EPISODE 35

200 15 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to, masoyana dake duniya gabaɗaya🙏

*TUNATARWAR*

*(1), Addu'ar Bude Sallah (watau Bayan An yi Kabbarar Harama)*

*اَللَّهُـمَّ باعِـدْ بَيـنِي وَبَيْنَ خَطـايايَ كَما باعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبْ ، اَللَّهُـمَّ نَقِّنِـي مِنْ خَطايايَ كَمـا يُـنَقَّى الثَّـوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسْ ، اَللَّهُـمَّ اغْسِلْنِـي مِنْ خَطَايَـايَ بِالثَّلـجِ وَالمـاءِ وَالْبَرَدْ.*
Allahumma ba'id baynee wabayna khatayaya kama ba'adta baynal-mashriki walmaghrib, allahumma nakkinee min khatayaya kama yunakkath-thawbul-abyadu minad-danas, allahummagh-silnee min khatayaya biththalji walma'i walbarad.

Ya Allah! Ka nisanta tsakanina da laifuffukana kamar yadda Ka nisanta tsakanin gabas da yamma; Ya Allah! Ka tsarkake ni daga laifuffukana kamar yadda ake tsarkake farar tufa daga dauda, Ya Allah! Ka wanke ni daga laifuffukana da kankara da ruwa da raba.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿35

A hankali yake murɗa key ɗin zuciyar shi cike da burin sadaukar da rayuwar shi cikin mamaki ya buɗe idon shi sakamakon buɗewar da yaji yayi lafiya batare da wata matsala ba.

Sai da yayima Allah godiya yafi aƙirga, sannan ya ɗaga faifan a hanakli ƙiri ƙiri yaga wayoyin bomb ɗin sunyi mishi, rasa yadda zai yi yayi can sai ya tuna maganar da Gen yayimai cewa "Hamza aduk lokacin da kazo zaka yi disconnecting ɗin bomb ka lura da cewa wayoyin a waje suke ko aɓoye suke in a bayyane suke to baka da buƙatar wani ƙarfe ko wani abu domin guntile wayar, duba mahaɗa kawai zakayi ka raba wayoyin dake haɗe in kuma a ɓoye suke to anan kana buƙatar a bun taimako, kuma karka manta akoda yaushe waya me launin ja itace positive, me wani kala daban kuma ko baƙi itace nagetive dan haka ka kula sosai kafi maida hankali akan fara zare jarwaya a koda yaushe".

yana tuna hakan da sauri ya kalli cikin ramin da ya buɗe sai yaga jar waya a hankali yasa hannu yana addu'oi tareda tsatstsafowar zufa agoshin shi, har ya samu nasarar cirewa, wani irin tsalle ya daka tare da faɗin *Alhamdulillah.*

agogo kawai ya kalla ya haye mashin ɗin da yazo dashi da sauri, domin ya tuna cewa DDS yace daga ƙofar gidan Raziya KIRANI ROAD zai nufa kuma awa ɗaya ce zata kaishi can sannan bomb ɗin cikin gidan sora mintuna talatin ya tashi, damuwa ya shiga sosai dan haka yasa ya hau titi yanata uban gudu baji ba gani, ga dai iska na kaɗashi amma sai uban zuface ke fita daga jikin shi.

sosai yaji daɗi domin mintuna goma sha biyu ne ya kaishi gidan, ya shiga ya ɗakko screwdriver, touchlight, da kuma player, yana fitowa ya cire key ɗin da ya buɗe gidan ya yar dashi kamar yadda DDS yace yayi.

a komawa ma mintuna goma sha biyu ya ɓata daga KIRANI ROAD zuwa SPINNY ROAD, sai ya rage sora mintuna shida bomb ɗin gidan Raziya ya tashi.

sosai yake a tsorace saboda keys biyu kaɗai ya rage, kuma so ɗaya zai gwada inyafi haka bomb ɗin dake bayan ƙofar gidan zai tashi kuma muddin ya tashi to daga shi har Raziya da ƴaƴanta sunansu gawa, dan haka yasa yataka ahankali zuwa ƙofar gidan bakin shi ɗauke da addu'oi.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now