EPISODE 17

266 21 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to ZM Chubado (My chuchu). Tareda My Soupnassy (Ummu Janan), Tareda miƙa muku gaisuwa da fatan Allah yabaku lafiya dama duk wanda lafiya tayima ƙaranci a gida ko Asibiti, Allahu Subhanahu wata'ala ya kawo mana ƙarshen Covid 19🤲🏻

Haryanzu book ɗin *SAINA AURI MIJIN ƳATA (TA CIKINA)*  Yana nan yana cigaba da zuwa amma a group ɗin waɗanda suka biya 200 ɗin karatu kawai game buƙatar shima a warware ƙullin dashi yana iya yin magana ta 08036542610 kokuma 07013872581 dan yabiya shima ya shiga sahu😁.

*TUNATARWA*
*(ADDU'OIN TASHI DAGA BACCI)*

Alhamdulillah kamar yadda nayi Alƙawari na cigaba da kawo mana addu'oi daga *HUSNIL MUSLIM*, in sha Allah bazanyi ƙasa a gwiwa ba a yau zamu fara da babin  addu'oin bayan  tashi daga bacci.👇

"الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور"
Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi tashi yake.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿17

ROHIT ya fara buɗe ido ahankali kafin ƙwayar idonshi yakai ga kangadon da SONIA take sai yayi sauri ya rufe, domin yana matuƙar tsoron yin ido huɗu da abunda zai iya gani Kunal yana yima abar ƙaunar tashi,  sai dayayi haka kusan so uku sannan  ya lura ashema kunal baya ɗakin ganin haka yasa yayi saurin ƙara ware idanuwan shi yana kallon SONIA dake kwance sumammiya akan gadon jikinta babu kaya daga pant sai bra, hakan ke tabbatar mai da cewa kunal bai mata komai ba wani daɗi yaji ya ratsa shi, da sauri ya rintse ido yana kiran sunan abunda suke bautamawa acikin ranshi yana faɗin "thank you lord Ganesh". cikin daƙiƙun da basufi uku ba yajiyo muryar Kunal ɗin yana faɗin " eh sir yanzu haka kuna gurin kenan, A'a gaskiya mufa sai anbiya tukunna muke samun ƙwarin gwiwar yima mutum aiki indai kunsan babu kuɗi to karma ku fara ɗaukata aiki kawai kunemi wani danni sam bani da mutum ci indai akan kuɗine, Ok to gamunan zuwa yanzu nida yara na, ok bye"

Mummunan faɗuwar gaba ROHIT ya ƙara faɗawa sosai yakejin bugun zuciyar shi afili dajin muryar Kunal da yayi da alama kenan wayar da yakeyine ya hanashi cimma burin shi akan SONIA, ƙara rufe ido ya kuma yi tareda kasa kunne domin jin mai zai faru dayaga Kunal ya ƙara shigowa ɗakin, yana wannan yanayinne yaji an ɗan mari fuskarshi ahankali, da sauri ya buɗe ido, kunal yagani yana mishi dariya tareda kashe mai ido ɗaya yace "tsuntsun soyayya yau Allah ya ceceku kaida masoyiyar ka inada wani uziri yanzu duk da dai ba haka naso ba naso ace na ɗan zuƙi kalan nata zaƙin naji yadda yake, to amma gobe ma kana iya dawo da ita kaji tsuntsun soyayya?" yafaɗa tareda kwance shi ya mishi nuni da SONIA yace jeka ɗauketa kutafi amma gobe kudawo.

Kunal na gama faɗin haka yasa kai ya nufa fallo inda su Hamza ke zaune, shikuwa ROHIT sauri yayi ya maidamata da kaya ko tsayawa baiyi ta farfaɗoba ya sungumeta ya fice da ita daga gidan rawar jiki na rawa yana tafiya yana sambatu yana faɗin nida MARGALLA har bada.

acan fallo kuwa kunal na shiga Tara ta kalle shi ta sakarmai wani irin shu'umin murmushi tareda faɗin kai bro daɗina dakai kasan ɗanɗano wato lolli ɗin yau babu daɗi kenan shiyasa ma ko ɓata lokaci bakayiba gurin tsotse shi kana ɗan lasa da tsinin harshenka ka furzar tareda yin jifa dashi ko? nasan dai da yayi zaƙi da sai kayi awa uku kana ɗibar ɗanɗanonshi ta ƙarasa maganar tana kashe mai ido ɗaya, tana rufe baki sauran ƴan ɗakin suka kwashe da dariya suna faɗin sai Oga, shazumamu kasan zaƙi.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now