EPISODE 19

246 16 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to,     masoyiya barkono uwar yaji (mom fadeel🤪), kuma wallahi sora inji kin zageni ehe😡, yasin me rabani dake sai Allah ko a ranki kika zageni zan gane in kikayi vn.
Kyauta ta musamman zuwa ga Anty meena Abba, kuma ina shaidamiki cewa kema *_SONSO FISABILILLAH_*, dama duk members na official group ɗinmu. Amarya beemad Allah ya sanya Alkairi ya bada zaman lafiya yakuma sa wata 9 mugarzaya minna suna lol😀,,,,,,Allah ya ƙara ɗaukaka Intelligent writters Ass, da dukkan mutanen cikinta..... *Ummu Dilshad dai tace SONSO❤️FISABILILLAH.*

Ga masu buƙatar biyan kuɗin karatun book ɗin *SAINA AURI MIJIN ƳATA(TA CIKINA)*, Kuna iya tuntuɓar waɗannan numbers ɗin 08036542610.....07013872581.

*TUNATARWA*
*(ADDU'OIN TASHI DAGA BACCI)*
haryanzun dai awannan babin muke. Allah ya bamu ikon aikatawa🤲🏻👇
(3)

"الحَمْدُ لله الذِي عَافَانِي في جَسَدِي ورَدَّ عَلَيَّ رُوحِي، وأَذِنَ لي بِذِكْرهِ"
Alhamdu lillahil-lathee AAafanee fee jasadee waradda AAalayya roohee wa-athina lee bithikrih.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya bani lafiya a jikina, kuma ya ya dawo mini da raina, kuma ya bani izinin ambatonsa.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿19

Adaren Ranar dai zuciyar saifullahi cike take fal da farin cikin da yadaɗe rabon da yaji irinsa, dan haka ne ma yana cikin tiƙa rawanshi da sauri ya tsaya ya nufi inda wayar shi take ya ɗauka yayi saving ɗin dukkanin maganganun da sukayi da Farrah waɗanda ya yi recording ɗinsu domin wani ƙudiri nashi.

Acan ɓangaren su Farrah kuwa tunda tabar ɗakin su Hamza bata tsaya ko inaba har saida takai ɗakinsu tana shiga ta maida ƙofa ta rufe tabar Afshan a waje sai buga ƙofar take tana kiranta, amma shiru tayi kamar ma batajinta, ganin hakanne yasa ta ƙyaleta ta ɗaga waya takira Hamza tace mai duk abunda yakeyi yabari yanzu yazo domin akwai matsala, Farrah taje ɗakinku tana faɗama Saifullahi wasu irin maganganu waɗanda sam basu dace dashi ba dakai suka dace Hamza, hakan yayi dai dai da lokacin da Tara ke zaune a gefenshi tana ta ɗaɗɗakar giya tana mishi tayi yace bazai shaba amma sai da ta zuba ta miƙa mai , ko asannan Tara na riƙe da cup ɗin tana kara mai a fuska ɗaga mata hannu kawai yayi alamar dakatarwa sannan ya kara akunne jin abunda Afshan ɗin ke faɗi gameda Farrah ne yasa cikin tashin hankali da damuwa baima san sanda ya bige cup ɗin ya faɗi ƙasa ya fashe ba, ya miƙe da sauri ya ɗauki key ɗin motar shi ya wuce ya barta anan da sauran ƴan ƙungiyar.

wani irin ƙululun baƙin cikine taji ya tokareta dan haka kawai itama sai ta ɗauki nata key ɗin motar ta bishi abaya, yana sha rara uban gudu akan titi gabaɗaya hankalin shi yayi gida dan hakane sam baima lura tana binshiba.

Tana tafiya tana sanbatu da zage zage tana faɗin *"Hamza nizaka wulaƙanta  ina baka abu ko kallo na bakayiba harka bigemin hannu katafi babu ko wai waiye, yauniko sai na ga abunda yasa kamin wannan rashin mutumcin"*.

ganin ya tsaya a ƙofar wani ƙayataccen gidane yasa tayi parking daga baya baya, dan karya ganta, tana kallo yayi horn aka buɗe ya shige aka maida get aka rufe, mamaki ne yayi matuƙar kamata tanata saƙe saƙe aranta da tanbayar kanta shin wai dama nan ne gidansu Hamza kokuwa dai wani gidane yazo, ganin batada amsar tanbayartane kawai saita sakko daga motar ta nufi get ɗin gidan aƙafa, ta ƙwanƙwansa har so uku amma babu ko motsi hakan yasa ta dinga bugawa da ƙarfi. da gudu me gadi ya ƙaraso bakin get ɗin bai buɗeba yace waye?

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now