EPISODE 30

308 15 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to ɗaukacin jama'ar Musulmi aduk inda muke tareda tayamu murnar zagayowar babbar Sallar layya da fatan munyi sallah lafiya, Allahu Subhanahu wata'ala ya nuna mana na baɗin baɗaɗa, ya kuma mana maganin wannan cuta ta corona (Covid-19) dama sauran cututtukan da Al'umma keta fama dashi a faɗin duniya Ameeen, Happy Eid Kabeer acigaba da shagulgulan sallah lafiya🤗.

*TUNATARWA*
*(Zikiri Yayin Shiga Gida).*

*بِسْـمِ اللهِ وَلَجْنَـا، وَبِسْـمِ اللهِ خَـرَجْنَـا، وَعَلَـى رَبِّنَـا تَوَكَّلْـنَا.*
Bismil-lahi walajna, wabismil-lahi kharajna, wa'ala rabbina tawakkalna.

Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita kuma ga Allah kadai, Ubangijinmu, muka dogara.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

🅿30

Suna shigowa Suka koma gefe sukayi cirko cirko sakamakon ganin abunda take aikatawa.

ganinta sukayi tasa surgical blade ɗin ta tsaga tsakiyar tafin hannunta na dama dai dai gurin babban yatsa "inda mukema lalle muna yara muna kiranshi da (cinyar kaza)" , tana yankawa jini ya fara zuba dunƙule hannun tayi jinin na cigaba da ɗiga, kasa cewa komai sukayi duk suka tsaya suna kallon ikon Allah fuskokinsu cike da mamaki.

tana gama yanka nata hannun sai ta nufi inda Hamzan ke kwance ta zauna abakin gado tasa blade ɗin abaki ta riƙeta da haƙoranta sannan ta kama hannun shi na dama ta buɗe tafin ta ɗora shi akan cinyarta, ta cire blade ɗin ta nufi tafin hannunshi da ita da niyyar yimai yanka dai dai da wacce take hannunta......

ihun da suka saki atarene tareda faɗin "karki yanka dan Allah" yasa ta dakata sannan ta waigo ta kallesu cikin takaicin ɓata mata lokacin da sukeyi tace "wai wanda ya kiraku bai faɗamuku nace banaso wani yazo ya dameni ko yayi ƙoƙarin dakatar dani bane? to inbai faɗa muku ba ni bari in faɗamuku, sanin kankune sarai nasan abunda nakeyi domin ni ba mahaukaciya bace kamar yadda naji ya faɗamuku, kuma duk wani wanda zaiso Hamza ya cigaba da rayuwa barinnice daɗin daɗawa nasan dukkan ku kunsan cewa I'm a medical doctor by profession ko? to kune zaku sanar musu cewa dukkansu babu wanda zai iya ceton Hamza acikin su inba niba kawai suna ɓata muku lokacine domin dukkanin waɗannan machines ɗin da wasu ƙwayoyin da suketa ɗuramai sam basu yake buƙataba, wannan yake buƙata.

ta faɗa tareda ɗaga hannun da ta yanka jini yana ɗiga ƙasa ta kalleshi sannan ta waigo ta kalli doctors ɗin ta maida kallonta zuwa ga Ahalinta tace kunganshi ya ɗiga a ƙasa ko? to jini na Hamza yake buƙata batareda wata ƙwaya ko tsinin alluraba, dan haka banaso wani ya kuskura ya ƙara ɓatamin lokaci gurin yunƙurin dakatar dani.

tana gama faɗin haka ta maida hankalin ta zuwa ga cigaba da aikata abun da take da nufin aiwatarwa, harta ɗora blade ɗin akan Hannun Hamza zata danna taja kenan da sauri ɗaya daga cikin doctors ɗin ya ƙarasa kusa da ita ya riƙe mata hannu cikin sanyin ciki da zullumin abunda zatayi kan iya jama Hamzan yafara faɗin "dakata dan Allah, karki yankashi ya zubar da jini sosai kuma da ƙyar akasamu jinin da aka samai duk da hakama inda za'a ƙaramai yanaso to amma munƙi ƙaramaine saboda condition ɗin da heart ɗinshi ke ciki dan ƙiris ya rage harsashin ya taɓa mai zuciya kuma yanzu haka muna ƙoƙarin ganin bai samu internal bleeding ba cos ciwon yana barazanar komawa ɗanyene, sannan jinin da kike ƙoƙarin haɗawa da na Hamza bamu tantance ko zaiyi dai dai danashiba kuma bamuyi miki test ɗin da zai tabbatar da cewa your blood could not conterminated his own blood ba saboda bamu sani ba ko kina ɗauke da wasu ƙwayoyin cutarba".

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now