👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to, Dukkan masoya littattafaina aduk inda kuke,❤️Anatare🤝🏻
*TUNATARWAR*
*(2), Addu'ar Buɗe Sallah(wato Bayan An yi Kabbarar Harama)**سُبْـحانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْـدِكَ وَتَبارَكَ اسْمُـكَ وَتَعَـالَى جَـدُّكَ وَلا إِلهَ غَيْرُكَ.*
Subhanakal-lahumma wabihamdika watabarakas-muka wata'ala jadduka wala ilaha ghayruk.Tsarki ya tabbata gareKa, Ya Allah, tare da yabo gareka; Albarkatun sunanka sun yawaita; mulkinka da girmanka sun daukaka; babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿36
Akanta suka tsaitsaya Gen ya zauna ya ɗago kanta ya ɗora akan cinyarshi yana ɗan jijjigata yana faɗin "Farrah kitashi ki faɗa mana meyafaru, shiru bata koda motsi ganin hakan yasa Saifullahi fita da sauri ya ɗebo ruwa a buta ya kawo ma Gen ya karɓa yaɗan shafa mata a fuska.
wata irin ajiyar zuciya ta saki me ƙarfi, sannan ta buɗe ido da sauri tareda miƙewa ta zauna ta saki kuka me ƙarfi tana magana "Dady Hamza ya mutu ko?, wallahi banaso ya mutu inaso in rayu dashi kuma ina son sanin tarihina bana so na rayu da kowa sai Hamza inna rasashi nima tabbas za'a rasani Dady inason Hamza, kuma gashi nayi mafarki cewa yana cikin wuta yana miƙomin hannu yana cewa in ceceshi Dady in Hamza ya mutu ya zanyi?"
Rungumo da kanta Gen yayi yana faɗin yi shiru Farrah in sha Allah Hamza zai dawo lafiya na yarda da irin son da yake miki kodan sabo dake nasan bazai bari ya mutu batare da ya mallakeki ba, kuma ai munyi mai addu'oin neman tsari da kariya daga gurin Allah dan haka karki damu kiyi imani da cewa Allah yana tare da Hamza kuma shi kaɗaine zai dawo mana dashi lafiya dan haka ki zama jaruma ki dena zubar da hawaye akan mafarki ai ba kowani mafarkine ke zama gaskiya ba, kawai ki cigaba da yimai addu'a, kinji?"
gyaɗa kai kawai tayi tace to Dady.
duk da faɗin tana son Hamza da takeyi bai hana Saifullahi shiga tsananin tausayin su daga ita har Hamzan ba, sosai yake ƙara tabbatar da cewa So gaskiya ne.
Suna nan a police station har ƙarfe tara da rabi na dare suna jiran tsammani, shiru babu Hamza babu dalilinshi sosai hankalin kowa dake gurin yatashi.
daga masallaci sai suka koma falon station ɗin suna zaune ta bayan kanta, Tv na kunne yanata magana sai aka fara News, suna ɗan kallo suna basarwa domin kowa jikin shi yayi sanyi sosai raban kowannen su da cin Abinci tun da rana Daadaa yasa akayo musu takeaway babu wanda ya ƙara shan koda ruwa ne, yanzu da daddaren ma yaso ya kuma yi to kowa sai yace ya ƙoshi.
*Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un, ayau ɗinnan ne muka samu labarin Fashewar wani abun fashewar da bamu san ko mene ne shiba a unguwar Sabzal dake garin Quetta, wanda ya fashe da misalin ƙarfe shida da rabi na yamma, abun fashewar da yayi sanadiyyar mutuwar mutane Uku' maza biyu mace ɗaya, sai dai babu wanda yasan dalilin fashewar kuma mene ne ya fashe ɗin a inda muka samu bayanai daban daban daga mazauna yankin, wasu sunce tukunyar gas ɗin girki ce wasu kuma sunce bomb ne, to amma koma dai menene har yanzu bamu gano komai ba sai dai jami'an tsaro sun tsinta wani travellin passport me ɗauke da suna kamar haka Hamza Hussein Jalal Khan........*
ana faɗin haka gabaɗaya suka miƙe atare suna salati, Farrah kuwa tunda tace Innah lillahi wa'innah Ilaihirraji'un, sannan ta fasa wata Ƙara tana faɗin ƙaryane Hamza bai mutu ba, kawai sai ta faɗi sumammiya.
gurin ruɗewa yayi da salatin kowanne daga cikin, duk sun ruɗe sunma rasa me ya kamata suyi, Gen ne ya iya yin ƙoƙari ya nufi Office ɗin D.p.o jiki na rawa ya shiga babu ko sallama cikin ruɗewa yace "yallaɓai Hamza ya mutu yanzu muka gani a labarai dan Allah kutaimaka mana muje a yanzu mu duba ko zamuga koda gawarshine dan ance an tsinci travelling passport ɗinshi a gurin, kama Gen D.p.o yayi ya zaunar dashi yace " yallaɓai kayi haƙuri ka kwantar da hankalin ka in sha Allah komai zai wuce zamu duba shi indai yana raye zamu dawo dashi in kuma Allah ya mai rasuwa ma in sha Allah zamu kawo gawarshi har gidanku, yanzu da zan tashi ne ma inbar yara amma yanzu na fasa zan kwashi yaranne mutafi can Quetta ɗin, namaka Alƙawari in sha Allah sai na dawo da Hamza ko gawarshi.
