37.

63 6 0
                                    

*A DUNIYARMU*
    written by (mrs bb).

              37.

Da asuba daker na tashi,ban san na gaji har haka ba sai da bacci ya sace ni idona har kullewa yake ina sallah,daker da jib'in goshi nayi Adduoi na sannan na kwanta saman abun sallar dandanan bacci yasake sureni.

Ban tashi ba saida Amnah tayi man dagaske sannan,taita man dariya wai haka na kulla amana da bacci.
Dariya nayi ina mika tare da salati nace"wlh Aa Amnah,gajiya ce kurun don da anbarni zan iya kai 12 ina bacci na."

Dariya take tana rike baki tace"halinku guda da yah AJ don mashi yana dadewa kafin kiga yayi bacci haka,amman wani zubin weekend ne chans dinsa."
Bance komiba don ta tuno man da abunda ya faru jiya........barth room nashige donyin wanka inajin tana cewa bari nima naje na ida aikina.

Na jima ina cikin kwomin sannan nafito nazauna gyara jikina,farar powder na saka na dan saka lipstick,sai kwalli doguwar rigace ta less darkblue da fari yayi kyau matuka,kunsan dark din abu yana yiwa farin mutun kyau.
Bubace rigar ban saka kallabin ba gyalena fari nayi rolling kaina dashi,bayan nagyara gashina na daureshi da rubom nayi donet da gashin,sai yayi kamar acuci.
Wankan turare nahauyi babu kakkautawa saida naji yayi man yadda nakesawa sannan na ajiye,wayata na dauka nashiga kiran zuly,ina nufar cikin gidan........."haba wa daga kin samu AJ shikenan baki ko tunawa dani."
Murmushi nayi nace"kibar wannan maganar don Allah,yazu dai yajikin baban,kinsamu iya da mariya lafiya ko."
Muryarta cike da farincikin dana jima banjita haka ba tace,
"Wallahi Hanan gani ga iya ga yah umar ga mariya,baba kuma insha Allah muna kyautata zaton dacewa,nanda awa biyu zai farka,hanan bansan da wane bakin zanyiwa AJ da Asim godiyaba Don Allah kitayani gode masu,sunyi mani komi sun nuna man kauna wadda bantab'a zatoba......dajin muryar ta kuka take don farinciki.....hanan kin taka rawar gani cikin rayuwata,bazan tab'a mantawa dakeba.....kukan yaci karfinta jin danai bazata dainaba kurun saina kashe wayar,don nikaina jinai kwallar zata kucceman.
Falon Babu kowa zama nai ina kallon labarai,zaro ido nayi ganin abun da labarai kecewa.
Alhaji kallah mujitafa tareda Alhaji Musa mas,ud sun b'ata,tun daren jiya ba,agansuba kuma hukuma tana tsaye kan lamarin,duk wanda aka kama da hannu cikin case din to kuwa kashinsa yabushe,sannan duk wanda yazo da labarin ganinsu ko makamancin haka yanada kaso mai tsoka.
Jinjina kai kurun nake babu kakkautawa,tabbas ko babu tantama Aj ne da wannan aikin,to miye hikimarsa na yinhaka atunina zai mik'asu ga hukumane........jinjina lamarin kurun nake,har akagama nuna news din babu wanda yashigo,saida shad'aya tayi sannan hajiya tafito,bilal ma haka sai Amnah.
Gaishe gaishe akai kafin ahau table.
"Bilal yace yah bai tashi bane."
Hajiya tace "shikau ya riga kowa tashi"

Amna tace "ina yaje haka da safe yah baya gajiya wlh."

"Uhm shiyasa kanshi,tun da uwar safiya hajjo tajashi wai yakaita shopping,yau take son siyo kayan takai d'inki,muna nan daku bazai dawo gidan nan ba sai kusan azahar."
Wani kududu yazo ya tokareman wuya,shin wai wannan yarinyar meye alakarta dashine,wannan zakewar tayi yawa.......jinake dankalin dana ke taunawa ya tsaya cak,saida na bishi da ruwan tea sannan ya wuce,uffan bance ba har akagama break din.
Ganin idan muka zauna jiranshi bazamu fita yanzu ba yasa nacewa hajiyar"hajiya mai zai hana Tun da ga Bilal shi yakaimu Asibintin,nasan kilan bayanzu zasu dawo bah."
Jinjina kai tayi tace"sosai kuwa hanan,haka za,ai kai tashi ka saukemu Aminu kano hospital."

