👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
https://www.facebook.com/groups/703796023429534/
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar *LABARINA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
*(Onward together).**Dedicated to my mom, Allah yakara lafiya da nisan kwana me Albarka* Ameen ya Rabbih.🤲
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿1⃣.
Katafaren babban ginin gidan soja me hawa uku, adai dai misalin 11:30pm, na hangi wani kyakkyawan matashin saurayi da baze wuce shekaru 30 ba, fari tas me kyan gaske kallo daya zakayi mishi kagane ba Dan Nigeria bane domin yanayin kirarshi irin mazannan ne masu masu cikar zati da kwarjini ga kyakkawar halitta duk da cikin shigar kayan da suka rufemai jiki yake (jallabiya) behana kaga tsabar alamun karfi a tattare dashiba domin shidin mutum ne mematukar son motsa jiki, fuskar shi tana daukene da kayatattun gashin gira Dana ido masu kyan gani se madaidaitan idanuwa, tareda dogon tsararren hanci, dakuma madaidaitan labba masu launin pink kamar mace, *HAMZA HUSSEIN JALAL KHAN* Kenan yana tsaye a farfajiyar tafkeken gidan tsohon soja Wanda yasha gwagwarmaya a fagen fama Kuma ya taka matsayi daban daban harzuwa mukamin Major General Wanda dagashine yayi retire.
Kana nan duwatsune dauke a hannun Hamza, Wanda kimanin yawansu zasukai guda goma, jefasu yakeyi daya bayan daya tareda nufin sutaba window dakin dake hawa nabiyu, duk jifan dayayi seya taba window Amma shiru babu wani motsin daze iya nuna alamar akwai mutum adakin, cigaba yayi da jifan har seda yayi so 10, yakuma dibar wasu duwatsun ana 11 dinne seyaga an kunna wutar dakin.
Nan take wani irin farinciki ya ziyarci zuciyar shi, sake ware kyawawan idanuwan shi yayi sosai tareda shiga cikin yanayin zumudi da kosawa dasan hango bugun zuciyar shi, can bayan kunna wutar dakin da 2 mins seyaga an bude window dakin, kyakkawar fuskar Nan da yakeson kasancewa da ita har abada itace ta leko da kanta, take zuciyar shi takama bugawa da sauri tana fidda sautin da duk Wanda ke kusa dashi yana iya jiyoshi.
Wacce ke bakin window kuwa kallo daya zaka Mata kafahimci antakura Mata domin dagani baccine a idanuwan ta sosai, sun kankance suyi jawur, hamma tasaki medan tsayi kafin tamishi nuni da hannu alamar ya hauro sama, cikin farinciki da zumudi ya zagaya yabi steps din cikin sanda domin kuwa kofar baya ta dakin ta tana kusa da dakin babantane, Yana zuwa kofar dakin ta bude kiris ya rage suyi karo, ta kauce da sauri ya shiga cikin dakin, daddadan kamshin turarukan wuta datayo tsarabarsu daga inda tadawo daga karatune ya bigi hancinshi, kasa sarrafa kanshi yayi tareda kulle idanuwan shi da Jan dogon numfashi Yana fadin WoW, jinshirun dayayine yasan tabbas tana Nan tana kallon shi, shiyasa yabude idanuwan shi ahankali, hakanne kuwa yakasance idanuwan ta yayi arba dasu tazubamishi tana jiran yagama zumudinshi ta tanbayeshi meyakawoshi da tsakar darennan, ganin irin kallon datakemaine yasa yaki fara magana seya tsaya Yana karemata kallo, farawa yayi da kyakkyawan pink lips dinta Sannan yakoma Kan dogon hanci tsararre me tsawo da burgewa, Sannan yakumayin sama izuwa kyawawan idanuwan ta Dara Dara masu dauke da launin kwaya brown sauran harabar Kuma farare tass, masu janhankalin duk Wanda yabari nashi idanuwan suka hadu dasu, Sannan yakoma Kan gashin kanta, seda taga bashi da niyyar yin abunda yakawoshine ya tsaya yanata karemata kallo kamar yau yafara ganinta, Wanda inda sabo yaci ace yanzu tasaba domin aduk sanda zasu hadu haka yakemata tunsuna makaranta.
Kamar daga sama yaji muryata tana fadin wai Dan Allah Hamza yaushe zakabarni na hutane?, Take yadawo daga duniyar karemata kallo, ya tattaro natsuwarshi Sannan yace, harse sanda kika furtamin cewa kinasona, Kuma kin amince Dani a matsayin masoyinki *Farrah* ya ambaci sunanta Sannan yacigaba dacewa kinsani kece farinciki na kece wacce zuciyata ta Amince da ita kadai, nasani kema kinasona Amma narasa dalilin dayasa kika zabi wahalar Dani memakon Amince wa da soyayya ta Farrah tun muna makaranta kike wahalar Dani narasa me hakan yake nufi agurin ki, cikin yanayin tsananin shauki da bantausayi yake maganar, sannan yayi shiru Yana jiran mezatace Mai.
