👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to My Fans love you all😍
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿9
Take amsa kuwwar muryar Farrah ta karade gidan a inda take Kiran Gen cikin tsananin Kara me dauke da rudewa da shiga tashin hankalin faduwar wannan baiwar Allah da tashigo gidan tareda karamar yarinyar da Bata wuce shekaru 6 ba.
Kan kace meye wannan kowa dake gidan ya hallara a bakin gate tundaga kan ma aikatan har zuwa shi kanshi mamallakin gidan, a inda duk bikin da akeyi Hamza Yana daki yana baccin gajiya da wahalar kwana dayayi Yana Sallah da addu'oin Allah ya aiko da Wata kaddarar da zata Hana Auren Farrah da Saifullahi sakamakon hakannema ya sakarmai da zazzabi me zafin gaske Wanda tun bayan idar da sallar asubahi bacci me nauyin gaske ya daukeshi ko breakfast besamu yayiba.
Suna zuwa gurin cikin yanayin rudewa Gen yafara magana Yana fadin Yar Dady Lafiya mukaji muryarki kina Kira da damuwa meke faruwa?
Kasa cewa komai tayi tana fadin "kallah" tareda nuna Yar karamar yarinyar Nan da Kuma matar dake kasa kanta Yana kan cinyar Farrah, wacce bazatafi shekaru *35* ba, Gen kwata kwata be fahimci me Farrah take son nunamaiba Dan hakane ma ya bita da tanbayar me nene Kuma kallah, me zan kallah, wacece wannan?
Kasa magana Farrah tayi duk a rude take ganin haka yasa Gen yace ma matan dake gurin sudauketa su kaita daya daga cikin dakunan bakin dake jere da dakin Hamza Wanda kullum safiyar Allah se anshiga an gyara kowani bangare naciki Haka kuwa akayi shiga da ita a inda suka kwantar da ita akan tankameman gadon dake dakin, Nan take Gen yasa khalil ya kwaso kayan aiki aka shiga yi mata gwaje gwaje, a inda ya sheda musu cewa akwai Tsabar gajiya tattare da ita Kuma ta sumane sakamakon wani Abu da tagani Wanda yayi matukar Bata mamaki dakuma tsoro, dajin Haka se Gen ya kalli Farrah wacce har awannan lokacin a kidime take tana zaune ta kama wannan yarinyar ta kankame a inda takejin ta kamar Wata wacce suka hada jini da ita, a hankali Gen yazo ya zauna kusa da kujerar da suke zaune yarinyar tanata kuka, seya samu cikin dabara ya banbare Yar daga jikin Farrah sannan yace ma Farra, Yar Dady, daga Kai tayi ta kalleshi, sannan tace Na'am.
Yace wannan matar wacece Ina kuma Kika samota? Inaso ki natsu kimin bayani, se alokacin ne natsuwa tafara ziyartar zuciyar ta da gangan jikin ta tace Dady Ina dakine na jiyo hayaniya shine nazo bakin gate Dan Inga kome ke faruwa to shinefa senacema me gadi ya kyaleta, kawai tana shigowa muna hada ido da ita seta fadi kasa.
Kallonta yakuma yi cikin rashin fahimta yace, to ke me Kika lura gameda ita? Ban lura da komaiba sedai kawai naga muna kama Sosai da ita Kuma bisa ga dukkan alamu ba Yan Nigeria bane Dan wannan yarinyar ba hausa takeyiba yaren India takeyi, se alokacin ne Gen ya fahimci tabbas wannan matar akwai abunda ta gani gameda Farrah da har yasata suma, Dan Haka seya bar inda Farrah din take yaje bakin gadon da matar Nan take kwance ya kafa mata ido nanfa shima Gen din ya taga taga ze fadi Dan tsananin kamanin daya gani na farrah a akan fuskar wannnan matar, da sauri su Baba kharami suka tareshi tareda zaunar dashi akan kujera suna mishi fifita shikuwa yanata sanbatu Yana fadin _Farrah ce bata mutuba dama Farrah tana nan, Farrah kitashi dama Baki mutuba? Tashi ki fadamusu kina raye ga yarkinan tanata jiranki ta girma_, Farrah tanajin sanbatun da babannata keyi ta taso da sauri tazo ta rikeshi tana fadin Dady me kake nufi, kana nufin wannan matar itace mahaifiyata?
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.