👨✈💗👩✈ *GIDAN SOJA*👨✈💗👩✈
By
*UMMU DILSHAD*
Marubuciyar
*(1) LABARINA*
*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*
*(3) GIDAN SOJA*
👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).Dedicated to, dukkan masoyana da kuma masoyan dukkan littafaina uwa uba na Gidan Soja, ina godiya sosai Allah ya bar ƙauna me ɗauke da tsoron Allah da tsantsar zumunci na gode🤝🏻
*TUNATARWA*
*(5), Addu'ar Buɗe Sallah (wato Bayan Anyi Kabbara Harama )**اللهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا، اَللهُ أَكْبَـرُ كَبِيرًا، اللهُ أَكْبَـرُ كَبِيرًا، وَالْحَمْدُ للهِ كَثيرًا، وَالْحَمْدُ للهِ كَثِيرًا، وَالْحَمْدُ للهِ كَثِيرًا، وَسُبْـحانَ اللهِ بكْـرَةً وَأَصِيلاً. (ثَلاَثاً)*
*أَعُـوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّـيْطَانِ مِنْ نَفْخِـهِ وَنَفْـثِهِ وَهَمْزِه.*
Allahu akbaru kabeera, Allahu akbaru kabeera, Allahu akbaru kabeera, walhamdu lillahi katheera, walhamdu lillahi katheera, walhamdu lillahi katheera, wasubhanal-lahi bukratan wa-aseela. (3)A'uthu billahi minash-shaytani min nafkhihi wanafthihi wahamzih.
Ina girmama Allah girmamawa, ina girmama Allah girmamawa, ina girmama Allah girmammawa. Kuma yabo ya tabbata ga Allah, a safiya da yammaci (sau uku). Ina neman tsari da Allah daga shaidan, daga hurawarsa, da tofinsa da kuma zungure-zungurensa.
*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*
🅿39
Dariya DDS yasaki yana faɗin "hhhhhhhhh lallai kuwa Hamza duk jarumtar da kayi zata tashi a banza kenan tunda babu wannan ƙaramin akwatin.
kowa dake gurin ran shi sai da ya sosu domin sun san hali DDS sarai inba sa'a ba sai ya ƙara tura Hamza inda zai sha wahalar da tafi wacce yasha abaya.
Sosai Hamza ya ruɗe tareda jin takaicin DDS jiyake kamar yaje ya shaƙe shi to amma hakan bazai yiwu ba domin yana iya ƙirƙirar mai wata masifar.
a hankali Raziya ta buɗe jakarta ta ɗakko akwatin tana faɗin ko wannan kuke nema? na ganshi ne akan kujera ina tuna nin dama ko daga Aljihun kayan daka cire ya faɗo, sai bayan ka tafi ka kwanta na gani shine na ɗauka na ɓoye ajakata da niyyar da safe in baka sai na manta, da sauri Hamza ya karɓa yana faɗin "Eh shine" tare da ƙoƙarin buɗewa.
da sauri DDS ya ƙwala ma Hamza kira tareda faɗin "karka kuskura ka Buɗe!
cak Hamza ya tsaya daga buɗe akwatin.
DDS yace bani shi nan, ba hurumin ka bane nawane.
yana karɓa ya buɗe sai ya girgiza kai yace lallai Hamza ya tabbata kai jarumine tunda ka iya ɗakko wannan dan haka dole nima in sara maka domin kayi ƙoƙari, duk da dai akwai saura amma karɓi wannan, hannayen shi biyu ya ɗaga dake ɗaure da Handcuff da nufin yimai salute.Sannan ya waiga ya kalli Farrah yace zonan, babu musu tazo yacema hamza kaima zo ka tsaya kusa da ita shima yayi yadda yace mai, sannan ya ƙara buɗe akwatin ya ɗakko zobe na mata me tsadar gaske ya mika ma Hamza yace saka mata, har Hamza ya buɗe baki zaiyi musu sai DDS ya nuna mai cewa akwai sauran mission inbaiyi yadda yace ba. yana sakama ta itama ya ɗakko na maza ya bata ta karɓa ta saka mishi, sai ya kalli jama'ar dake gurin yace me kuke jira bai ƙarasa rufe baki ba gurin ya gauraye da tafi jikake raf..raf...raf..raf.
YOU ARE READING
GIDAN SOJA
RomanceLABARINE A KAN GIDAN BABBAN TSOHON SOJA DAYASHA GWAGWARMAYAR RAYUWA, SANNAN AKWAI CHAKWAKIYAR SOYAYYA.