*A DUNIYARMU.*
Written by mrs bb
Mom muhseen.43&44.
Duk halin da ake ciki ya kwashe ya sanar wa Asim,tare da sake sanar dashi abunda yafaru yanzu shida hanan din.
Cigaba yai da cewa"wallahi banyi niyyar hutting dintaba itace ta tun zurani,akanme zata ringa furta kallamar so ga wani katon banza wanda nine nacancanta da ita,ayau nayi niyyar fara bayyana mata abun danakeji akanta,amman shine zata kuntata zuciyata saboda shi.
Bacin bakina da nashi yace mun inhar inason ta wallahi yabarmun saboda ahalin yanzu,bazai iya auren hanan ba saboda ganin cewar kawarta yake aure,zai so taje inda zata samu farinciki hakanma ya isheshi."Kallonsa asim yake yana sake danne dariyarsa don ida yace zaiyita yanzu tofa fada zasuyi,duk wani haushinsa kanshi zai juye mashi shi.
Yadan yi gyaran murya yace,"Aboki baka kyauta ba,duk abunda ta fada wanda yafi wanda tace bai dace kafurta kalamin da kayi mata ba,ai ko wani kaji yana gayamata irin haka sai inda karfinka ya kare,to balle ace kai dakanka ka yi mata haka,taya bazataji zafinkaba karinga controlling temper naka idan ranka yab'aci."
"Naji nayi badaidai ba pls taya zan samu ta sauko,zuciyata bazata jure fushinta ba wallahi nasan bazata sake kulaniba,pls Aboki bazan jureba inasonta Ina son Hanan,itace muradina itace mafarkina in ban sameta ba bazan taba samun natsuwaba."
Wannan lokacin duk yadda yaso danne dariyarsa kasa wa yayi,
Saida ta fito yadunga yi yana rike cikinsa,Kallonsa kurun yake cike da tarin haushi,
"Sorry Abokina wallahi kaban dariya,kaine fa kake cewa Kai ba kayin soyayya,daka ga yarinya kawai zaka fada ayi auren kurun awuce wurin,amman kaine yanzu duk ka fita hayyacinka kan so."Cikin shan mur yace"Asim banson iskanci,taya ina neman yadda zaka shawo man matsala amman kana man shine kake dariya,plsss solution nake nema."
"Shikenan Aboki tashi zakai muje wajenta don saika sauke girman kanka ka bayar da hkr gaskiyar magana."
"Nidai inhar zata hkr wlh zan bata,ahaka suka shiga wajen mama don ya gaidata.
*********
Bilal ne ya kawo Amnah har cikin gidan yashigo,yagaida su iya da baba.
hira muka hauyi sosai,muna dariya daga yadda ya ke yawan kallon mariya nasan cewa bilal ya kamu,ban dai ce mashi komiba har kusan tara na dare sannan suka tafi.KO minti goma basuyi da tafiyaba saiga Su Asim sunyi sallama,
YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...