*A DUNIYARMU*
written by (Mrs bb).36.
Muna shiga falon hajiyarsu zaune wata budurwa mai mugun kama da AJ tana daddana mata k'afafunta,ga wata budurwar itama gefe tana tafaman danna computer.......sallamar damukai ce tasata d'agowa daga dukiyar datai,hajiyar kuma ta washe fuska tana dakatar da budurwar dake danna mara k'afa....."Aaaaaaa Hanan sannu da zuwa diyata sannunki,zo maza ga waje kusadani zauna,matsa Amnah matsa gefe mik'o mata tuntun ta zauna sosai."
Tsaye yayi yayi polding hannunsa ga kirji yana kallonsu,
Amnah tace"hajiya duk dokin ganin hanan dinne."
Kallonta tayi tace"eh wlh Amnah d'okinne maza tashi jeki had'o tire,daman tun d'axu nake fama da hajjo akan ta had'a tak'iya.....saboda wani banzan Assignment d'inta."
Dariya hajjo tayi tace"tuba nake hajjajuna wallahi idan nabari yah bilal ya dawo ban gama wannan Aikinba nashiga ukuna kiyi hkr."
Banza tayi da ita Tamaida hankalinta kan hanan.
"Sannu d'iyata kullum mita nake akan akawo man ke amman saiyau yaga dama."
Murmushi nayi ina kallonshi shima shiyayi yana isowa wajenmu,su Amnah suna gaidashi ya ansa yazauna gaban hajiyar yana lank'washe k'afafunshi yace"ni bandani sannun hajjaju,bacin ni yadace ayiwa sannun duk irin gajiyar dana kwaso."
Harararsa tayi tace"naji wanan,tashi Hanan Amnah ta nuna maki d'aki kiyi sallah ki watsa ruwa kizo ki ci abinci."
Ina murmushi nace"to hajiya."
Natashi ina gyara mayafina nabi bayan Amnah.........inajinsu shida ita da alaman dai sunsaba haka tsakaninsu.
D'akin masha Allah komi yayi towel ta d'aukoman sabo ta ban tace" bari naje in kawo maki kaya don naga kayan yah hajjo zasuyi maki."
Murmushi nayi mata nace'kinga barshi nazo da kayana kicewa yah Abdul yabude but ki d'aukoman."
Face"angama Antyna."
Murmushin nima nayi ina juya kalmar Antyna ganin bangane inda ta nufa ba kawai nashige tiolet din.
Wanka nayi da sabulu nayi alwallah na fito,harta fiddoman komi ta na jerawa cikin wadrof d'insu,ta ware inears da kananan kaya da kayan shafa,ta kuma ware man wad'anda zan saka......murmushi nayi nace"sannu da k'ok'ari Amnah,Kinfa kyauta."
Dariya tayi batare data juyoba tace"Haba Antyna daga zuwa sai nabarki da wahala,wannan aikin nawa ne ga kayanan nasan zakifi jin dadin saka marasa nauyi."
Kallon kayan nayi doguwar rigace yar sawai murmushi nai nace"godiya mai yawa."
Batace komiba tacigaba da shirya kayan tana man hira,hajjoce ta shigo fuskarta babu yabo babu fallasa tace"Bak'uwa sannu da zuwa d'azu bamu gaisaba."
Fuskata wasai nace"ah haba walh babu komi yakike ya gida."
Wucewa take zuwa can wajen bed side drower tace"lafiya lau."
Bansake ce mata komi ba har Amnah ta gama ta juyo "to Antyna na gama inkin shirya sai muje ki ci abinci bari naje nasan yah najirana."
Fita tayi tabarni da hajjo hayewa gado tayi tana danna waya,bandai sake kulata ba nayi sallolina na gama sannan na fito cikin falon.
Babu kowa sai TV keta surutu wajen da aka shirya man abincin nanufa,nazuba ina ci ina kallon TV Kafin najiyo motsin fitowa hajiya ce ta fito tana ta fata,a
Isowa tayi tana cewa"harkin fito hanan."
Kai na k'asa nace"eh hajiya."
Hira tayita jana ina biyeta don naga bata da wuyar sabo saidai bansan meyasa nakejin yauyinta ba,nagama ci nakauda kayan nazo na gyara wajen tana cewa in daina akwai mai aiki zatayi,nace aa bari dai nayi nagama nadawo muka cigaba da hirar take cewa,
"Hanan ya akaji da hakurin rashi,ubangiji yajik'an su yayi masu rahama Allah yasa sun yi shahada."
