👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to daukacin yan group dina na watsapp wato *UMMU📖 DILSHAD 📗Novels📚* wanda ke karkashin kulawar Babban Admin kuma dan uwa wato *NAZEEFI YARIMA*, ina godiya sosai kuma mara adadi, Allahu subhanahu wata'ala ya kara yimana jagoranci, Ameen🤲🏻
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿️11.
*_Assalamu Alaikum_*
*_Fans, Ina bukatar addu'oin ku saboda yarinyata Yar shekaru 7 jiya 24/2/2020, aka dawomin da ita daga Islamiyya hannunta nadama ya karye a inda me machine ya bigeta, sakamakon Haka zakuji Ni shiru harse Allahu subhanahu wata'ala ya Bata Lafiya, wannan page dinma dandai nariga nafara typing dinshine shiyasa na daure na kawo mukushi, Dan Allah My daughter Islam need your prayers please🙏_*Duk da dai cikin harshen hausa Haj maimunatu take zubabama Gen masifa, hakan be hana Hussien fahimtar cewa tana maganane tareda nuna kishi gameda auren zoya da Gen yace yanasoba, dan haka shi kanshi seda ya kara jinjina maganar da Gen din yayi kafin zuwan Haj maimunatu kuma ya kara tabbatarwa da cewa Gen kwata kwata baya more ma zama da wannan masifaffiyar matar dan gaskiya in shinema da tuni hawan jini ya kasheshi kokuma da ya dade da rabuwa da ita.
shidai zare ido kawai yakeyi tareda kara shiga tsananin mamaki, wanda ake masifar domin shi kuwa banza yayi da ita, ganin be kulata bane yasa ta cigaba da bala'i tana fadin dakai nake kasan Allah indai ina raye tofa sedai kazaba kodai ni yar uwakka kokuma wannan me kama da Aljihun bayan wacce addinin ma bamu tabbatar da wanne takeyiba, inkuma ba hakaba sedai itama kayi zama da ita na karuwanci kamar yadda ka zauna da tsohuwar karuwarka wacce harta haifa maka ya, wacce ita kanta yar gata ga kamarta har boye gardi takeyi a daki kome suke aikatawa oho, Hummmmm mazadai kar a gyarama yarinya zama bari itama taje ta debo dan gaba da fatiha, koda yake ai itama tanan aka same...............jikakeyi tassssss Gen ya dauketa da wani irin mugun zazzafan mari wanda seda ta gigice tawani juya sannan ta fadi kasa, wani irin tsit taji wanda ya daukemata ganin idanuwanta dakuma karfin sauraron kunnuwanta saboda Tsabar Kara dakuma azabar Marin daya mata, rasa awace duniya take tayi kawai se tayi shiru bata kuma cewa komaiba, cikin Tsabar hasala da kara jin tsananin zafin zancen Haj maimunatu, Gen ya kara yin kanta da nufin kara kai mata wani dukan, da gudu Hussein ya karasa gurin ya rikema Gen hannu yana fadin haba General kayi hakuri mana ya kake dukan mace haka kamar kana filin daga sufa suna da rauni se an dinga hakuri dasu, Murmushin takaici Gen yayi yana fadin Hussein dandai bakasan wacece wannan matar bane, kuma na godema Allah da bakaji me take fadaba da natabbata yadda kakeson yar uwakka farrah dakuma abunda ta haifa da sekasa an kulle matarnan, wallahi hussein tun bayan barina kasarnan kaga yanzu ana neman shekaru 23 kenan ko? to gabadaya duk yawan shekarun nan befi na samu farin cikin shakaru 2 bane daga cikinsu inda za'a iya tattarawa akirga, duk sauran 21 din kullum cikin takaicin wannan matar nake dagani har Farrah, Yana gama fadin Haka ya waiga Yayi mata wani irin kallo me cike da takaici sannan yace wallahi kikayi wasa zakisani in aikata abunda Baki taba tunanin zan iya aikata mikiba ko amafarki, itakuwa tana ganin yadda Gen ya canja cikin kankanin lokaci se kawai ta koma daki da gudu, tana shiga gado ta haye tanata shafa inda Gen din ya mareta Sosai takejin shedar hannun shi agurin lallai tasan yau ta Maru, da tayi kokarin yin tunanin abun da yakamata tayine Amma saboda Tsabar firgita se kwakwalwarta takasa yimata wani tunani, ahaka har bacci ya kwasheta.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.