30.

69 6 0
                                    

*A DUNIYARMU*
     written by Mrs bb.

30.

Sunan mahaifinmu Alhaji   shehu,babban mutunne wanda ya tara dukiya mai tarin yawa,mutunne mai mutane mai gaskiya da amana mai faran faran,yadda kaga yaya mahaifin hanan haka mahaifinmu yake,itama mahaifiyarmu haka mace mai karamci da dattko,yaya ne dansu na farko bayan shekara biyar sannan aka haifeni,munyi rayuwa mai kyau nida yaya tare da iyayenmu, wani shakikin abokin baba,alhaji mas,ud sun shaku matuka don tashi mukai muka gansu tare,kwatsam barayi suka shiga gidnshi suka kashesu tare da kwashe duk wasu kadarori da dukiyarsa.

Baba har suma yayi saboda wannan mutuwar,saida yayi jinyar sati biyu kafin daker ya dawo hayyacinsa,dansa guda aka bari shine *musa* baba y ansheshi ya hadamu dashi,haka muka tashi babu wani banbanci tsakaninmu dashi,duk daya iyayenmu suke daukarmu.
Mu duka kasar waje mukai karatunmu tunda ga digree har zuwa marsters,duk wani jin dadin duniya mun sameshi tare da iyayenmu,yaya tsaye yake kanmu kan komi shine komi namu,yana kulawa da tarbiyarmu yadda ya kamata.
Kafin mutuwa tayi mana yankan kauna.............hawaye ya share yana cigaba da cewa.
Hatsarin jirgi sukai wajen dawowa daga ganin likita don mamarmu tana fama da ciwon suger,munga tashin hankali wanan lokacin muduka babu wanda baisha ledojin ruwa ba,saida yaya yayi wata kwance baya cikin hayyacinsa,kafin afara mashi rubutun dan gana cikin yardar Allah ya fara dawowa hayyacinshi............koda akazo rabon gado mukace bawani rabo abar komi wajen yaya,tunda shima business ya karanta yacigaba da juya dukiyar.

Haka ryuwar taci gaba da kasancewa yayinda yaya yayi aure mukuma mun fara aiki,amman duk munsaka shiririta,saboda musa da yafara canza mani halaye,kullum da kalar karatun dazai dorani kai,tun bana dauka har zuciyata ta fara ansar sakonsa,ganin yadda yaya yake facaka da kudi sai nakega ai dukiyarmuce yake ma wannan almubazzarancin,musa yake zugani akan ince mashi araba gadona abani kar ya karar da kudin dandanan,bayan ribarshi ce da yake samu ce yake duk wata hidimarsa idan tataso,saboda ba yan kananan kudi yake samuba.

Haka na murje idona na sameshi akan nifa araba abani kasona nima auren zanyi,yayi mamakina saboda ko maganar nayita ne cikin gadara da nuna cewa nima na girma.
Bai mani musuba washe gari aka nemo lawyer baba akafara kaso,wanda nace banyarda ba harda ribar duk za,a raba,dole yaya yace ayi yadda nakeso haka na tashi da miliyoyin naira,wanda lokacin nikaina tsoro suka bani,yaya yake jaman kunne akan inbisu ahankali,inkuma kashesu hanya maikyau,kar na biyewa rudin duniya da abokai na lalata kudin.
Alokacin gani nake haushi yakeji don na anshi kasona,har nake cewa to ina ruwanka idan ma giya da neman mata nayi dasu.......maganar tayi mashi ciwo sosai amman sai bai nuna maniba,yasamu musa yake ce mashi don Allah ya kula dani,yaringa kwatanta mani akan rayuwa kar in tusa kudin nan gaba in gama masu aiki lokaci guda.
Shi ma bakar magana ya gaya mashi cewa,
To kai yaya ina ruwanka ai yanzu bakada iko da dukiyarsa,kabarshi yyi abunda yaga dama dasu,idan ma kesta masu ashana yyi bakada ikon hanashi,don haka ni bazan wani kwabeshi ba,ai yana d hankali yasan daidai da kuma akasin haka.