Idona yacika da kwallah nace"angode Hajiya kuma ai kunsha naku rashin,Allah yajik'an Abba Allah yasa halinsa na gari yabishi,Abba ya sadaukar da rayuwarsa madadina hajiya insha Allah Aljannah ce makomarsa,bazan gajiya da yi masa Addua ba har in koma ga mahaliccina,Abba mutunne yayi abunda y'an uwan mu da ya kamata suyi basuyi ba,sai ma kokarin ganin bayana da sukeyi,hajiya bacin ku yanzu banda kowa banda wani wanda zan kalla inji dadi......kukana yafito sosai muryata har rawa take......kusadani ta dawo ta rungumeni jikinta tana lallashina,
"Hajiya kamar yadda wancen karon suka so halakani nida Abba,Allah yasa wancen karon inada sauran numfashi agaba,Abba kuma yatasu.....hajiya yauma sune suka biyomu nida Yah Abdul jab.....bansan yadda akai muka tsiraba.....nasake fashewa da kuka mai cin zuciya.....Amnah da Aj duk sun shigo falon ban ma saniba shashshekar kukana kurun nakeyi hajiya na ta bubbuga bayana.
Shiru falon yayi Kowa yana sauraren kukana zuwa can hajjo ta fito,tasamu waje k'asa kusada Aj tana lankwashe kafafu tave"uncle don Allah kaduba man wannan formular wlh tun safe nake ta faman solving Amman abun yak'i yuwuwa,kuma yah Bilal yaban aikin haka nan don yak'ure lissafina."
Kallon computer yake yana kallonta,kafin ya ansa ya ajiye gefe kurun ya koma cikin kujera ya lumshe idanunsa.Cikin lallashi da tausar zuciya tace"kiyi hkr Hanan kowa ne bawa da kikagani da kalar kadarar rayuwarsa,kuma jarabawace kiyi Adduar Allah yabaki ikon cinyewa,kuma insha Allah komi yazo karshe duk mai hannu cikin wannan abun bazai shaba,karki saka damuwar komi cikin ranki kinga makaranta zaki koma."
Na tashi daga jikinta nace"hajiya don Allah ki saka baki Yah Abdul yafita daga cikin case dinnan,inajin tsoron kar shima suyi mashi wani abun."
Murmushi tayi tana dafa k'afadata tace"karki damu Hanan,Abdul yasan me yakeyi kuma zaiyi komi don ganin duk dukiyarki ta dawo gareki,kuma zai mik'asu hannun hukuma,insha Allah kukanki ya k'are Hanan insha Allah kamar yadda kika ga su Amnah kema haka zamu cigaba da zama dake acikin gidannan,fatana kicire komi kifuskanci gabanki yanzu."
Jinjina kai nayi ina share fuskata,Amnah ta kawo man ruwan sanyi na kurb'a nayi mata godiya.Hajiya ta kalli AJ tace"Abdul kana lafiya kuwa "
D'agowa yayi yana d'an jujjuya kai"wlh hajiya kaina ke ciwo,inajin gajiya ce kurun."
"Ayya kasha magani sai kaje ka kwanta ka huta nasan gobe kanada ayyuka sosai,ya batun zulaiha da Asim."
Nan yace masu Amnah subar falon,
Sannan yasoma yimata bayanin yadda suka shawo kan Baban da kuma ciwonshi,har kan yadda akai fama da zulaiha wajen tahowa.
Tayi sallalami tayi ma Baban Addua tare da cewa goben sai muje harda ita aganoshi.Bilal ne yashigo ganin Yayanshi yasashi washe baki,
"Broth kaine yau kenan,harna ce kila sai mun bika bauchi kilan Hanan ta had'a dakai ta rik'e."
Duka ya kaima shi ga baya ya goce,dariya yayi yace" Hanan barka da zuwa ya bauchin."
Murmushi nayi nace"tana can mun baro ya aiki mun sameka lfy."
"Wlh lafiya lau,ina yaran nan hajiya yunwa nakeji."
Tashi nayi nace"bari na kawo maka."
Saurin tashi yayi ya biyoni yana cewa can k'asa k'asa,
"Kirufa man asiri kar boss ya bani punishment."
