👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to All my Fans Love you😘
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿6️⃣
Kara kallon Hamza da Farrah tayi ta tabe Baki tana fadin kufa nake jira, kubani hanya zan wuce inkun gama iskancin, dawannan kallon nawa da kuka tsayayi dama hanya kuka bani nawuce Dan wallahi yin fuskar tausayi bashine ze hanani fadama Gen abunda nagani, kodayake ma ai ba yadda Dani zeyiba Bari inkirawo shedu. Hamza da Farrah najin haka suka Mike tsaye, suna jiran hukuncin da Haj maimunatu zata yanke, se sukaga ta sauka kasa, tana wucewa Farrah takalli Hamza tace kagani ko duk Kaine kajama wannan cin mutuncin da kazafi daga bakin Haj, Ni tashi muje inyimaka dressing din kafarka.
Hakanan Hamza yashiga gaba Farrah na binshi abaya harsuma suka sakko suka nufi dakin Hamza, itakuwa Haj maimunatu tattaro ma aikatan gidan tayi Wai suzo suga abunda Hamza da Farrah sukeyi, Koda sukazo se sukaga babu kowa, nan take tafara kame kame da dai sukaga Bata da abuncewa se suka fara tafiya suna barinta anan a tsaye, ganin hakan ne yasa tafara magana tana fadin tabbas nasan daki suka koma kuzo muje kugani kodai dakin ita Farrah din kokuma dakin Hamza, muna fukan cikin su suka bita wadanda dama ikon da take dashine da yasa suke mata biyayya yanzu sundena tunranar da Gen ya shaketa ire irensune sukayi tafiyarsu Basu bitaba domin sunsan Tsabar tsanar datayinma Farrah ne yasa kullum take neman lefinta.
Haka taja su harzuwa dakin Farrah Amma abun mamaki se sukaga babu kowa, takuma sakko dasu zuwa dakin Hamza nanma babu kowa, A'a ya haka wasu daga cikin suka fara fadi, harara ta sakarmusu tana fadin eh badai sharri namusu ba kuke wani fadin ya haka, duk Wanda zebini yabini Wanda Kuma baze bini ba ya wuce babu Wanda nace dole yazo, nan takama borin kunya kafin daga bisani ta Debi Yan ganin kwakwaf izuwa garden, can suka hangi Farrah a tsugune Hamza Kuma na zaune akan kujera takama kafarshi tana nadeta da bandage, wani irin mamakine yakama kowa dake gurin masu saukin ciki sukafara yima Hamza sannu tareda waigowa suna kallon Haj maimunatu suna tafiya suna barin gurin duk da dai babu Wanda ya isa ya fadamata babu dadi duk da tayi sanyi.
Kama kugu tayi tana tabe Baki tareda fadin, Hummmmm gaskiya Farrah kun iya bariki, wato ke da aka turaki India karatu bariki kikaje Kika koyo ko, duk Dan kar insamu sheda shine Kika shirya wasan kwaikwayon cewa Hamza yaji ciwo, kuci gaba ai akwai ranar kin dillanci. Duk wadannan sambatun da Haj maimunatu keyi Farrah Bata ko kalli inda takeba balle ta kulata, Haka ta kada Kai tawuce tabarsu agurin sunata mata dariya, daganan Hamza da Farrah suka shirya kamar Basu taba yin fadaba suka cigaba da soyewarsu, a garden suka wuni ranar Sallah ce da cin Abinci kawai ke dagasu daga gurin Kuma suna gamawa suke dawowa.
*************
Bangaren Haj maimunatu kuwa tinda tabarsu Hamza zuciyar ta ke mugun tafasa, zuwa tayi ta dauki kayan da tamanta dasu ta koma gidan sunan jiki babu kwari saboda kunyar da taji agurin Yan aikinta ai dama masu iya magana suna cewa *inbaka iya kama barawoba se barawo ya kamaka*.
*Hajiya Karimatu* itace uwar me jego, a inda ta dakko yarta tunkafin ta haihu tace a gidanta zata haihu ayi suna takula da ita sannan ta maida ita dakinta intayi Arba'in. Kuma babbar kawar Haj maimunatu ce wacce kusan halayyarsu daya shiyasa ma abotarsu da amintakarsu take tafiya dai dai Dan itakadaice kawarta ta Rai da Rai tunsuna makaranta.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.