Shiko Hussein jalal tsabar takaici daya kwashe shi bai kaishi ko ina ba sai cell ɗin da aka kulle DDS yana zuwa ya shaƙeshi yana faɗin Azzalumi kaji daɗi ance Hamza ya mutu, wallahi in har ya tabbata cewa ya mutu ɗin kaima saina kasheka da Hannuna, dan bazan jira a yanke maka hukunci ba dan bawani abun arziƙi za'a yankemaka ba da ya wuce zama gidan yari har ƙarshen rayuwarka, to ni kasheka zanyi domin shine hukuncin da yafi dacewa dakai, ya ƙarasa maganar yana kaimai duka, yana cikin wannan yanayinne sai Gen da d.p.o nan sun shigo, da gudu Gen ya ƙarasa ya riƙe Hussein yana faɗin "rabu dashi abokina zomuje, yaja hannunshi suna tafiya shikuma yana wai gowa yana yima DDS kallon takaici, shiko dariya ya saki mai ƙarfi tareda faɗin "kujirani gobe da safe ina nan zuwa gidanku a matsayin Hamza da fuskar shi da komai kuma babu wanda ya isa ya faɗama Farrah niba Hamza bane, domin nasan lokacin idonta arufe yake burinta kawai taganshi dan haka dole ta yadda nine shi, yes Hamza ya tafi Farrah ta zama tawa" sannan ya ƙara fashewa da wata dariyar mai ƙarfi.
sai da suka fito inda Farrah take ne sannan suka tuna da ita, Afshan suka gani akanta tanata rarrashinta bayan ta yayyafa mata ruwa ta farfaɗo duk da dai itama kukan take amma bai hanata rarrashinta ba.
Umarni Gen ya basu na cewa su tashi su tafi gida kawai dan yanzu su D.p.o zasu tafi can dan neman Hamzan, to kawai suka amsa dashi suka miƙe amma banda farrah da ta coge taƙi tafiya wai ita ai tayima Hamza Alƙawarin zata jira shi dan haka ita tana nan ko akawo shi araye kokuma a kawo gawarshi itadai tana nan tana jira.
Daƙyar suka samu suka lallaɓata suka wuce gida.
a gabaɗaya daren dai babu wanda ya iya rintsawa domin kowa hankalin shi a tashe yake .
*Washe gari da safe*
Misalin ƙarfe Takwas da rabi D.p.o da yaran shi suka iso gidan su Hamza amma babu shi babu alamar shi bare kuma gawarshi.
Suna shiga falo kowa ya miƙe tsaye yana ware idanuwa da nufin ganin hamza, D.p.o yana shigowa tsakiyar falo jiki a sanyaye ya cire hula cikin sanyin murya yace"Yallaɓai sai dai haƙuri domin babu irin dubawa da bin ciken da bamuyi ba amma bamu ganshi ba munfi tunanin ko ya ƙonene ya zama toka aciki.
da gudu Farrah ta nufi D.p.o cikin kuka ta dinga dukanshi tana sambatu "ƙarya kake yi baka iya aiki bane inka amince ka bani kakin ka in saka zan iya maye gurbin ka dan kawai in nemo Hamza kuma saina tabbatar maka da cewa Hamza yana raye bai mutu ba, Dady ƙarya yakeyi Hamza yana raye fa bazai mutu ya barni ba, ku ƙyaleni na tafi na nemo shi" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikin Gen da ya ɗauketa daga dukan Dpo da takeyi, zaunar da ita yayi yanata rarrashinta.
kowa ya koma ya zauna ba tare da ya ƙara cewa komai ba sai sautin koke koke ne kawai ke tashi.
Suna cikin wannan yanayinne sai sukaji Sallamar Hamza kanshi naɗe da Bandage ya shigo yana ɗin gishi yana tafiya da ƙyar, ganin shi da sukayi yasa kowa dage kuka yayi shiru ya kafama ƙofar da yake tsaye ido suna kallon ikon Allah.
Da gudu kowa ya nufeshi da niyyar rungumeshi Farrah ce agaba wacce tafi kowa farin ciki sai dai kafin su ƙarasa gurin Hussein Jalal ya ɗaga murya yace D.p.o karka barsu su ƙarasa domin wannan ba Hamza bane, sunajin haka suka tsaya cak babu wanda ya ƙara koda taku ɗayane sai ma juyowa da sukayi fuskoki cike da mamaki da nufin yima Hussein jalal tanbayoyin hujjar shi......
*SHAMSIYA ABDULLAHI (UMMU DILSHAD MRS YAHAYA)......✍️*
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.