Cikin mamaki nace"saboda kai mashi me kenan."
Dariya yayi yace"muje dai in tayaki d'aukowa amman bazan barki ki yi ke d'aya ba."Tare muka dawo falon Aj suna hira da hajiya duk akan wannan issue din,had'a ido mukai wani kalar kallo yajeho man saida naji kamar zan narke awajen,hajjo ce ta fito cikin kayan bacci masu masifar kyau sai yatsina fuska take,
"Yah bilal wlh nidai nakasa wlh saidai karik'e kudinka."
Dariya yayi yana kai lomar abinci bakinsa yace ma Aj,
"Gasa muka saka nida ita da Amnah,cewar inhar sukai man wani solving math zan basu kyautar 20k,Amnah dai tayi kokari sosai taci rabin kudin,ita ko mutuniyarka kwana uku kenan ko 1k ta kasa ci."
Murmushi yayi yace cikin low voice d'insa da tayi man dadi,
"Ga shinan ta kawo man wai induba mata,kenan danayi kan kazo taci banzai."
"Sosai kuwa don nace bazan bata ko sileba idan bata fiddashiba,ke wannan karatun naki na ha inci kikai ko,shekara hudun abanza kika b'atota."
Ta turb'une fuska tafara diredire kusada AJ,tana kuka....."hajiya ki shiga tsakinina dashi kinajin abun da yake gaya man cikin mutane,wallahi saina rama aidama rannan gaban friends dina karinga dizgani,bance maka komiba shine yanzu zaka sake ko......kuka kawai take hajiya na lallashinta.......idonshi lumshe yasaka hannu ya jawota gabanshi,ya dora yatsanshi kan bakinta alamun tayi shiru......kamar anyi ruwa an d'auke haka tayi shiru,kafin ya bude idonshi kanta yace"mezakiyi da kudi."
Cikin shagwaba tace"bikin shuhuda fa za,ai this week kuma nice babbar kawa Uncle anfiddo anko kala uku Hajiya tayi man guda saura biyu kuma idan banba wlh ajina zubewa zaiyi."
Shike goge mata kwallar yace"sorry daughter zan baki ni kamar nawa kike so "
Had'a ido mukai ta yiman wani kalar kallo bance komiba ta juya kanshi tace"uncle ni 35k nake so,daman idan yaban 20 xanje wajen Anty fatima ta cikasa man sauran,tunda Anty B tace ita bata iya wannan adashen ba babu ranar kwasa."
Haji ya dariya kurun tayi tace"kunga dare nayi saida safe,hanan mukwana lafiya kije d'akin Amnah sai ku kwana,wanan dai bata son mutane kamar mujiya."
Har falo na rakata na dawo,
Samunta nai tanata godiya ga kudin gabanta tana yiwa bilal gwalo,
"Yace wllh broth kaike shagwaba wannan yarinyr,harta rainani irin haka.""Kadaina biyeta biye matan da kake yasa take gayamaka mgn,ni tayi man mana."
Nidai kwana nayi ina tafiya nace masu,
"Saida safenku."
Bilal ya ansa inajin idonsa akaina har nakai k'ofa bankuma juyo ba,don haka kurun naji haushinsa nakeji,na kula wannan yarinyr ba yar gidan bace,don yadda duk tasha banban dasu akan komi ma.Sadda naje Amnah harta gyara mana gadon,yayi kyau karatun kur ani take inashiga tayi addua ta shafa,
"Antyna kishigo yanzu nake shirin zuwa kiranki kizo mu kwanta idan kika biye yah Abdul da Hajjo sai ki kai 12 koma sama da hk."
Yak'e kurun nayi inason tambayarta amman sai naga baidace ba,kayan bacci ta ban sabbi masu kyau nasa muka kwanta muna hira sama sama......wayata tayi kara na jawota naga miss call din Zulu har biyar,sai sak'on daya shigo.
Ban Kira ta ba don ganin dare yayi kuma tana asibiti karna takurata,massege din na duba naga sunan.
*YAH ABDUL JAB.*
*_BABU GOOD NIGHT KO TUNDA KE BAKIYI MAN NI NA MAKI,AYI BACCI LFY.*wurga wayar nayican gefe nahau addua na kwanta.
(Sai nace mukwana lfy Hanan)
Mrs bb ce👌🏻
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...