page 20to28

162 7 0
                                    

[4/15, 9:25 PM] Mom Muhsen: *A DUNIYARMU*
      Written by [Mrs bb]

21.

Hawayen da yake rik'ewa suka shatato masa, ya juya ya shige cikin gidan yabarni nan da jikkar kayana yashe a k'asa,Asim ne ya iso Inda nake Shima kukan yake hawaye duk sun b'ata masa fuska, mutanen unguwa duk sun za ga yemu mun zama abun kallo wajensu, ban hanashi tattara kayan nawa bah ya gama Ya kamani na mik'e yariko hannuna tare da jana har Cikin gidansu, ya direni gaban Mamansu idonsa yayi jajawur,kamar ace nawa tambayarmu take lafiya daker yayi mata bayani saboda ni dai zuciyata wani irin k'una take bazan iya magana bah ahalin da nake ciki............ Kwallah ta goge ta jawoni jikinta tace,
"zulaiha kiyi hakuri kinji ko,kowa da irin kalar kaddararsa to ki d'auka kekuma kalar taki kenan,hakika abun baiyyi kyau ba banji dad'i ba Amman banda wani matakin d'auka tunda iyayenki ne illh iyaka ince kiyi hakuri,kikuma cigaba da yin Addua Allah ya sassauta zuciyarsa ya  kawo karshen lamarin.........zanyi magana da mahaifinku Idan yadawo daga tafiyar da yayiAsim,saboda zamanta anan bada saninsa ba wata fitinarce, kuyita Addua Allah ya dorama akan sa..........Ameen duk mukace................haka nayi ta zama gidan Su bana cikin walwala na shiga damuwar ko awane hali iya ke ciki yanzu,kullum da tunanin ta nake kwana Ina kuma k'arajin tsanar baba na girma cikin zuciyata shida Auwalu,na fara shiga school da taimakon yah asim don shida mama da nasira kullum cikin kwantar mun da hankali suke, ba laifi nad'an samu natsuwa sosai tunda nasan karatu da damuwa ba zasu had'u waje guda bah, sosai na ke fahimtar Duk darasin da ake mana don yawanci munyisu secondary saidan Abunda ba,arasa ba kuma Idan na dawo da dare yah asim yana mana lesson nida nasira,kasancewar Itama BUK d'in take yi.

Rannan iya ta zo gidan nasha kuka kamar idona zaifita, jin bata da lafiya tun ranar da na baro gidan kusan sati Na biyu kenan,taje asibiti ance hawan jini ne da ita tayi ta lallashina tare da cewa incigaba da yiwa baba addua Insha Allah zai sassauto ya nemeni,ta kuma ce na maida hankali sosai nayi karatu don shine babbar nasarar da zanyi........da zata tafi kamar inbita Amman dole nayi hakuri don gudun abunda zai je ya dawo........bayan sati guda dadyn Su ya sauka ranar da Wata irin fargaba na wuni don ina jin tsoron kar yace  bai yarda bah, ranar d'aki na wuni ko makarantar banjeba gudun karna fito ya ganni.............da daddare muna tare da nasira tace ai yanzu daddy yace akira mu nida yah asim...............wani luguden tashin hankali ne yazo ya rufeni jikina har rawa yake,haka muka k'arasa falonsa wanda yake kamar aljannar *duniya* sadda idona ya shigo cikin nasa kad'an ya hana fitsari bai kucce Mani bah,can bakin k'ofar da na shigo  na rakub'e kaina yana k'asa,gabana kamar zai rabe gida biyu............ Bangama tunani naba naji yayi magana Cikin kakkausar murya....... Yace,

"Asim.!"

Batare da ya amsa shi ba ya d'ago yana kallonsa kawai,

"naji duk abunda kuka shirya kaida uwarku,watau ba atashi mani maganar ba sai da ta gama nuna cikin gudana taci tasha acikin gidana, tayi bacci acikin AC da hasken wutar gidana ko? To kun kyauta Nace kun kyauta sosai.............ke kuma kafin nan da minty goma kifice Mani agida, idan kika sake na fito bakibar gidan bah wallahi da karnuka zan had'aki dasu. "

Zunbur nayi na mik'e zan ruga Aguje don da wannan karnukan Su cijeni gara an harbeni da bindiga,saidai me! jinai anyi saurin rik'o mani hannuna Na waigo Asim ne ya taso Ya rik'enk.........idona cike da tashin Hankali nake kallon sa, magana zanyi naji yace,

*"dady,zulaiha ba zata bar gidan nan bah, muddin kuma Kace sai tatafi to saidai mutai tare."*

Cike da mamaki duk falon suke kallon shi, don maganar ta girgizasu har ni kaina saida na razana............fizge hannuna nayi nace cikin kuka tare da durk'ushe wa k'asa,

"Yah na rok'eka kar muyi haka dakai, wallahi Idan kayi haka baka kyauta bah kabarni ni da ba gidanmu bane na tafi, bazan so rayuwarku ta rushe ba ta silata,na hadaka da Allah.............cikin tsawa yace,

A DUNIYAR MUWhere stories live. Discover now