[3/15, 7:28 PM] Maman Muhsin: 🥎🥎
*A DUNIYARMU*
🥎🥎
Written by (Msr Bb)Wannan book d'in nakud'ine daga page d'in farko zuwa na goma, zai zama free ne nairar ki d'ari biyu tabiya maki buk'ata.
Name:halliru salisu
Acc:3094299530
Bank:first bank
Idan kituro saikiyi screen shot shedar kinbiya ta wanna layin 09034722970Ga masu turo katin waya kuma,zasu iya tun tub'ar wannan no. d'in
09034722970*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI*
Free page
8.*Remain page biyu free yakare*
Falon na tun kara ina k'arajin gabana duka baki k'ofar shiga najiyo hajiya ma,u tana magana cike da masifa tana cewa,
"wallahi Alhaji baka isaba ko sama da k'asa zata had'e Harun bazai ta'ba auren wannan yar iskar yarinyar ba,hafiza zai aura idan kuwa har kace nace wallahi daga Kai har ita bala,in da zai sameku nikaina bansan iyakarsa ba.""Ma,u kenan naga dani dake Waye zai nasara,nidai Nace inhar Yarinya nason shi to duk duniya babu Wanda ya isa ya dakatar wannan auren,kifada da ihu ki k'ara da Wayyo."
Lumshe idona nayi inajin wani irin ciwon kai yana dandak'a saboda tsananin tension,
Nayi shahada na tura k'ofar bakina d'auke da sallama duk idonsu akaina sai naji kamar na zunduma aguje, kowane kamar zai hallakeni da kallo, duk tashin hankalin da nake ko kad'an babushi ga fuskata haka jikina babu inda yake rawa ko karkarwa.Waje Na samu k'asa na zauna hajiya ma,u kamar ta tashi ta kaimani shak'a saboda tsananin haushina da takeji,
Harun ne yayi sallama yashigo idonsa akaina, sai gabana yafad'i saboda yadda duk naga ya rame, nan take naji wani masifeffen sonsa da kaunarsa sunman dirar mikiya,jinake zuciyata tana Wata irin azalzalata akan cigaba da Kallonsa.
Amman na hanata saboda muddin nayi hakan bazan iya aikata abunda yake daidai ga rayuwata bah,
Inama zan iya zubda kwallah Inama zan iyayin kuka awannan halin, Anya kuwa ban zalinci zuciyoyinmu ba? Nayiwa yah harun adalci?
To Amman banida Wata mafita data wuce wannan..........maganar dady ta katseni daga halin da zuciyata tashiga kiran sunana yayi,"Hanan."
D'agowa Nayi ina kalllonsa batare dana amsa ba,
Cigaba yayi da cewa"harun yayi Mani maganar yana sonki,nima kuma naga haka saboda tsawon shekara da shekaru kenan bai tab'a zuwar mani da maganar Wata ba sai ke,shiyasa banyi sanya ba nace bari naji ta bakinki don atsayar da magana."
"shin kina son harun zaki auresa matsayin mijinki?ina jiran jin ta bakinki."Wani kidahumin kallo hajiya ma,u take auna mani tana cije baki,
Kallon Harun nayi inajin zuciyata tana tsanan ta bugu,duk ya marairaice fuska kamar zaiyi mani kuka sai naji bazan iya furta kalmar dake bakina ba,inason yah harun bansan Ina sonsa haka ba sai yau, nan take naji bakina yana cewa,"eh dady Ina sonsa."
Idona na kanshi nafurta wannan maganar saidai nagama furtawa sai naji ashe wai duniyar tunni natafi.
Katseni yayi yace,
"ke nake saurare kintsaya kinata kallona."Kaina yana k'asa Nace,
*"dady Yah harun bai fahimceni ba,amman ni ba sonsa nake ba kayi hakuri yah harun baka fahimceni bane."*Wata muguwar dariya hajiya Ma,u ta kwashe da ita,
Tace"Allah ya auna maki gyad'ar dogo don billahil azaim da na lahira sai yafiji jin dad'i,bama keba har shi uban naki bazan kyaleba,kaikuma tunda kaji matsayinka saika shiryama Auren hafiza don duk duniya ba kada mata data wuce ta."Tatashi tabar falon,shiru ya ratsa don dady huking yayi,jin juwa na d'aukarsa yasashi neman kujera ya zauna,harun yana layi kamar d'angiya haka yafice daga falon,jiyake gabaki d'ayan duniyar batai mashi dadi hatta bakinsa d'aci yake mashi baisan da yaya yakai kanshi d'aki ba.
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...