SECOND TO THE LAST, EPSD 43

384 22 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to, dukkan masu karanta wannan littafi na gidan soja, ina godiya sosai sannan ina mai farincikin sanar daku cewa in sha Allah wannan littafin ina sa ran in dai har Allah ya bani iko da dama zan gama muku shi a next page, sannan ga wani albishir na musamman ga waɗan da basu samu damar karantashi ba kuma suna so to ga wata dama ta musamman da zarar na gama shi in sha Allah zai fara zuwa muku a matsayin na saurare wato Audio a inda zan dinga yaɗa muku link ɗin kowani page kuna ziyarta youtube channel ɗin da zaku dinga saurarar shi tun daga farko har ƙarshe in sha Allah, sannan nace kusha karatu lafiya domin wannan shafin yafi kowani shafi tsawo.🤝🏻

*TUNATARWA*
*(Addu'ar Dagowa daga Ruku'u)*

*سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ.*
Sami'al-lahu liman hamidah

Allah Ya ji wanda ya gode masa.

*رَبَّنـا وَلَكَ الحَمْـدُ حَمْداً كَثِيراً طَيِّـباً مُـبَارَكاً فِيهِ.*
Rabbana walakal-hamdu hamdan katheeran tayyiban mubarakan feeh.

Ya Ubangijinmu! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sawa albarka a cikinsa.

*مِلْءَ السَّمَوَاتِ وَمِلْءَ الأَرْضِ، وَمَا بَيْنَهُمَا، وَمِلْءَ مَا شِئْتَ مِنْ شَيءٍ بَعْدُ. أَهْلَ الثَّنَاءِ وَالْمَجْدِ، أََحَقُّ مَا قَالَ العَبْدُ، وَكُلُّنَا لَكَ عَبْدُ. اَللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَـيْتُ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ.*
Mil-as-samawati wamil-al-ard, wama baynahuma, wamil'a ma shi'ta min shay-in ba'd, ahlath-thana-i walmajd, ahakku ma kalal-'abd, wakulluna laka 'abd. Allahumma la mani'a lima a'tayta, wala mu'tiya lima mana'ta, wala yanfa'u zal-jaddi minkal-jaddu.

Ya Ubangiji! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, (yabo) mai Cika sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, mai cika duk wani abu da Ka so bayan haka. Ya wanda ya cancanci yabo da daukaka. (wannan yabo) shi ne mafi cancantar abin da bawa ya fada, kuma dukkanninmu bayi ne gare Ka. Ya Allah! Babu mai hana abin da Ka bayar, kuma babu mai byar da abin da Ka hana, kuma wadata ba ta tsirar da mai wadata daga gare Ka.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

🅿43

Da sauri ta yar da diary ɗin a kangado ta ɗaga kai ta kalli agogo taga har ƙarfe 12:00am na dare yayi ƙara fashewa tayi da wani kukan ta miƙe da sauri takama kici kicin buɗe ƙofa da nufin fita. ƙarar abun da takeyi ne ya tashi abokanan kwanan nata (Afshan da Nabeela) aɗan firgice Afshan ta tashi tana faɗin "Farrah lafiya, meke damun ki kike kuka, kuma ina zaki kike ƙoƙarin buɗe ƙofa? dare fa yayi.

ta ƙarasa maganar tana miƙewa ta ƙarasa inda take ta riƙe mata hannu. da ƙarfi Farrah ta fizge hannu idanuwanta cike da hawaye tace "Afshan ki rabu dani Dady na zanje in tanbayi dalilin dayasa ya cutar da rayuwata, meyasa zaimin haka Afshan Why?

Rashin sanin kan zancen da Afshan batayi bane yasa ta saki baki tana kallon farrah ta fara yin addu'oi tana tofa mata dan aganin ta gamo tayi da tsohon daren nan take faɗin irin abubuwan da take faɗa akan mahaifinta.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now