Cikin tsabar tausayin shi itama ta fada, ciki yanayin idanuwa masu shirin Tara hawaye takalleshi tace, Hamza kayi hakuri bazan iya amsamaka bukatarka ba please kafita kabar dakinnan, cikin yanayin sanyin jiki yajuya zefita sekuma ya juyo yadawo Yana fadin Dan Allah ko Zaki iya fadamin dalilin dayasa kike nunamin irin wannan tsanar afili Amma Kuma yanayin ki Yana kokarin fallasa abunda zuciyar ki take boyewa, Hummmmm Farrah tasaki wani irin gwauron nishi tareda yin magana cikin yanayin damuwa tana fadin Hamza Ina da tanbayoyi ne dayawa gameda Rayuwa ta, wacece Ni sannan kaidinma wayekai, sannan, menene alakarka da mahaifina?, Bayan Nan akwai abubuwan danakeson sani dayawa kafin intabbatar dawa yakamata inyi soyayya kokuma in aura Kuma Wanda nakeso ze yadda ya aureni ayadda nake kokuwa ze gujeni, tafada tana kokarin maida kwallar dake Shirin zubowa daga idanuwan ta.
Tausayin tane yayi matukar Kara kamashi yace gaskiyane kam, nikaina Ina da tanbayoyin dasuke bukatar amsa, Amma matsalar ko munyi magana dake nasa lokacin haduwar mu bakya zuwa sedai kibarni intajira har ingaji.
Kallon shi tayi da idanuwanta datake budesu da kyar sannan tace namaka Alkawarin wannan karon zanzo kodan insamu inhuta da takurarka, murmushi yayi sannan yace muhadu a garden 4:30pm, gyada Kai tayi alamar na Amince, sannan ya yimata sallama yafita.........duk wadannan maganganun dasukayi cikin harshen turanci sukayi domin kuwa duk basajin yaren junansu....................KUBIYONI KUSHA LABARIN WANNAN GIDA ME SUNAN *GIDAN SOJA*......
*Gen Abubakar Umar khamis* me retired, babban tsohon sojane daya taka mukamai kala kala aciki fagen matakai irin na al'adun aikin sojojin Nigeria, Wanda tunbayan dayayi retired yakama harkar kasuwancin itacen tunba Yana fita dasu kasashen waje, Allah subahanahu wata'ala ya dafamai akan Al'amuran shi yasa yakara daukaka Sannan yayi bankwana da talauci haryazuwa yanzu Yana cikin rufin asirin Allah, Yana da Mata daya dakuma yara 5.
maza 2 Mata 3, Ibrahim shine babba ana kiranshida *Khalil* me shakaru 28,
Sena biyu khamis kasancewar sunan mahaifin Megidan ne yasa ake kiranshi da *baba karami*, me shekaru 20,
sekuma Mata babbar mesuna *Farra*, tabiyu mesuna *Nabeela* meshekaru 16.
sekuma auta *Farida*katafaren ginin gidanshi nasama me hawa uku Yana Nan azaune a unguwar *layout, behind governor house of Katsina State*, kayataccen katon gidane cike da masu hidima Wanda komai namore Rayuwa akwai aciki, kowa na gidan Yana cikin farinciki tundaga mamallakin gidan harzuwa kan yara da Yan aikin gidan Amma Banda mutum daya aciki, wannan bakowa bace illa babbar budurwar Yar tsohon General din wacce itace ta farko acikin jerin Yaranshi Mata, me shekaru 24 wacce ke gabda kammala degree dinta nafarko afannin likitanci, ko incema ta kammala sakamako take jira, seta dawo daga kasar India kafin sakamakon yafito, wannan ba wata bace illa *FARRAH ABUBAKAR KHAMIS*.
*Farrah* kyakkyawar yarinya ce, me Kira da launi irin na Larabawa wani lokacin Kuma inka kalleta setayimaka yanayi da mutanen kasar India, farace doguwa, baza'a kirata da siririyaba Kuma baza'a kirata da me kibaba, tana da manyan idanuwa iya dai dai nata, launin kwayar idonta brown ne, me yalwatacce gashin ido Zara zara Dana gira kamar anyi Mata cabin, gashin kanta bakine me laushi da sheki kodayaushe Yana kwance akan gadon bayanta tana kokari sosai gurin gyarashi, sedai Bata sanyin kitso kwata kwata, macece meson saka kana nan Kaya dakuma kayan India sannan Kuma da kallon Fina finansu, shiyasa ma tacema mahaifinta tafison taje tayi karatu acan kasar, Wanda hakan yayima mahaifinnata Dadi dukda dai a burinshi yaso ne ace yasamu magaji, ma'ana Wanda zeyi aikin soja kodakuwa a Yaranshi matane dakuma wani dalilina shi na daban dayaso ace Farrah tazama soja, Amma duk da besamuba yayi farinciki da shawarta nabarin kasa Nigeria kodan tasamu saukin tsana, kyara, tsangwama datake fuskanta agurin matarshi *Hajiya maimunatu*..........
_kucigaba da bina yanzu aka fara_............✍
*Shamsiya Abdullahi (ummu Dilshad Mrs yahaya)*.....✍
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.