EPISODE 27

244 19 1
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to, *Uwani koko 😅 to dai gashinan nayi muku page 27 ɗin sabo dake kawai nayi typing badan ke ba bazanyi ba cos karancewa kawai sukeyi suyi shiru ba comments ba godiya ba liking, daga wannan ma sai nayi sati 3 kafin kuji update indai baku gyara ba, wallahi sam bamajin daɗin mu kashe abubuwan mu masu muhimmanci muyi typing ku karanta kuyi shiru hakan yakan nuna mana kamar abunda muke muku bashida muhimmanci agurinku hakan na ɗaya daga cikin dalilan da suka hanani ƙarasa muku book ɗin SAINA AURI MIJIN ƳATA (TA CIKINA), dan Allah ku gyara mudaku ai anzama ɗaya inba hakaba za'a wayi gari gabaɗaya andena Online Writting.*

*TUNATARWA*
*(Zikiri yayin fara Alwala)*.

*بِسْمِ اللهِ.*                                  Bismi l-lahi

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿27

Itadai shiru tayi tana jin bugun zuciyarshi tana bugawa normal babu wani alamar dake nuna cewa yaji tsoro da zuwan ƴan sandan, mamakine yayi matuƙar kamata domin kuwa a iya sanin da tayima Hamza yana tsananin tsoron bindiga dama duk wani abu dazai taɓa ko cutar da jikin shi.

gane hakan ne yasa ta ƙwace jikinta daga nashi da sauri tana faɗin to ai ba wani abu dan ƴan sanda sunzo wata ƙila Daddy nane ya turosu dan mu koma gida kaga in mun koma sai in faɗamai kawai ba yaya saif nakeso ba kai nakeso.

A'a Farrah bazan bari waɗannan mutanen suzo su kamamu ba dan gaskiya za'a iya samun matsala, saboda ina tuna nin su kunal ko Samantha ne suka yimana cinne kuma kinga bansan me suka faɗa musu ba, dan haka kawai sai ya ja hannunta suka shige bedroom ɗin da aka sakata.

da sauri ya ɗakko jakar da diary ɗinta ke ciki yazo tsakiyar ɗakin dai dai inda center carpet yake ya ɗaga saiga wani murfin ƙarfe mai nauyin gaske agurin a rufe, da sauri ya buɗe yajata suka shige.

irin ginin nanne na underground building, bayan shigarsu sai ya danna wani madanni nan take carpet ɗin yakoma yadda yake kamar ba'a ɗagashi ba.

kan ladder suka hau suna sauka ahankali, suna gama sauka saiya nufi wani bango ya lalauba ya danna wani madanni nan take haske ya haskaka ko ina wata hanyace samɓal miƙaƙƙiya kamar ba aƙarƙashin ƙasa take ba, suka fara tafiya babu alamar motsin komai.

sai da sukayi tafiya mai tsawo sannan taga wata ƙofa a ɓangaren hannunsu na dama.

budewa yayi suka shiga, nan ma wani ƙayataccen falo tagani me ɗauke da ɗakuna guda huɗu kowanne da bayi sai kuma kitchen guda uku.

mamakine ƙara kamata kasa cewa komai tayi bin shi da kallo kawai takeyi yayin da zuciyarta taketa ƙara tabbatar mata da cewa wannan ba hamza bane dan sam bahaka Hamza yake tafi da komai nashi ba amma koma waye ya karanci Hamza kokuma ya ɗan jima tare dashi shiyasa ya san abubuwa da dama gameda shi.

kuma dai ba acikin su kunal bane dan kunal yadda bashi da mutumcin nan bazai taɓa yadda wani daga cikinsu yasashi wannan aiki kuma yayi ba daga cikin su kuwa harda Hamzan dan koda yaushe kunal ɗin yana nuna yana saman kowa ne, tabbas wannan wani ne daban, to kowaye Oho.

tana cikin yanayin tunanin ne taji ya taɓata tareda faɗin Farrah kizauna mana, ko dai tsoranne haryanzu bai sakeki ba, karki damu yanzu mun tsira daga sharrin ƴan sanda basu ba ko Aljanine bai isa ya gano inda mukeba.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now