👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to Janafty (My), Ina Miki jinjina ga yadda kike karbar mutane hannu bibbiyu babu nuna banbanci kowa nakine, wannan shine sirrin kara daukakarki aduniyar rubutu dama al'amuranki na yau da kullum, duk mutumin da bashida kyashi ko hassada haka yake cigaba arayuwa, wallahi kina burgeni sosai kuma irin halinnan naki nima inanan ina kokarin kwaikwayonki ne in gani ko zan iya kamo koda kafarkine, kedin ta dabance agurina bazan taba mantawa dake tareda irin gudunmawar da kika bani, kuma kike kan bani ba, Allahu subhanahu wata'ala yabarmu tare, SANSO FISABILILLAHI.💓.
Wannan page din nakine kiyi yadda kikaga dama dashi mallakinki ne.*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿4
Dakatar da Haj maimunatu Gen yayi ta hanyar daga mata hannu tareda fadin malama rufemana baki kinjiko, tabe baki tayi sannan taja baya tana tana kunkunai tareda sauraron me ze biyo baya, tunbayan da tasha matsa agurin Gen tadena yimai tsawa inyana magana sabanin da dataraina shi yanzu abun da sauki.
Gen ya juyo da dubanshi zuwa ga saifullahi, yace saifullahi inaso kafin kayi magana akodayaushe kazamo me gaskiya, tabbatarwa, kuma tsakaninka da Allah acikin lamuranka da kuma dukkan kalmarda zata fito daga bakinka, kuma inaso kasani matsayinka acikin raina dai dai yake dana ƙanwarka Farrah, kuma karka kuskura ka biyema wannan matar....yafada yana nuna Haj maimunatu, sannan yacigaba da cewa duk da dai nasan ba halinka bane kuma banaso kafara daga yanzu, inaso ka faɗamin abunda kakeson cewa. saifullahi ya dago ya kalli Gen sannan ya maida kanshi kasa yana tunanin shin anya, ya cancanta yafadama Gen abunda yaji kuwa? wata zuciyar tacemishi eh, watakuma tace mishi A'a, amma da yatuna yana gabda rasa farrah muddin yabari Gen ya fuskanci akwai wata alakar soyayya a tsakanin Hamza da farrah, yasani kadanne daga aikin Gen daga ranar da yasani yana iya tara mutane washe gari a daura musu aure, tuna haka yasa yace inah! kawai seya bi shawarar zuciyarshi me cemai yafada kawai.
Maganar da Gen yamaine ya dawo dashi daga duniyar kokwanton daya shiga, yana fadin saifullahi ina tanbayarka kayi shiru me kakeson fada ne?.
Sosa keya yayi tareda dago kai ya kalli Gen sannan ya sauke kanshi kasa yana fadin dama nazo wucewa ne ta dakin farrah shine najiyo muryar Hamza a dakin kuma yana fadamata wasu irin maganganu wanda mijine kawai ya cancanta yafadama matarshi irinsu, kallon shi Gen yayi sannan yace Saifullahi ka tabbata da cewa muryar Hamza kaji? gyaɗa kai yayi alamar eh, OK to muje ɗakin Farrah din aduba mugani, tsabar mamaki yakama saifullahi da Haj maimunatu dan a tunanin su dasuka faɗa mai ze fara faɗane tareda ƙwalama hamza kira to amma se sukaga ko ajikinshi kuma be girgizaba dayaji zancennasu.
Shiga gaba Gen yayi sukuma suna biye dashi abaya cikin rashin ƙwarinjiki, suna isa ƙofar dakin suka hangi wutar ɗakin akashe, wai gowa Gen yayi sannan yacema saifullahi, kai kana ganinma za'a iya samun farrah batayi bacciba ballantana ma har asamu wani a ɗakinta? gyaɗa kai Saifullahi yayi alamar eh, duk da dai tun kafin abuɗe ƙofar ɗakin yaji jikinshi yayi sanyi, take yafara daya sani da beyi hakaba. jin bugun ƙofar da Gen yayine ya dawo da saifullahi daga tuna nin shi.
Seda suka buga kusan so biyar sannan sukaga an kunna wutar ɗakin sannan akazo kusa da ƙofar ana faɗin waye? muryar Farrah sukajiyo da alama ma baccine a idonta.
Gen ne ya ɗaga murya yana faɗin ƴar Dady nine kibuɗe ƙofar, toh Dady farrah tafaɗa tareda buɗe ƙofar ɗakin. da ƙyar take buɗe idon ta tana mayarwa ahankali tanagama fahimtar ba Gen ne kaɗai agurinba, se tayi sauri ta buɗe idon gaba ɗaya tana faɗi, a'a Dady lafiya dai ko tareda sakin wata irin doguwar Hamma irinta masujin bacci, naganku anan? kafin Gen ya buɗe baki yayi magana Haj maimunatu ta yi saurin karbe maganar tana faɗin, _"Eh ai dole kiyi kamar kina bacci tunda kin rainama mutane hankali, ko anfaɗamiki bamusan kin ɓoye gardi aɗaki bane"._ jitayi gabanta yayi mummunan faɗuwa, take tafara tunanin me yasa Haj maimunatu faɗin hakan, muryar Dadyn tace tadawo da ita, da yake yima Haj maimunatu tsawa yana faɗin, keh! mlma ki rufe mana baki kuma kibar nan gurin kafin in saɓa miki wallahi, wai ke dan Allah yaushe zakiyi hankaline? samun saukina ɗaya Alhamdulillah duk a ƴaƴan da kika haifa babu me hali irinnaki. komawa gefe tayi amma taƙi tabar gurin duk da faɗan da Gen ɗin yamata.
Itakuma Farrah kasa magana tayi domin batasan ma me zata faɗa ba, kawai se dabarar yin hawaye ya faɗo mata saboda muddin Gen yaga hawaye a idonta to fa babu wani binciken kirki da zeyi ze kashe maganar, nan take kuwa se idanuwanta suka cika da kwalla, ta dago kanta tana kallon Gen tana faɗin "Dady dan Allah me kukeson faɗaminne, kuna nufin tarbiyyar da kukayimin kenan ta tashi abanza, kuna nufin ni zan iya kawo wani cikin gidannan har inkaishi ɗakina kenan? haba Dady kuma haddakai aka yarda da zanyi hakan?" ganin hawaye a idon Farrah yasa daga Saifullahi har Gen hankalin su yayi mummunan tashi, nanfa Gen yashiga rarrashi yana faɗin, ba haka bane ƴar Dady ba zarginki mukeyiba dama yayanki saif ne yace yazo wucewa seyaji muryar Hamza a ɗakinki shine fa memakon yazo ya faɗamin shine yaje ya faɗama mamanshi itakuma kinsanta indai harna kuskura na ƙyale maganar batareda na kashe maganar ta hanyar tabbatar da gaskiyar ido da ido taganiba seya zama abunda zata tara ƴaƴanta tana faɗa musu cewa kinyi abu mara kyau kuma na ƙyaleki, kuma kinsan tun basa yadda wata rana suna iya yadda da ita cewa nafisonki akansu, tunda mahaifiyarsu, fitoma ki ganta gatacan na koreta amma taƙi tafiya setaga komai da idonta yafaɗa tareda nuni da hannu adai dai gurin da take jingine tana zare ido.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.