Hada Amna mukatai sai hira take mun,daker nake bata ansa,don Allah yasani wannan abun yaki wuce man ga wuyana,bakinciki nakejin zuciyata naciki.....yake kurun nake har muka isa.
Bai farkaba saura duka awa daya,anyi gaishe gaishe sosai da jajantawa tsakanin iya da hajiya,da zasu tai tyi masu alheri mai yawa sai tsokanar zulaiha take,nan suka barni sai dare ko yamma Bilal zaizo ya tai dani kasuwa zanyo siyayyar kayan dazan anfani dasu,tunda gobe makaranta.

Munsha hira dasu iya sosai kamar munsan juna,sai godiya take man tana cewa ai zulaiha tabata labarina,ta kumayi man gaisuwar iyayena,naji dadin hakan sosai mariya kuwa Anty sama anty kasa haka taketa kirana,naji dadin hakan.

Zulaiha tace jiyan saiga mama da dadyn Asim harma da hasina da mijinta,don kwanan nan akai bikinta.
"Nace to ya ya babudai wata matsala ko."

"Wallahi Hanan nima nayi tunanin hakan,aman kuma sai naga ba hakaba,cikin mutunci dadynsu suka gaisa dasu iya,yayi mata jaje sosai yabada dubu dari yace asai ma baba magani,mama kuwa abinci mai rai da lafiya ta kawo mana,mijin hasina yabamu dubu ashirin."

"Nace Alhamdulillah!wallahi abunda naita zullimi kenan amman naji dadi,insha Allah zulaiha komi yazo karshe natayaki murnan samun daidaito tsakaninki da iyayen Asim da kuma naki iyayen,saikiyi hankali ki dauki darasi yanzu zagewa zakiyi kicigaba dayi masu biyayya kina kyautata masu."

Tace"wallahi hanan dolena ne bakamar danaji labarin musabbabin abunda yyi cousing ciwon k'afar baba."
Cikin mamaki da zak'uwa nace"meya faru."
Tace"uhm yaya auwal ne,ingaya maki wannan mutunen mugun butulune,bayan barina gida ashe yashiga yiwa baba sata babu kakkautawa,can wajen aikin nasu da anbashi aiki wanda yakawo gyara yabiya kudin sai yacinye,bazai ba baba ba tun baba na kawaici yana kyaleshi har yakai yana tankawa,to donme zai tanka yaringa mai rashin kirki maganganu kala kala,karshe yabi dare ya yiwa baba mugun bugu,har ya kairyashi yakuma kwashe duk kudin da baban ke tarawa idan zaima mariya aure yagudu dasu.
Shinefa ciwon yakai haka bayan tafiyarshi aka zo ana neman shi shida baba wai kanwar baban uwar yaya auwal tarasu gidan karuwai,suje sudauko gawar.
To badai wanda yaje bansan ya sukai da gawarba."

Jinjina kai kurun nake ina goge kwallata nace"zulaiha idan baka kyautata ma iyayenka ba yanzu wa zakayiwa,shiyasa kayi anfani da damarka kafin ta kuccemaka,Allah yana sonki tunda har yabaki dama sau biyu,karki yi wasa da ita kiyi kokri yanzu kece jigonsu,yah umar karatunsa yake,kisamu Asim yasamar maki aki kina tallafar rayuwarsu,zakiyi mamakin albarkar da zaki samu."
Munjima muna tattaumawa iya najimu sai albarka take saman,baba ya tashi cikin yardar ubangiji likitan kuma ya tabbatar aikin ya tafi successful,murna akaitayi da godewa Allah nayi kukan tausayin baba da zulaiha yadda suka rungume juna suna kuka,kowa naneman yafiyar kowa.
Kamar bazan baro wajenba haka naji,amman dole nabiyo bilal muka shiga boutique,kaya nasiya readymade size dina da takalmomi,jikuna sai abubuwan dai danasan i need it,dan wannan lokacin naji munsaba dashi sosai,akwai barkwanci Bilal sosai.
Ban sake bi takan AJ ba bai kirani ba nima ban nemaiba.

Mun nufo gida kenan naji  gabana yana fad'uwa kirjina yana duka,wani yanayi naji bansan ya akai ba nji yah harun ya fado man ga rai.........lumshe idona nayi ina jin kwalla,jinai ganinsa kurun nakesonyi jinake kamar nace Bilal yayi kwana yakaini gidansu,amman bazan iyaba.......cikin wannan halin muka karasa gidan,daidai kuma tsaywr motar AJ da alamun su biyune..........nai zuru da idona kan kofar mai zaman banza,sonake inga waye hakanan naji inason ganin kowaye......kafarshi yazuro naji kirjina yabuga,kafin yafito gaba dayashi...........idona nazaro gabaki dayansu waje ina kallonashi......yayinda shima idon shi yake kallona......jinai jiri yana dibata kamar zan fadi......bansan sadda natai luuuuu.

Mrs bb ce👌🏻

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now