👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to *UMMU SUHAANAR*, Har abada bazan taba mantawa dake ba domin kuwa kinyimin abunda baduk mutum ne ze iya yimin Shiba, Kuma dama wani lokaci haka abun kan kasance Wanda baka taba tinanin cewa masoyinka ne na hakika ba, sekaga Kuma shine, Hausawa sunce *Ba'a sanin maci tuwo se Miya ta kare* wannan haka yake Wanda kwata kwata baka taba zatan ze iya maka Wata alfarma ba sekaga Kuma shiyayi maka, Hummmmm nidai na lura sambatu kawai nakeyi domin narasa dawace kalma zan nunamiki irin farincikin da kika sakani. Dan Allah kiyi hakuri ki karbi kalmar *Godiya* Amma ki hada da maneji, Dan ita dinma gani nake tamiki kadan. Gaskiya na gode Sosai, Allah yabar so, kauna, da Kuma kawace me dauke da zumunci na har abada.
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿5
Har akagama breakfast acikin gidan soja, babu Saifullahi babu labarin shi Yana can Yana ta ramakon baccin da yadauki bashi, wanda ya farashi tun bayan ya tashi da kyar yayi sallah alokacin da gari yagama wayewa, yayi wanka shima da kyar domin kuwa babu abunda yakeji se wani irin mugun bacci daketa dibarshi kamar ya fadi, hakan yasa Yana fitowa daga wanka a memakon ya fito babban fallo domin karya kumallo, sekawai yasa kaya yafada kan katifarshi Wanda ya Lula dashi duniyar mafarkin rayuwar aure dashi da abar kaunarshi Farrah.
a inda *ya ganta azaune awata kayatacciyar babbar kujera irin ta gidan sarauta ta Dora kafarta daya akan daya tareda sakarmai wani irin mayataccen murmushi me matukar Jan hankali, tanayi tana lumshe wadannan kyawawan idanuwan nata tareda tsararrun jerin hakoranta data budesu tana sakarmai wani irin murmushi da yasashi hanzarin, doki, tareda tsananin kosawa da yakarasa inda take, ganin irin halin da taga yayan nata saif ne, yasata mikewa cikin yanayin yauki da yanga irin ta masu aji matakin farko. Ahankali ta daga hannayenta biyu tareda budesu alamar Oyoyo, bakinta na motsawa tana fadin _Zo, taho Hasken Qalbina, Ruhina dakuma gangar jikina............._, jinta ambaci wani sunane a karshen maganar ta yasa yaja ya tsaya ya kasa karasawa inda take, Kara bude kofofin kunnuwanshi yayi tareda Mika dukkanin natsuwar shi Yana kokarin fuskantar me Farrah ke fadi haka? Shin Wai dama ba dashi aka daura musu aure bane? Amma yaji ta ambaci wani sunan. Tsayawar shi da dakikun da basufi 5 ba seyaji an bangaji kafadarshi anwuce Wanda yayi sanadin juyawar gangar jikin shi izuwa barin fuskantar inda Farrah din take, muryar dayaji na fadin _Gani nazo, farincikin Qalbina Ruhina dakuma gangar jikina, har abada muna tare babu abunda ze rabamu, se Wanda ya hadamu wato mahaliccin zukatanmu, gangar jikinmu dakuma dukkan komai kenan_, yasa yayi saurin waigawa tareda San tabbatar ma kanshi dagaskene abunda yakeji kokuwa dai kunnuwanshi ne ke yaudararshi, Tsananin tashin hankali ya shiga dayaga _Farrah da Hamza_ na kokarin rungumar jikin juna......yasa shi sakin Wata irin Kara me karfin gaske tareda fadin, _A'a Farrah karkiyi haka please zaki aikata haramun nine mijinki zabin mahaifinki Kuma Dan uwanki na jini, wannan ba mijinki bane babu aure tsananin ku, karki aikata hakan Dan Allah_, ganin ko saurarar shi basuyi bane yasa ya Kara sakin Kara me karfi Yana fadin _Noooooooooooooooooooo_*.
Firgigit ya tashi daga baccin dayake tareda shiga tsananin tashin hankali, Yana bude ido Kuma wani irin mugun firgita yayi sakamakon ido hudu dayayi da lantana wacce ta Dade tana karemai kallo tareda ayyanawa a ranta dama Saifullahi yazama nata mallakin, mijinta Kuma uban yayanta, wannan tunanin ne yasa duk irin ihunda Saifullahi din yakeyi amafarkin shi ko kadan batajiba.
Da zata samu Saifullahi a matsayin miji da tafi kowa farinciki domin Sosai take jinshi aranta tun bayan da Inna lami ta kawota gidan, shi tafara gani amazan gidan bayan taga baba megadi, tunda ta hada ido dashi tafarajin kamar dama an haliccetane domin Saifullahi, Amma ta rasa meyasa kwata kwata ko kallonta bayayi, kuma a kauyensu har fada maza keyi akanta domin akwai wan wani saurayinta dayace seya kashe kanin Dan kawai ya jashi rakiya tadi gurinta shinefa shima yanuna Yana santa, shine Inna lami ta dakkota ta dawo da itanan Dan gudun masifa a kauyen.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.