EPISODE 22

228 17 0
                                    

👨‍✈💗👩‍✈ *GIDAN SOJA*👨‍✈💗👩‍✈

By

*UMMU DILSHAD*

Marubuciyar

*(1) LABARINA*

*(2) DALILIN BAKIN KISHINA*

*(3) GIDAN SOJA*

*(4) SAINA AURI MIJIN ƳATA (TA CIKINA)*

👇
Intelligent writers Association...®✍
(Onward together).

*TUNATARWA*
*(Addu'ar Sanya Sababbin Tufafi.)*
"اَللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ كَسَوتَنِيهِ، أَسْأَلُكَ مِنْ
خَيْرِهِ وَخَيْرَ ماَ صُنِعَ لَهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهِ وَشَرَّ مَا صُنِعَ لَهُ.
Allahumma lakal-hamdu anta kasawtaneeh, as-aluka min khayrihi wakhayri ma suni'a lah, wa-a'u'zu bika min sharrihi washarri ma suni'a lahu.

Ya Allah! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne Ka tufatar da ni shi (wannan tufar). Ina rokonKa alherinsa da alherin abin da aka yi shi dominsa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrinsa da sharrin abin da aka yi shi dominsa.

*BISIMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM.*

              🅿22

Oyoyo ɗan uwa barka da zuwa pakistan, Hamza yafaɗa tareda ɗan bubbuga bayan khalil, barka kadai ya faɗa yana ƙoƙarin sakin Hamzan tareda da satan kallon Afshan.

itakuwa gabaɗaya tagama ɓaro jirgin shi abunka da ƙwararriyar lawyer, amma ganin yadda yaketa tsarguwane yasa ta basar kamar bata gane komai ba, dan khalil ɗin ya samu yasaki yasa ta ɗan fashe da wata ƴar dariya ta kalli Hamza tace "haba Bro haka ake tarbar baƙo mutum ya taho ƙafa ya ƙafa amma a tsakar gida kakemai sannu da zuwa? ka jashi kabashi masauki mana" tafaɗa tana kashema Hamza ido ɗaya.

shiko mutumin naka gabaɗaya ƙara narkewa yayi, komai tayi burgeshi yakeyi kashe idon ma datayi sai da tsigar jikinshi ta tashi, tuni ya ƙara afkawa duniyar nishaɗin masoya.

shi kanshi Hamzan yagama fahimtar Khalil ɗin dan haka sai kawai yayi dariya yace "Angama  your royal highness Solisitor" yafaɗa tareda jan hannun khalil yana faɗin zomuje ɗan uwa.

hamza na riƙe da hannun shi suna tafiya shiko sai waigen Afshan yaketayi, itakuwa tunda ta gama gano shi sai sakar mishi lallausan murmushi kawai takeyi tareda lumshe manyan dara daran idanuwanta masu jan hankali kawai takeyi.

Sosai jama'ar gidan sukaji daɗin isowar khalil, musamman ma Gen dan yasan yaron nashi yana da hankalin da zai bashi goyon baya akan auren Anty Zoya, dan tun suna yara suna ganin irin rashin mutumcin da mahaifiyarsu Haj maimunatu take mishi dan shi khalil ɗin tun yana ƙarami akwai lokacin da ya taɓa cema Gen ɗin "dady to ka kawo wata matar mana wacce bazata dinga maka faɗa ba mana" sai dai Gen ɗin yayi murmushi yace karka damu lokacin yana nan zuwa.

To yanzu dai Alhamdulillah lokacin ma ya riga da yazo domin kuwa Haj maimunatu na can na haukarta shikuma Gen ya gama arragement  ɗin komai domin a halin da ake ciki yanzu Har Anty zoya ma ta amince da zancen auren, sunata shan soyayyar su uwar gida bata sani ba.

bama ita kaɗai ba hatta mutan gidan ma babu wanda yasan zancen.
***********************

a ɓangaren Farrah kuwa bayan ta gama cin kukanta ta ƙoshine ganin zuwan Khalil yasa ta ɗan saki jiki tareda da ƙara zuba ido da kasa kunne kowani acikin gidan zai nuna mata yasan da zancen cewa gobe birthday ɗin ta amma abun mamaki shiru babu wanda ya nuna koda alama hatta Khalil ɗin da take tunanin shi zai tuna tinda ba agidan yake ba yau yazo inma ƴan gidan sun yi shiru ne dan suyi mata suprise tasan shidai zai nuna alama amma ko kaɗan bata komai ba dan hakane ma suna cikin yin dinner, tanata raba idanuwa daga kallon wannan zuwa wancan duk dan ta gano ko suna yin wani shiri a ɓoye, amma sai taga kamar ko yaushe ne babu wani banbanci.

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now