page 11

75 3 0
                                    

*A DUNIYARMU*
   
Written by (Mrs bb)

Wannan book d'in na kud'ine Kiji tsoron Allah karki tura ma wasu inkina tsoran Allah Amman.

Dari biyu ne ba yawa ta biya maki buk'ata ga account number nan.

3094299530
Kokuma transfer ta katin waya ta wannan no. 09034722970.

11.

Sai dai farkawa nayi na ganni  cikin wata duniyar wani da jine bukkokin dake cikinsa Na mutanen dake rayuwa wajen bata Kai goma ba wallahi zulaiha,alamun dai su kad'ai Suke rayuwa cikin wannan kun gurmin dajin,jinai jikina bazan iya yin wani Motsin kirkiba saboda an d'ad'd'aireni da wasu igiyoyin magani, jikina wasu ganyaye ne d'auke da magani jikinsu,an lillib'eni dasu babu wasu kaya tare dani.......saboda jikina babu inda babu ciwo bakina saboda ragargajewar da yayi bana iyayin magana,idanuna kawai nake iya juyawa suyi motsi suma na k'arfin halinsa saboda yadda fatar Idon ta kwaye ta kubura bama sosai zakiga kwayar idon ba, sai hawaye dakebin gefen fuskata suna kwarara........... Shashshekar kuka ta hana na cigaba.

_shiru zulaiha tayi tana d'igar da kwallah tama kasa lallashina,hanky ta zaro cikin jikkarta ta bani na ansa ina share kwallan tare da kurban ruwan kafin nace,_

_"anya kuwa zulaiha zan iya cigaba da baki labarin nan kuwa? Kinsan halin da zuciyata take ciki kuwa?duk abubuwan da kikaji bafa yana nufin sukenan ba,akwai wani tabon da har na koma ga Allah bazan tab'a man tawa da shiba haka kuma ciwonsa da rad'ad'in sa har abadan bazan daina jin sa ba._

_tana goge kwallarta tace,_
_"Hanan kiyi hakuri ki idasa mani Idan ki ka barni haka zan kasance cikin tunani da sonjin yadda kika rayuwa har kawo zuwanki kaduna."_

_shiru nayi Ina sauke Ajiyar zuciya kafin na cigaba da cewa._

Ina  nan kwance wani tsohon mutum ya shigo, tsohone sosai don da sanda ma yake tafiya, ganin na bud'e idona ya saka shi isowa gareni hausar sa bata fita sosai yace,
"binti kin farka?"
Ganin hawaye nata kwarara gefen fuskata yasa ka wani k'yalle yana goge mani hawayen, murmushi yayi Mani yace"akwai rad'ad'i ko? To kiyi hakuri zaki warke cikin Kwanan nan,don magani ya fara bin jikinki da ya idasa bushewa zaki warke tass, ai mun gode Allah sadda muka d'aukoki mun zaci gawa ce saida sambarutu tace xuciyarki tana bugawa, munsha wuya kafin muyi maki magani ki godewa allah shine ya ceceki."

Yawan gudun ruwan hawayena zai nuna maka cewar inajin sa, kuma maganar tana shigata ba komi yake sakani kukan ba sai Bawan Allah nan da ya rasa rayuwarsa akaina yanzu ahalinsa suna can cikin tashin hankali,wane irin mutun ne shi mai sadaukarwa haka,lallai Allah bazai barsa haka ba ba ma kawa ya ta nadar masa acan ranar gobe kiyama.

Haka naci gaba da rayuwa da wad'annan mutanen masu karamci, ba sufi  sha ba duk fad'in wannan dajin, fulanin cikin Jejine,anan Suke rayuwarsu da ya ransu basu da wasu kaya sai na jikinsu,haka abincin su shine ganye sai fa fura da Suke yi da kansu,basa fita cikin wannan dajin sai bayan wata tara sanan sufita cikin wani k'aramin k'auye wanda tafiyar zata d'aukesu kusan kwana bakwai ga masu jakuna kenan, ga wad'anda ba suda jakunan sai shanu bama sukaiwa sai sunkusa kwana goma, saboda shanun basa jurar wahalar da jakuna Suke jura,sai Su mutu kafin Suje,idan ak'afa zaka yunwa da kishirwa da wahala ga rana Su zasuyi ajalinka Kankaje,don masu zuwa k'asa sai masu Nisan kwana gaskiya.

