👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to, 80k's to all people bearing the name 80k, Ina godiya sosai wacce Bata misaltuwa, kudin Yan halakne Kuma masu San cigaban harshen hausa, sannan dason kawo gyara ga tarbiyyar yaran hausawa, tanx once again🤝🏻 Allah yabar zumunci.
Ban manta dakaiba Nazifi yarima, babban admin Kuma bro, Allah yakarayin temako a kowani al'amura naka damu baki daya, godiya mara adadi🤝🏻.
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿3.
Hamza ya jefo mata tanbaya, shiru tadanyi kafin tace senan da watanni 8 sannan zan cika 25, Kuma gaskiya yayimin nisa inaso insan asalina kodan insamu in huta da irin gorin da Haj maimunatu take min, Tsabar Sabon tausayintane yakara kama Hamza kallonta kawai yakeyi kamar ya fashe da kuka, sundan jima ahaka kafin yace to Amma me ze Hana kikuma tuntubarshi, toh Amma yama kuke da Saifullahi tukunna?, murmushi ne yaso ya kwacema Farrah dajin tanbayar Hamza domin kuwa tasan bawani Abu yasa yayi tanbayar Nan ba daya wuce kishi dayakeyi dashi, wato so yake yaji inda aure a tsakanin su yakara zage damtse gurin yada manufarshi kafin ayimai kwace ko?.
Duk yadda takai ga boye murmushi seda ya bayyana, ga ido cike da hawaye, tace Nima bansaniba, What?!, Me kike nufi da baki saniba, ba Dan uwanku bane?.
Tace Eh Dan uwanmu ne Amma gaskiya bansan cikakken hadinmu dashiba Amma dai nasan Saifullahi jininane saboda naji Dady Yana cewa Dan babban wansune Kuma Dan yayar Haj maimunatu ne, hankalin Hamza yayi matukar tashi dajin zancen Farrah gameda saifullahi, Amma seyayi ta maza yace Farrah meze Hana kisamu Gen kifara tanbayar shi asalin Dan gantakar shida saifullahi indai kika samu yafada Miki ahankali seki tanbayeshi sauran, tanbayoyinnaki Ina ganin kamar sandama ze fadamiki baze saniba.
Ajiyar zuciya Farrah tayi sannan tace toh zan gwadayin hakan.
Wani irin farinciki ne ya ziyarci zukatan masoyan Wanda Kuma a can gefe Kuma kowanne na manne da yar wata fargaba, Hamza tsoro yakeji kar dai Gen yanaso ya hada Farrah Auren zumunci ne da Saifullahi yasa ya rikeshi a gurinshi.
Itakuma tana fargabar kardai akwai wata danganta tsakanin ta Hamza wacce zata iya jawowa su rasa junansu.
Yawan shirune ya ratsa gurin se kukan tsintsaye ne kawai keta tashi tareda kadawar kamshin sanyayyun furannin dake zagaye da harabar gurin dasuke zaune.
Muryar saifullahi ce ta kawar da shirun a inda yake fadin Farrah Gen yadawo Yana kiranki yace begankiba, adan razane dukkanin su suka dago atareda kallon Saifullahi, Farrah ce tafara magana tana fadin Yaya saif yaushe kuka dawo, Bata Rai yayi Yana fadin bamu wuce 10mins da shigowaba, yafada tareda yin kallan kallon dake dauke da tuhumar juna tsakaninshi da Hamza, kafin yajuya yabarsu agurin ranshi Yana Mai zafi.
Cikin natsuwa Farrah tamike tana fadin Hamza nizan shiga ciki, zakazo mujene?, Girgiza Kai yayi alamar A'a, kije kawai zanzo daga baya, ranshi adan bace yayi maganar, harta juya zata wuce asanyaye yakira sunanta tawaigo ta kalleshi suka hada ido irin Wanda babu shiri dukkansu kasa kauda kai sukayi anan kowannensu yaji wani irin sabon salan so Yana shigarshi medauke da yanayin shaukin dakansa mutum yakasa sarrafa yanayin dayake ciki, dasauri Farrah ta kawarda idonta tareda sunkuyar da kanta kasa domin gudun wuce gona da iri, sannan tace Hamza kakirani Kuma bakace komaiba, cikin rashin kwarin jiki yace dama inasone inakaramiki tini gameda tanbayar Gen, please karki yimin halinnaki na nuna halin ko inkula da alakata dakikeyi dake, Farrah Ina sonki bazan iya Rayuwa da kowace maceba inba keba, Ina lura dake gameda irin son da kikemin aduk sanda muka hadu Ina hango tsantsar so da kaunata a cikin idonki Amma narasa dalilin da bakya serious adukkan wani Abu daya shafi soyayyarmu yauma bakaramar sa'a naciba harkikazonan mukayi magana, kinsha samana lokaci Amma kina kin zuwa, Dan Allah inaso ki aiwatar da abunda nacemiki adaren yau base wani lokaciba, Dan wallahi hakan kan iya zama barazana ga lafiyata Farrah,; tasowa yayi ya tsuguna a banta tareda marairaicewa Yana fadin Dan Allah kizama matata hakan shikadaine cikar babban burina daga cikin manyan burikan da nake dashi arayuwata gabadaya, wata irin Tsabar tausayin kansune yakama Farrah, hawaye suka cika idanuwan ta da sauri ta juyama Hamza baya Dan karyaga zubar hawayen daga idanta, sannan tace namaka Alkawarin in Sha Allah yau zanyi abunda kace base wani lokacin ba, tana gama fadin haka ta fara tafiya da sauri tareda sassarfa, tanayi tana share hawaye haseda ta tabbatar ta gyara fuskar ta Dan kar afahimci wani Abu gameda yanayin ta sannan tasakai tashiga.
Direct fallon Dadyn dake hawa nabiyu tanufa, azaune ta taraddashi kan lallausar kujerar dake fallon, tana shiga kallo ɗaya yayimata yafahimci tana cikin damuwa, dan hakanema yasa yayi murmushin karfin hali tareda fadin yar Dady zonan yafada tareda daga hannunshi dayin alamar nuni da bata gurin zama agefen shi kan babbar kujerar dayake zaune.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.