naje.
Yau azumi na tashi dashi daurere kasancewar dama bana sahur inhar zanyi fasting,Amnah tayi mun tayin break nace"sorry dear inni sa,imun."
Dariya tayi tace"ok anty Allah yabada ladar."
Hajjo nanan ko kallo ban ishetaba haka nima iskar dake kwasarta ma bata gabana,bin bayanshi nai don yana hangoni yafita Amnah kemun saina dawo nace"ok my dear."

Sabuwar mota yasiya inajin don dagani sabuwarce sai daukar ido take,jikin motar nasamai yana danna waya,ya kanga ga kunne kallona yake tunda nafito nai kamar ban ganiba,jinai yatullo min key daban luraba saiya samu goshina"kijamu."
Tsaye nai ina mamaki"kijamu"kenan nizanyi tukin,girgiza kai nai kurun nazagaya baya inda driver kezama nazauna.
Allah yasa ban mance yadda ake driving dinba na anbata can kasa kasa,ahankali natada ta tabata wuta nayan mintyna sannan nai kwana nadoshi get,waya yake yi anma banmajin meyake cewa,saboda shegen kilbibi saikace mace,kaita wani make murya.

"Ina zamu."
Nace dashi bayan yagama wayar.

"B U K"
Bansake bi takanshi ba na yi kwana naci gaba da tukina,ina ganinsa ta gefen idona kallona kurun yake,dayaga zan juyo sai yakawar dakai..........traffic ne ya tsayar damu na dan lokaci kafin wani dan sanda yazo wajemu.......yana ganinsa ya kama sara mashi hana dukawa yana gaidashi,kafin yace mun"good morning madam."
Ansashi nai ina fara,a muka wuce nasake shan mur kamar naga wani abun kyama.
Abun yabashi haushi kenan shine baza tayiwa dariyarba,ko gaisuwa basuyiwa junaba sai daukemashi kai take,jiyai bazai iya jurewa ba saiya tanka.
"Don me zaki ansashi kina mashi dariya,kurun dan ki zubarmun da kima."

Kallonsa nai up and down na kauda kai nace"Au karnayi dariya kamar kai kenan,ai murmushi ga d'an uwanka musulmi sadakane."

"Nasani,malama Hanan Kinsandai matsayina ai karki sakemun irin haka,sokike yaje gaba yakara magi da gishiri."

"Oh wai kana gudun karyace ni matarkace yaje yace matar *SS ABDULJABBAR* batada kamun kai ko,to kwantar da hankalinka Alhaji Abdul jabar Hanan bata kama da matarka,don da alama matar taka ma girman kaine da ita like u."

Ina gama fad'a naja bakina nai banza har muka shiga school din nai parking.

Mrs Bb ce👌🏻

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now