EPISODE 7

371 14 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

Dedicated to To maman ummee makociyata ta gari kuma daya daga cikin fans dina na rai da rai, Alhamdulillah ansamu nasarar yin aiki lafiya muna kara yima Allah godiya, ubangiji Allah yakara lafiya da kwarin jiki, Ameen ya Rabbih🤲🏻

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿7️⃣.

Cikin huci da tsananin bacinrai ya kalli Hamza dake kwance yace alokacin da Nigeria ta karbi ƴanci muna yara dan alokacin ban wuce 8yrs ba saboda anhaifeni a 1952 ne kuma harya zuwa 1960 ɗin india da pakistan suna nan suna ta rikicin da british suka haddasa musu na raba kawunansu.

Se bayan shekara gomane da muka ƙara ƙwari a 1970 lokacin ina da shekaru 18, se nasamu nasara aka daukeni aikin soja a matsayin kurtu, aka debemu da yawa aka turamu can dan mu temakama Pakistan, seda mukayi shekaru 19 muna famar yaki, sannan muka dawo kasa Nigeria a 1989, bayan dawowarmu da shekara daya aka daura min aure da haj maimunatu,  bayan Watanni 9 ta haifi khalil a 1992,  Khalil nada Watanni 2 aka Kara nemanmu a kasar Pakistan Haka na tsallake natafi nabar matata da dana, muna komawa kawai naje natadda budurwata tareda yaro Dan shekaru 2 asan saninmu inda aka hadamu da sojojin kasar Pakistan anan muka hadu Dan itama sojace, Dana tanbayeta setacemin Wai ai daciki na tafi nabarta, alokacin Dana aikata hakan kuruciya ce kedamuna, sanda nakoma sekawai nace muyi aure da ita Dan hakane bayan aurenmu akasamu Farrah, Dan Haka Hamza Dana ne na cikina Amma ba Dan Sunnah ba shiyasa naki inkarbeshi intaho dashi se nacema mahaifiyarshi ta tafi dashi nikuma na taho da Farrah tana da shekaru 2, saboda ba Dan halal bane shiyasa yakeda hali irin na Dan akuya, saboda babu wani Dan halak da zece yanason kanwarshi wacce suka fito ciki daya. Kuma wannan labarin na bakushine a takaice saboda kusan matsayin wannan Dan iskan yaron Dana haifa kuma nayi Dana sanin haihuwarshi, Dan Haka kowa ya shaida yau da hannuna zan kasheshi, Dan kawai yata ta halak tasamu jin dadin rayuwarta Koda kuwa hakan ze jawo Nima akasheni yakarasa maganar Yana dukan kirjinshi cikin isa wacce ke dauke da nuna sadaukar wa, sannan ya juya yakoma daki yadakko bindiga ya nufo inda Hamza ke kwance, ga mamakin Gen seyaga babu kowa agurin take yafara zare idanuwa Yana fadin Ina kake mara mutumci kafito yau da hannuna zan kasheka.

Kowa dake gurin yakasa cewa komai se raba idanuwa sukeyi. kamar daga sama Gen yajiyo muryar Farrah dake tsaye a gefanshi fuskarta ta jike sharkaf da hawaye, ta bude hannayenta biyu tana kare Hamza dake tsaye a bayanta yanata zare idanuwa domin gabadaya yagama tsorata da zancan Gen.

Cikin muryar tausayi da Kuma sadaukar war soyayya take magana tana fadin Dady wannan labarin da kabayar gameda Hamza baze hanani cigaba da sonshiba Kuma ina me maka rantsuwa da Allah cewa sena auri Hamza, Dady shin kama taba soyayya kuwa, kokuma kataba jin labarin rayuwar masoyan da zasu iya yin komai Domin farincikin soyayyar su kuwa? Kada Kai tayi alamar A'a sannan tayi Dan karamin tsaki tana fadin gaskiya ma baka taba ba, na tabbatar da ace kataba Koda jin labarin Wata soyayyar da bazama ka fara kirkirar labari Dan kawai karabani da Wanda zuciyata, Ruhina, dakuma gangar jikina suka Amince dashi amatsayin abokin Rayuwa taba, Dady Dan girman Allah kamar yadda kabada wannan labarin inaso indai kana Sona kamar yadda kake ikirari kafadama kowa cewa abunda kafada ba gaskiya bane kagaggen labarine, inkuma kace bazakayi abun da naceba sedai ka hadamu dagani har Hamzan ka kashemu kowa ya huta.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now