👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to, Fatima da kuma Ummu mammi dake group ɗinmu na *Our Fans* kuɗin na dabanne a masoyan *Gidan Soja* sosai nakejin daɗin comments ɗinku, inayinku sosai💖 Allah yabar ƙauna.
*TUNATARWA*
*(Addu'ar Sanya Tufafi):*
*الحَمْدُ ِللهِ الَّذِي كَسَانِي هَذَا الثَّوْب ورَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ"*
*Alhamdu lillahil-lazee kasanee hatha aththawb warazakaneehi min ghayri hawlin minnee wala kuwwah.**Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya tufatar da ni wannan (tufa), kuma ya azurta ni da ita, ba tare da wata dabara daga gare ni ba ko wani karfi.*
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿21
Wani irin ƙara Farrah tasaki tana faɗin *Innaah nillahi wa innaah ilaihirraji'un, Hamza ka kalli gabanka*.
da sauri Hamza ya kauda kanshi daga barin kallon Farrah ya ɗora fuskarshi akan titi gani yayai wata babbar mota tana tunkarosu da gudu, irin manyan Tanker ɗinnan nan ne masu jigilar man fetur, da sauri hamza yayi iyayinshi yasamu ya kauce yabi gefen titi, da ƙyar yasamu ya lalubi birkinshi ya taka sukayi wata irin muguwar tsayawar da tajawo kawunan su suka kusa su duki gaban motan sai dukkan ninsu sun saka hannayensu sun tare hakan yasa sai sukayi baya suka daki kujerun da suke zaune.
cikin fushi Hamza ya waigo ya fara mata faɗa yana faɗin *kinganiko, kinga abunda kika jawo mana ko?*
wani irin takaicine ya kamata tareda mamaki, waigowa tayi itama ta kalleshi tace *me kake nufi, nikuma me nayi ninake tuƙi, kokuwa ninace kabar hannunka ka koma hannun masu tahowa?*........
ta buɗe baki kenan zata cigaba da magana sai sukaji hayaniyar mutane suna ta musu sannu, abunka da india komai abun kallone ƙiris suke jira kaga sun taru wani lokacinma agabansu za'a kashe mutum amma babu abunda zasu iya sai dai sutaru kawai suyi kallo sannan in anzo neman sheda suƙi badawa, to yaudai abun da sauƙi tunda su Hamza da aka taru anata musu sannu, hakanne ya hanata cigaba da magana.
bayan mutanen sun watsene, wani wanda dukkan abunda ke faruwa yafarune akan idon shi da yake tsaye motarshi ta lalace yajima yanata tare private cars da taxi amma duk wacce zata wuce da mutum aciki, abunka da pakistan mutum ɗaya ake ɗauka ba kamar ƙasata Nigeria ba da sai ancikata dam kuga daga driver har pasinger da ƙyar suke sahaƙar iska in mutum ɗaya yayi tusa duk motar ake taruwa a kasa a shanye kowa saiya samu😅, nija my country, I love Nigeria and Nigerians.
ganin Allah ya tsarene wannan me babbar motar be buga musu ba, wanda shi tunda yasamu ya kauce ma bai ko tsayaba ya cigaba da tafiya abunshi kuma ma koda ya bige motar tasu ne indai tashi motar batayi komai ba wucewar zaiyi dan bazai tsaya ba.
ganin koda jama'ar suka watse su Farrah basu tada motar sun tafi ba yasa ya fara ƙoƙarin tsallakowa domin yasamu ya ara koda wayar ɗaya daga cikin su ne dan yasamu ya kira me gyara ya duba mai tashi motar wanda bayan tsayawarta ne ya fahimci ashe bai fito da tashi wayar ba.
adai dai wannan lokacin ne sukuma su Farrah keta famar faɗa atsakanin su, Farrah na faɗin *"Haba Hamza wai meyasa gashi ƙiri ƙiri kaine da lefi amma kake ƙoƙarin ɗoramin lefi sannan kuma ka kasa faɗin hujja koda guda ɗaya wacce zata tabbatar da cewa nice na jawo muka kusa samu accident"*......katseta yayi cikin masifa yana faɗin *"saboda Ina Sonki Farrah, amma kika nuna bani kike soba kinma san waye wanda kika zaɓa fiye dani kuwa?, to inbaki sani ba tsaya na faɗa miki kiji saifullahi sam ba sonki yakeba kawai hassada da baƙin ciki yakeyi gameda soyayyar mu dake, kuma ya amince da zai aurekine dan kawai wata buƙata tashi ta daban Far"*........
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.