EPISODE 29

239 15 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to Ɗan uwa NAZEEFI YARIMA, Allahu Akhubar dukkan mai rai mamacine😭😭😭wanda Allah yayima mahaifiyarshi Rasuwa jiya 23/7/2020, ina miƙa ta'aziyyata tareda Addu'ar Allahu Subhanahu wata'ala ya jiƙanta ya gafarta mata yasa ta huta yasa Aljannattul Firdausi yazama itace makomarta, sukuma waɗanda tabari Allah yabasu haƙurin rashi ubangiji ya duba maraicin su ya dafama musu dan tsarkin mulki da jalala irin tasa🤲🏻, Ameen ya Rabbih😭.

*TUNATARWA*
*(Zikiri Yayin Fita Daga Gida)*

*بِسْمِ اللهِ ، تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللهِ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ.*
Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah.
Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.

*اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ أَنْ أَضِـلَّ أَوْ أُضَـلَّ ، أَوْ أَزِلَّ أَوْ أُزَلَّ ،  أَوْ أَظْلِـمَ أَوْ أَُظْلَـمَ ، أَوْ أَجْهَلَ أَوْ يُـجْهَلَ عَلَـيّ.*
Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿29

Kai amma in yarinyar nan taga fuskarnan tabbas tawa ta ƙare kamata yayi innemi mafita tun kafin kashina ya bushe, ya faɗa afili kafin daga baya ya dawo ya cigaba da buga ƙofar yanata ihu da sambatu dan tazo ta buɗe mishi ƙofa, amma shiru babu ita babu alamar ta, sosai hankalin shi ya tashi dan kuwa ya tabbata indai da Farrah ta fita daga gidannan da yanzu andawo da ita kuma an buɗeshi to amma meke faruwa kenan me yarinyar nan take ƙoƙarin aikatawa ne, yanzu gashi tsawon awa 2 kenan ko motsinta baijiba.

yayin da DD yake banɗaki  ita kuma Farrah tun bayan da takira wayar nan sai kawai tashiga duba jakarta amma sam  bata ganiba, sai daga ƙarshe ta shiga store room aikuwa nan ma dai bata ganiba taci nema sosai harta gaji.

jiki babu ƙwari ta juya zata fita kenan sai ta hango wani abu a lulluɓe da farin ƙyalle cikin sauri ta matsa kusa dashi ta yaye lulluɓin, wani ƙaramin akwatin katako tagani an garƙameshi da ɗan madai daicin kwaɗo taja taja amma yaƙi buɗuwa, sosai kanta ya ɗaure dan tama rasa mai zatayi tana cikin wannan yanayinne sai wata dabara tazo mata, kawai sai ta bar store room ɗin ta koma ɗakin da DD yake.

tana shiga yaji motsinta nanko ya fara ƙwala mata kira wai shi yana so yayi mata wayo cikin sanyin murya yafara mata magana yana faɗin "Farrah dan Allah ki matso kusa da ƙofar nan kiji abunda zan faɗa miki wallahi bani da niyyar cutar dake, nasan izuwa yanzu dai kin gama sanin komai game dani inma kuma baki sani ba zan faɗa miki komai domin kawai in nunamiki cewa ni mai ƙaunarki ne kuma ban kawo ki nan dan incutar dake bane "

matsowa tayi tareda ƙoƙarin tsinkayen muryarwa takeji haka domin cire fuskar dayayi ya bayyanar da asalin muryarshi, sosai zuciyarta ke ƙoƙarin tunowa da tabbatar mata da cewa tasan mai muryar amma sai dai kash sam ta kasa tinawa, ganin cewa ba sanin koshi waye ne ke gabanta ba yasa ta matso ta tsaya dab da ƙofar  tace "ina jinka me kakeson faɗa?"

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now