EPISODE 12

335 20 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to, *Sadiya  Sidiya* tamu ta INTELLIGENT WRITERS, Allah yakara hada kawunan mu Ameen.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿12

*Ina masoyana na gaskiya da gaskiya? Ina me farincikin Sanar daku cewa, _wani Sabon Novel Dina me sunan "SAINA AURI MIJIN ƳATA (TA CIKINA)_, yafara zuwa muku tun ranar 3/3/2020 , a inda zaku nunamin Irin matsayin da nake dashi azukatanku ta hanyar biyan supporting fee 200 kacal, domin ku karanta wannan Labarin kuga irin dunbin fadakarwa, Ilimantarwa, Nishadantarwa da Kuma tarin cakwakiyar dake ciki, Sannan kuga tayaya suruka zata auri mijin ƴar cikin ta, shin ze yiwu ko baze yiwuba, Wai shin mema yasa tace seta aureshine, meye hujjarta, Kuma menene dalilin ta Kuma me take takama dashi????????? Duk dai amsoshin suna Nan acikin book din  *_SAINA AURI MIJIN ƳATA (TA CIKINA)_,*, karku Bari ayi babuku.........

************************
Harya taka corridor din kitchen din da nufin shiga sekuma ya fasa, kawai saiya bar gurin ya fito tsakar gida, direct bakin gate yanufa,  yayi mishi sallama sannan yafara yimai magana da turanci kasancewar dukkanin su basajin yaren junansu, Saifullahi bayajin yaren Urdu shikuma me gadi bayajin hausa.

Dan Allah Ina so ka taimakamin ka yimin kwatancen inda zan samu fure me kyau, kamshi da daukar hankali....... Murmushi yayi sannan yace gaskiya sedai in rakaka domin kuwa me gidan yace kar inkus kura inbari wani ya fita shi kadai saboda bakine ku Kuma gaskiya fita sai Dan Islamabad ne kawai ze iya gane yadda garin yake natabbata Inka fita kana iya bacewa saboda streets din suna kama da juna Kai hatta gine ginanma musamman ma nan *Zone V*, duk Wanda ya kuskura ya siya gida da nufin zama Kuma  Yana bako to kuwa kullum ya fita se an kaishi gidanshi Dan baze ganeba.

Murmushi yayi yace to naji muje ka rakani.

Sukaje ya tayashi zaba, sannan suka wuce wani babban mall dake bakin titin, nanma ya shiga ya kashe kudi Sosai ya ciko Wata Yar karamar leda da kayayyakin lashe lashe na Zaki da sauransu, sannan suka dawo gida, Saifullahi jiyake zuciyar shi kamar an wanke mishi ita, saboda Tsabar farinciki Haka yasa hannu a aljihu ya debo kudi irinna India wato rupees ya damkama me gadi yanata godiya, tareda yima Saifullahi kallon mamaki Wanda ke cike da alamun Tanbayar a Ina ya samu kudi Haka da yawa harya damkamai kimanin kudin da ze Kai Naira 2000 na Nigeria.

Kallo daya Saifullahi yayimai ya fahimci inda yanayin shi ya dosa Dan Haka nema yasa yayi murmushi tareda faɗin karka damu, Dadyn mu General ne ya rabama kowa kimanin 200k kafin mu taho ko zamu iya bukatar wani Abu kaga base mun ta neman kudi bako? Gyada Kai yayi Yana fadin gaskiya ne na gode Sosai.

Saifullahi Yana shiga yaji gida ya cika da kamshi girke girke iri iri, jiyo Yar kamar hayaniya yayi Yana fitowa daga kitchen din Dan Haka kawai seya nufi can, zuciyar shi cike da karfin hali da kwarin gwiwa tareda kokarin kakaro walwala da murmushi ya dorasu akan fuskar shi hannun shi daya dauke da flowers dayakuma dauke da kayan ciye ciye na zakin da suka siyo, seya boye me dauke da flowers din abaya.

Guys! Sannunku da kokari kunsan kamshin girke girken Nan naku yacika unguwar nan? Tundaga Baki gate ake jiyo kamshi gaskiya yau da alama zamu ci me dadi, kamar daga sama suka tsinkayi muryar Saifullahi hakan yasa dukkanin su suka dago kawunansu atare suka dorasu akanshi, shima kallon nasu yayi musamman da idanuwan shi suka sauka akan Hamza da farrah a inda suke tsaye a guri daya agaban wani faffadan  frying pan Farrah tana juya wani faifan gurasar  flour a inda shikuma Hamza yake murzawa Yana Mika Mata cikin farinciki da salon so da kauna suke aiki tare. Wani irin mugun takaicin kishine ya mamaye zuciyar shi, da sauri yafara bama zuciyar shi haƙuri tareda kakaro murmushi ya kauda kanshi ya maida dubanshi izuwa Zoya yace "Anty Zoya kunata aiki gaskiya sannunku, nagode Sosai da kike koyama my wife to be irin Abincin kasarnan kamar kinsan in akayi bikin mu anan zamuyi Honeymoon, gaskiya na gode.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now