Yaya yayi kuka dajin kalaman musa,ya kuma tabbatar da cewar musa yake zugani akan komi,yaya baiyi fushi dani ba,koda yaushe zai kirani yayi mani nasiha amman ban taba dauka ba,idan ya gama kawai zan karkade kunnena nabarshi wajen,tun ma idan ya kirani ina zuwa har musa yace inbar zuwa.
Haka muka taso kudin nan gaba mune sai wa yanmata mota,mune club inyau muna nigeria gobe muna kasar waje,haka musa ya tasoni gaba nafa neman mata babuji babu gani,aikin da muke muka watsar ba mu zuwa,karshe aka koremu donshi musa wata irin sata ya tafka a office dinsu suka korai,tare da bata mashi takaddu.

Yaya yayi kuka kamar ba gobe saboda irin rayuwar da yaga mun saka kanmu ci,duk nasihar da yaya zaimana musa ke hana tayi tasiri acikin zuciyata,cikin shekara guda mun lalata miliyna talatin da biyar da dubu daribiyu...........muka dawo bamuda ko sisi yaya baiyi fushiba,haka shiga yi mana fafutukar sumum wani aikin,saida muka shekara biyu zaune kudin sayan kati sai yaya yabamu,agidanshi inda yagina suke tare da matarsa muka tare,don gidan da muka siya mun saida.

Awannan lokacin musa ya fara yiwa yaya sata babuji babu gani,inajin ciwon yadda musa yake mashi,aman kmar ymun asiri na kasa ganin abun tarayya dashi..........inagani zaiyi mashi satar dubunnan kudi amman banda damar hanawa........kuma ya sani bai taba tankawa ba,hankalin yaya bai kwanta ba saida yasamo mana wani aikin.

Amman saboda musa anriga anbata takaddunsa aikina yafi nashi tsoka........haka muka samu daker da kuma fadan yaya mukai aure rana guda nida musa,kuma komi yaya yayi mana tundaga kan lefe ginin gidanmu da duk abunda ake bukata,alokacin na farajin abunda nake mashi ban kyauta wa,don tausayinsa yake kamani duk irin abunda muke mashi baiyin fushi,tsaye yake kanmu.
Amman tarayyata da musa ta hana nadawo kamar da nida dan uwana,balaifi mun dan natsu sabanin kafin aure saidai kuma nasamu mata wadda itada musa kusan halinsu guda,don kullim shawara take ban akan yadda Zan mallake dukiyar yaya,gefe guda ma musa ya tasoni gaba akan haka hankalina ya tashi,jin yadda musa ke tsara yadda zamu kassara yaya,karon farko da nanuna ma musa bacin raina mukai fata fata dashi........wanda har aka haifeka bamu tare dashi,saida muka shekara bakwai bamu tare,har saida  aka haifi hanan bansan sanda muka shiryaba,nidai na wayi gari naga alkarmu tama fita da can,banda abokin shawara sai musa komi zanyi sai musa yaji,karshe na farajin wata guguwar tsanar yaya,banda abund nakeso illah inga bayansa.
KO ganinsa bansonyi burina in ga karshenshi in kuma mallake dukiyarsa ko iyalinsa bana son gani,tun hanan na yar mitsitsiya muka ta tsanemu, saboda duk sanda mukaje wajenshi don yi mashi barazana yarinyar nan tana labe tana ji,shiyasa kullum burinmu  muga suduka babusu adoran kasa.

Haka ryuwar tacigaba da tafiya har aka haifi atu da ilham,da islam musa kuwa yama kasa zama da mace guda,akallah yayi aure yafi goma kuma kowace saita haihu,shiyasa gasunan yaran zube babu tarbiyya babu arabi babu boko,don danshi na farko kasheshi yyi saboda yace baison haihuwa kuma matar tasamu ciki ta haihun,da yanzu yakusa kaika.

Kwatsam saiga Alhaji kallah aminin yayanmu yashigo cikinmu.

Mom muhsen ce

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now