Abunda kuma yake kaisu shine siyar da dabbonbinsu su siyo gero da dawa, sai gwanjunan kaya da zasu ringa suturta jikinsu, basu dawowa sai sunyi Wata guda suna tafiya suna yada zango har sai sun tabbatar kwanakin da sukai ya isa duk abunda zai faru yafaru.

kuma ba suyin wannan tafiyar mutun d'aya ko biyu ko uku Aa gaba d'aya su keyin ta, saboda wani iftila,i dake faruwa dasu duk bayan wata taran.

Abunda kuwa ke faruwa bayan wad'anan watannin,akwai mutanen da da dama sun san wannan jejin suna zuwansa ab'oye ne su kashe mutanen da suka tadda sannan sufara hak'ar gold dake wannan wajen,basa barin wajen sai sun gama abunda ya kawo su sau d'aya suka tab'a samun mutane tun daga nan ko baza suje kauyen nan ba to fah da anji jiniyar jirginsu za,afara gudun ceton rai, don bazasu bar kowa ba saboda gudun tonuwar asirin su.

Haka wad'annan bayin Allah Suke rayuwa cikin zullumi da fargaba,yanzu shekara guda kenan basu zoba,duk sai suka samu natsuwa da kwanciyar hankali,tunanin ko sun hakura sun daina zowa.

_"Hanan zuciyata har bawa take, badai wani abun yake faruwa bah,kiyi Mani tsallake inji meke faruwa da ku don Allah karkice mani ana kashe su."tafad'a cikin kermar murya da tsananin jin tsoro._

_Murmushin yak'e nayi Ina Kallonta kafin na sadda kaina nace"zulaiha kenan bazan yi maki tsallake bah, sai na kaiki har kawo Inda na had'u dake."_

_Hawaye suka ziraro mata tace"hanan jinake kamar yanzu abubuwan Suke faruwa, tsoro ya cika zuciyata anya zan iya jure sauraren wannan labarin da nai ma suna *A DUNIYARMU*."_

_"zaki jure tunda har kika jure na baya."sake Jingina nayi da bayana jikin kujerar da nake naci gaba da cewa._

Saida nayi wata hudu ina jinya sai antayar sai an zaunar,bana magana daga uhm sai d'aga Kai har Idan kuwa akazo bani abinci kamar zan mutu haka nakeji Idan zan bud'e bakin saboda jinake idasa ya gewa zaiyyi,amman da na samu sauk'i sai gashi ina ci da kaina sambarutu take ko yaman tafiya,itace ke mani wanka, ta shirya ni mu zauna muyi fira duk da itace K'arfin firar ni daga murmushi sai Eh da Aa.

Cikin wata guda na warke da yake karaya uku na samu ga k'afa guda, sai d'aya ga d'ayar k'afar sai gocewa ga kafad'a ta......bafa karamar jinya nayi bah zulaiha,nasha wuya mai sunan wuya ban tab'a tunanin zan tashi bah Wlh.

Munyi sabo sosai da samb'arutu da mijinta babani,basu tab'a haihuwa ba shiyasa sukeji dani bama su kad'ai ba gaba d'ayan mutan jejin kamar su goyani haka sukeji,nima kuma nasaki jiki dasu na maidasu kamar y'an uwana na jini..........bana kyamatar su komi suka bani cinake tunda harsu sukaci suka rayu to na tabbata nima bazan cutu bah, hakan da Su kagani yayi masu dadi ba kad'an ba don suna ganina nafita daban daga cikinsu bazan iya cin cimar suba........tun bayan dana warke babani yabani jikkata wadda tayi fata fata Amman wannan file yana nan shi kad'ai ya tsira shida wani plash mai d'auke da m card dana d'auki muryar dady kabir shida dady musa suna Wata magana......... Yadda jikkar nayi samb'arutu ta had'a mani ta kaba mai kyau wadda kika ganni da ita ranar had'uwarmu.

Muna Zaune dasu yau bayan mundawo daga yo itace,
Nace ma samb'arutu furar gero nakeso nagaji da ta dawar nan, shine tace to muje na rakata yo itace sai sai tayi mani..........gashi dubu ya fara hakanan naji hankalina yana tashi gabana yana ya waita fad'uwa kasancewar haka nake indai wani tashin hankali na gaba Toni zan nemi natsuwata in rasa tun bayan rasuwar su Abby haka nake.............

Maman Muhsin ce✍🏻

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now